Burkina Faso za ta dauki fararen hula domin yakar masu ikirarin jihadi
Shugaban mulki sojin Burkina Faso ya kaddamar da wani shiri na daukar dubban fararen hula 'yan sa kai domin taimaka wa kasar yakar masu ikirarin jihadi.
Jagoran kasar ya ce wannan yunkuri na shirin daukar fararen hula kusan 35,000, zai taimaka wajen kakkabe ayyukan masu ikirarin jihadi a kasar.
Za a bai wa matasan horon aikin soji na tsawo mako biyu, kafin a rarraba su zuwa sassa daban-daban na kasar, domin gudanar da ayyukansu.
Sau biyu dai kasar Burkina Faso ta fuskanci juyin mulki a wannan shekara, inda duka shugabanin ke alkawarta kawo karshen tashe-tashen hankula masu alaka da ayyukan masu ikirarin jihadi a kasar.