Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

An rufe rukunin shagunan Jabi Lake a Abuja saboda fargabar rashin tsaro

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Bankwana

    Da haka mu ke bankwana da ku a wannan shafi, sai kuma gobe Juma'a da yardar Allah. Umaymah Sani Abdulmumin ke cewa a kwana lafiya.

  2. Ana zanga-zanga kan kullen korona a China

    Hotunan bidiyo na ci gaba da bazuwa a shafukan sada zumunta da ke nuna yadda ake zanga zanga a babban birnin Tibet wato Lhasa da ke Kudu maso yammacin China.

    Masu boren na son a kawo karshen kullen Korona da tun watan Agusta.

    Mafi yawan wadanda ke gangamin yan ci rani daga China.

    Wani mazauni ya fada wa BBC cewa an kunshe su cikin gida ba sa iya fita neman abinci kuma ba su da komai a gida da sunan dakile yaduwar Korona.

    Ba a cika ganin ana nuna adawa da shirin China na ganin babu ko da mutum daya mai dauke da Korona, kuma kawo yanzu babu martanin kan boren daga hukumomi.

  3. Duniya na cikin yanayi mafi muni a tarihi - Putin

    Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ce duniya bata taba samun kanta cikin mawuyacin hali ba tun bayan yakin duniya na biyu kamar a wannan karon.

    A jawabinsa Putin ya zargi kasashen Yamma da kokarin tursasa wa duniya siyasarsu da al'adunsu.

    Ya ce kasashen Turan suna so kowa ya bi salon yadda suke gudanar da rayuwa ko yana so ko baya so, wanda kuma hakan a cewarsa mulkin mallaka ne.

    Putin ya ce su ne suka haddasa yakin da ke faruwa a Ukraine, kuma yana da yakinin a karshe Amurka da kawayenta za su bukaci su tattauna da Rasha.

    Rahotanni na cewa abunda Putin ya kira aiki na musamman a da suke yi a Ukraine ya shiga wata na tara, kuma ya sanar a yau cewa, ba ya dana sani.

  4. Canada na binciker China kan kafa caji ofis a kasarta

    Yan sanda a Canada na bincike kan rahotannin da ke cewa China ta kafa caji ofisoshin 'yan sanda cikin sirri a kasar, da ta ke amfani da su don takurawa 'yan kasarta mazauna Canadar.

    Sun zargi cewa ana amfani da wani gida da kuma shaguna a boye don yin aikin.

    Sun ce da farko an kirkire ofisoshi ne da sunan santacin taimakawa 'yan China da ke zaune can, to amma daga baya aka rika amfani wurin tursasawa Chinasawan komawa gida.

    Sai dai ofishin jakadancin China da ke Canada ya karyata rahoton, inda ya ce santocin ba sa wani abu da doka ta hana.

  5. Afirka Ta Kudu ta mayar da martani kan gargaɗin Amurka kan tsaron kasar

    Shugaba Cyril Ramaphosa na Afirka Ta Kudu ya nuna rashin jindadinsa da gargadin da Amurka ta fitar kan yiwuwar kai musu hari a wani yankin kasuwanci da ke Johanesburg.

    Amurka ta aike da gargadin ne ga Amurkawa ka su kauracewa shiga manyan taruka.

    Shugaba Ramaphosa ya ce an fitar da wannan gargadi ba tare da tuntubarsu ba.

    A ranar Talata, Amurka da wasu kasashen yamma uku sun fitar da irin wanna gargadi kan Najeriya.

  6. An tafka muhawara tsakanin masu takarar kujerar gwamna a Kano

    Kungiyar likitoci ta NMA a Najeriya, ta shirya muhawara a karon farko kan harkokin kula da lafiya ga 'yan takarar gwamnan jihar.

    Kungiyar ta gayyaci 'yan takarar gwamnan jihar Kano mutum takwas inda suka bayyana shirye -shiryen da za su yiwa fannin kula da lafiya a jihar Kano.

    'Yan takarar sun tafka muhawarar kan batun inganta lafiya da kayan aiki da kara ma’aikata da kuma kyautata yanayin aikin likitoci da tsaftar muhalli da kula da lafiyar mata masu juna biyu da kananan yara.

    'Yan takara takwas ne kungiyar likitoci suka gayyata amma biyar ne suka samu halarta.

    Akwai Dakta Nasiru Yusuf Gawuna na jam'iyyar APC da Salihu Tanko Yakasai na PRP da Injiniya Bashir Ishaq Bashir na Labour Party da Malam Ibrahim Khalil na ADC sai kuma Sha'aban Ibrahim Sharada na jam'iyyar ADP wanda mataimakin sa Malam Rabiu Bako ya wakilta

    Kungiyar likitocin da suka shirya wannan muhawara sun ce ba wai burinsu su kure kowa ba, amma a fahimci matsalar fannin lafiya a jihar Kano don su shirya yadda za su gyara.

    Sai dai 'yan takarar jam'iyyar PDP da NNPP ba su halarci taron muhawarar ba.

    Daga bayanan da BBC ta samu NNPP sun ce an basu goron gayyata a makare a dai-dai lokacin da dan takararsu ke halarta wani taro.

    Su kuwa PDP uzuri suka bayar kasancewar mutumin da ke ikirarin shi ne dan takarar gwamna a Kano yana halartar wani taro.

    Cibiyar kwararrun akantoci ta kasa ma, reshen jihar Kano sun ce za su shirya irin wannan muhawara ranar 8 zuwa 9 ga watan Disamba 2022.

  7. MDD ta ce ba a daukan matakan da suka dace wajen yaƙi da sauyin yanayi

    Wani rahoton majalisar dinkin duniya ya nuna cewa babu wata hanya da aka dauka wurin warware matsalar dumamar yanayi a fadin duniya.

    Rahoton ya ce kasashen duniya sun gaza cika alkawuran da suka dauka a yarjejeniyar sauyin yanayi da aka kulla a Paris, ta cewa za a rage dumamar yanayin da kashi Daya da rabi a ma’aunin Celcius.

    Rahoton ya ce yan tsirarun kasashe ne suka yi hubbasa wurin rage yaduwar bakin hayaki kamar yadda suka yi alkawari a Glasgow bara.

    Rahotanni na cea hakan ya dora duniya kan turbarar tsunduma dumamar yanayi da kusan kashi 2.6 a wannan karnin, abunda zai kara haifar da tsananin zafi da ambaliya da kuma fari.

  8. Sojojin na binciken hare-hare bisa kuskure kan fararan-hula a Najeriya

    Babban Hafsan Sojan Sama na Najeriya Air Marshal Oladayo Amoa ya ce rundunar ta kafa wani kwamiti da zai tattaro bayanai kan dukkan lamuran kai hari bisa kuskure kan fararen hula da sojojin saman kasar suka yi.

    A cewarsa kwamitin wanda ya kunshi manyan jami’an rundunar zai yi bitar abubuwan da suka faru har aka kai ga faruwar hakan domin daukar matakan magance su.

    A cewar wata sanarwa da rundunar ta fitar, Air Marshal Amao ya sanar da hakan ne a yau Alhamis, yayin da yake bude taron karawa-juna-sani kan aikace-aikacen rundunar sojin saman na shekara ta 2022 da ke gudana yanzu haka a Uyo, babban birnin jihar Akwa-Ibom.

    A cewarsa manufar hakan ita ce samun shawarwari kan muhimman matakan da ya kamata a dauka domin rage yawan kashewa da raunata fararen hula a kasar yayin wasu aikace-aikacen da rundunar ta sojin sama ke yi a wasu sannan kasar.

    Air Marshal Amao ya kuma kara da cewa binciken yana kuma da manufar kara tabbatar ana bin Kadin yadda sojojin rundunar ke aiwatar da umarnin da aka ba su da ba rundunar ta NAF damar koyon wasu muhimman darussan kan yadda za ta kaucewa faruwar hakan a gaba ko kuma rage irin ta'adin da irin wannan kuskure ke yi.

    Kazalika da kuma daukar karin matakai don rage cutar da fararen da ke zaune a yankunan da ke fama da tashe-tashen hankula.

    Yayin da yake taya sabbin matasan matukan jiragen yaƙi 17 da aka yaye a wajen taron, Mista Amao ya hore da su bi ka'idojin aiki da aka shimfida a yayin da suke fagen daga, kana su dauki dukkan matakan da suka wajaba wajen kare fararen hula da kuma rage illata su.

    Sai dai sanarwar, wadda mai magana da yawun rundunar Air Commodore Edward Gabkwet ya fitar ba ta sanar da lokacin da ake tsammanin kammala wannan binciken da fitar da sakamako ba.

    Mutuwa da kuma raunata fararen-hula a cikin hare-haren sojojin sama a Najeriya abu ne da ke ta maimaituwa a shekarun bayan bayan nan, tun bayan sakin wani bam bisa kuskure da suka yi a garin Rann na jihar Borno wannan ya yi sanadin mutuwar ‘yan gudun hijira da ma'aikatan agaji fiye da dari daya shekaru biyar da suka wuce.

    Ko a watan Satumban bara ma fararen hula fiye da 10 ne suka rasa rayukansu a kauyen Buhari na jihar Yobe wasu kuma 20 suka samu raunuka a wani harin da wani jirgin saman soji ya kai musu bisa kuskure.

    Lamarin dai bai tsaya kan fararen hula ba kadai domin wasu sojoji da dama sun rasa rayukansu a wata Afrilun barar lokacin da wani jirgin yaƙi ya kai wa motar su hari bisa kuskure a yankin Mainok na jihar Borno bayan da sojojin na kasa suka kira a kawo musu dauki a arangamar da suke yi da mayakan Boko Haram a lokacin.

    Akwai lamurra makamantan haka da suka faru a wasu yankuna cikin har da jihar Zamfara inda sojojin ke fada da ‘yan fashin daji.

  9. An rufe rukunin shagunan Jabi Lake a Abuja saboda fargabar rashin tsaro

    An rufe fitaccen rukunin shagunan Jabi Lake da ke babban birnin tarayyar Najeriya Abuja.

    Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake tsaka da fargabar rashin tsaro na yiwuwar kai hare-haren ta'addanci a birnin.

    A ƙarshen makon da ya wuce ne Amurka ta fitar da gargadin cewa akwai yiwuwar za a kai hare-haren ta'addanci a fain Najeriya, musamman ma Abuja, lamarin da ya ɗaga hankulan jama'a.

    Fargaba ta ƙaru bayan da a ƙalla ofisoshin jakadancin wasu ƙasashen da ke Abujan suka gargadi jama'arsu da su yi taka tsantsan don fargabar abin da ka iya faruwa.

    A wata sanarwa da hukumar rukunin shagunan ta fitar, ta bai wa masu hulɗa da su haƙuri kan duk wani abu da ba su ji dadinsa ba sakamakon matakin.

    "Muna bai wa jama'a haƙuri cewa za mu rufe rukunin shagunan a yau Alhamis 27 ga watan Oktoban 2022.

    "Mun ɗauki matakin ne don kare al'umma da kuma ma'aikatan wajen," in ji sanarwar,

  10. An janye karar mutanen da ake zargi da fyade a Afirka ta Kudu

    Masu shigar da kara a Afrika ta kudu sun janye karar da suka shigar kan zargin fyade da fashi da makami kan mutum 14 da ake tsare da su.

    A watan Yuli ne aka zargi mutanen da da ka iwa wasu mata hari yayin da suke aikin daukar wani fim cikin daji Krugersdrop.

    Masu shigar da karar sun ce gwajin kwayoyin halitta da aka yi yan una cewa ba bu wata kwakkwarar hujja da za ta sa a gabatar da su gaban kotu kan zarge zargen.

    Sai dai masu shigar da karar sun ce za a gurfanar da su kan saba dokar shigowa ba bisa ka’ida ba.

    Batun fyaden ya haifar da zazzafar zanga zanga daga al'ummar yankin, wanda hakan ya kara tada akidar kin jinin yan ci rani ta Xanaphobia.

  11. Indonisiya ta hana sayar da maganin tari bayan mutuwar 157

    Gwamnatin Indonesia ta ce kananan yara akalla 157 ne suka mutu kawo yanzu bayan sun kamu da cutar ƙoda sakamakon shan wani maganin tari.

    Ma'aikatar lafiya ta ce 73 sun rayu bayan sun yi jinya a asibiti. Mafi yawansu 'yan kasa da shekara biyar ne.

    Yanzu haka hukumomi sun dakatar da kamfanin har sai an kammala bincike don gano yadda aka yi hakan ta faru.

    Mako uku da suka wuce ma Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta yi gargadin a daina amfani da wani maganin tari da ya fito daga Indiya, wanda ke da alaka da mutuwar yara 70 a Gambiya.

  12. Lebanon da Isra'ila sun ƙulla yarjejeniya kan haƙar iskar gas

    Israila da Lebanon sun kulla wata yarjejeniya mai cike da tarihi da Amurka ta shiga tsakani, wadda za ta shafe wa kasashen hanyar tono albarkatun gas da aka dade ana kai ruwa rana a kansu.

    Arzikin na shimfide ne a kan iyakar kasashen biyu kuma a yanzu shugabanninsu sun saka hannu don ganin kowa ya cika lalitarsa.

    Kadan ya rage yaki ya barke tsakanin Lebanon da Isra'ilar kan ikon mallakar yankin da gas din yake.

    Ba a jima ba da kungiyar Hezbollah ta yi barazanar kai wa Isra'ila hari matsawar ta yadda ta fara haƙar gas din ba tare da amincewar Lebanon ba.

    Sai dai duk da kulla yarjejeniyar har yanzu kasashen biyu ba sa huldar difliomasiyya kuma ba sa shiri ko kadan.

    Wakiliyar BBC ta ce kowane bangare ya saka hannun ne a kasarsa, daga nan aka yi musayar takardun amincewar a kan iyaka, alamar da ke nuna cewa zaman doya da manja na nan.

  13. IMF zai bai wa Masar bashin dala biliyan uku

    Asusun ba da lamuni na duniya International Monetary Fund (IMF) ya amince ya bai wa Masar bashin dala biliyan uku da za ta karɓa cikin wata shida.

    Sanarwar ta ɓulla ne bayan ƙasar da ke arewacin Afirka ta karya darajar kuɗinta na Egyptian Pound.

    Ƙasar ta sha fama da matsalolin tattalin arziki tun bayan fara yaƙin Rasha da Ukraine, kuma a watan da ya gabata ne hukumomin Masar suka nemi tallafin IMF don ƙaddamar da "cikakken gyaran tattalin arziki".

    Masar ta zama ƙasa ta biyu da ta fi karɓar bashin IMF, inda ake bin ta dala biliyan 17.6.

    A 2016, Masar ta nemi bashin dala biliyan 12, inda daga baya ta sake karɓar biliyan 2.7 da 5.2 da zimmar rage raɗaɗin abin da annobar korona ta haifar a 2020.

  14. Najeriya za ta binciki zargin da ake wa sojin sama na yin ruwan wuta a kan fararen hula

    Babban hafsan sojin sama na Najeriya, Air Marshal Oladayo Amao, ya ce an kafa kwamitin da zai yi bincike kan zargin da ake yi wa sojojin saman ƙasar na jefa wa fararen hula makamai bisa kuskure.

    Ya ce binciken zai haɗa da gano dalilan da suka haifar hakan.

    Air Marshal Amao ya ce za a yi hakan ne domin lalubo hanyoyin magance irin waɗannan kura-kurai.

    Babban hafsan sojin sama na ƙasar ya bayyana haka ne a yau Alhamis, lokacin buɗe taron ƙara wa juna sani na jami'an sojin sama da ke gudana a jihar Akwai Ibom.

    Ya ce bayanan da za a samu za su zama darasi ga rundunar sojin sama ta Najeriyar.

    An sha zargin jiragen sojin saman Najeriya da buɗe wuta kan fararen hula a yankunan da suke yaƙi da matsalar tsaro na ƙasar, kamar arewa-maso-gabas da kuma arewa-maso-yamma.

  15. NNPC zai fara gyaran matatar man fetur ta Kaduna

    Gwamnatin Najeriya ta amince ta ƙulla yarjejeniya da wani kamfani a Koriya ta Kudu da zimmar gyara matatar man fetur ta Kaduna da ke arewacin ƙasar.

    Shugaban kamfanin mai na Najeriya NNPC, Mele Kyari, shi ne ya saka hannu a madadin Najeriya yayin taro kan harkokin lafiya da tawagar ƙasar ke halarta a Koriya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari.

    Sanarwar da NNPC ya wallafa a shafinsa na Twitter ta ce nan gaba kaɗan za a fara zagayen duba gyaran da za a yi.

    A ƙarshen shekarar 2021 ne gwamnatin Najeriya ta ware fiye da dala biliyan ɗaya don gyara matatar mai ta da ke birnin Fatakwal, aikin da ta ce ana ci gaba da yi.

    Kazalika, za a ci gaba da irin wannan aiki a matatar ta garin Warri na Jihar Delta.

  16. Ɗan China ya musanta zargin kashe Ummita a Kano

      • Marubuci, Zahraddeen Lawan
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Kano

    Dan Chinan nan da ake zargi da kisan tsohuwar budurwasa mai suna Ummukhulsum Sani Buhari, wadda aka fi sani da Ummita, a Jihar Kano da ke arewacin Najeriya ya musanta tuhumar da ake yi masa a gaban kotu.

    Bayan karanto masa zargin a gaban Babbar Kotun Kano, Mista Geng Quangrong ya ce ba gaskiya ba ne.

    Mista Guo Cunru, shi ne mutumin da ofishin jakadancin China a Najeriya ya turo don ya yi wa wanda ake zargin tafinta daga turancin Ingilishi zuwa harshen Chinanci.

    Lauya mai gabatar da kara wanda kuma shi ne kwamishinan Shari'a na Kano, Musa Abdullahi-Lawan, ya bukaci kotun ta fara sauraren tuhumar da ake yi wa wanda ake zargin.

    Alkalin babbar kotun Mai Shari'a Sanusi Ado-Ma’aji ya ɗage shari'ar zuwa ranar 16 ga Nuwamban 2022 don gabatar da shaidun da masu kara suka za su kawo.

    Ana zargin Mista Geng da kutsa kai cikin ɗakin Ummita tare da caka mata wuƙa a gidansu da ke unguwar Jan-Bulo da ke birnin Kano a watan Satumba.

    • Za mu tabbatar doka ta yi aiki game da kisan Ummita - Ganduje
  17. 'Yan bindiga sun sace ɗaliban jami'a a hanyarsu ta komawa makaranta a Jihar Enugu

    'Yan bindiga sun yi garkuwa da ɗaliban Jami'ar Najeriya ta Nsukka da ke Jihar Enugu a kudancin Najeriya yayin da suke komawa makarantar bayan dawowa daga yajin aiki.

    Rahotanni sun ce lamarin ya faru da misalin ƙarfe 4:00 na yammacin Lahadi a yankin Ƙaramar Hukumar Igbo-Etiti. Sai dai babu tabbaci game da yawan ɗaliban da aka sace zuwa yanzu.

    Kafar yaɗa labarai ta Premium Times ta ruwaito cewa 'yan bindigar sun shafe tsawon lokaci suna yin garkuwa da matafiya a hanyar tun daga ranar Asabar.

    Wasu majiyoyi sun ce an ci gaba da kai hare-haren har zuwa ranar Talata.

    Ɗalibai a jami'o'in gwamnatin Najeriya na komawa makarantu a makon nan bayan ƙungiyar malamai ta ASUU ta janye yajin aikin da ta shafe wata takwas tana yi game da walwalarsu da suka zargi gwamnatin ƙasar da ƙin kulawa.

  18. Sauyin yanayi: 'Dole ne kasashe masu arziki su taimaka wa masu tasowa'

    Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya shaida wa BBC cewa dole kasashen duniya su fifita batun magance matsalar sauyin yanayi a cikin lamurransu domin kauce wa mummunar matsalar dumamar yanayi.

    Wakilin BBC ya ce Guterres ya bayyana cewa kasashe masu arziki na jin haushin yadda ake samun matsalar sauyin yanayi a kasashe masu tasowa da kuma ganin yadda ake sukar su saboda sun gagara daukar matakin taimakawa.

    Ya ce akwai wasu matsaloli da yanzu gwamnatocin kasashen suka fi mayar da hankali a kansu maimakon batun sauyin yanayin.

  19. Najeriya: INEC ta soke rajista kusan miliyan uku

    Hukumar zaɓe ta ƙasa a Najeriya ta ce kashi 40 cikin 100 na sabbin waɗanda ta yi wa rajistar katin jefa ƙuri'a ɗalibai ne, tana mai cewa ta soke rajista kusan miliyan uku da suka saɓa wa ƙai'dojin hukumar.

    Shugaban hukumar ta Independent National Electoral Commission (INEC) Farfesa Mahmood Yakubu ya ƙara da cewa kashi 76 cikin 100 na masu zaɓe a ƙasar matasa ne.

    A cewarsa yayin wani taro da jam'iyyun siyasa a Abuja ranar Laraba, an samu ƙarin masu katin jefa ƙuri'a 9,518,188 a kan 84,004,084 da ake da su, kuma a yanzu rajistar farko-farko ta nuna cewa jimillar adadinsu ya kai 93,522,272.

    "Bayan kammala aikin, mutum 12,298,944 ne suka yi rajistar. Amma tun tuni mun sha faɗa cewa hanyoyinmu na tsaftace rajistar masu inganci ne," in ji shi.

    "Bayan mun tantance bayanan ta hanyar amfani da tsarin Automated Biometric Identification System (ABIS), mun gano 2,780,756 (kashi 22.6 cikin 100) ba su cancanta ba kuma muka goge su. Cikinsu akwai waɗanda suka yi sau biyu, da yaran da ba su kai ba, da kuma ma na boge waɗanda ba su cika ƙa'idojinmu ba."

    A watan Fabarairu na 2023 ne INEC za ta gudanar da babban zaɓe a Najeriya, inda 'yan ƙasa za su zaɓi sabon shugaban ƙasa da gwamnonin jiha da 'yan majalisar jiha da na tarayya.

  20. Ba za a daina wahalar fetur a Najeriya ba sai an kammala gyaran tituna - NATO

    Ƙungiyar masu dakon man fetur a Naijeriya ta NATO ta ce akwai yiwuwar ƙarancin man fetur da ake fuskanta a wasu sassan ƙasar ya ta’azzara idan ba a kammala gyaran hanyoyi da ake yi ba.

    Bayan taron da manyan kamfanoni da sauran masu faɗa-a-ji kan harkokin man fetur suka gudanar a birnin Legas ranar Laraba, ƙungiyar ta ce idan ana bukatar kawo karshen matsalolin man fetur baki ɗaya dole ne gwamnatin tarayya ta farfaɗo da matatu da bututan da ke aikewa da fetur zuwa jihohi.

    Wakilinmu na Legas Umar Shehu Elleman ya tattauna da Alhaji Yusuf Lawal Usman, shugaban kungiyar ta masu dakon mai.

    Latsa hoton ƙasa ku saurari tattaunawar: