Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Sojojin Najeriya sun kashe 'yan Boko Haram 31, sun kama 70

Wannan shafi ne da yake kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Muhammad Annur Muhammad and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Likitoci dubu 24 ne suka rage a Najeriya – NMA

    Kungiyar likitocin Najeriya - NMA ta ce a yanzu likitoci dubu 24 ne suka rage a kasar domin kula da lafiyar al'ummar kasar fiye da miliyan 200.

    Shugaban NMA, Ojinmah Uche wanda ya bayyana hakan, ya kara da cewa karancin likitoci a kasar ya saba da irin shawarar da hukumar lafiya ta duniya - WHO ta bayar na adadin likitocin da za su iya duba marasa lafiya.

    A cewarsa "A yanzu likita daya ne ke duba marasa lafiya 30,000 a kudancin Najeriya a yayin da likita daya ne ke duba marasa lafiya 45,000 a arewacin kasar."

    Ojinmah ya ce ficewar jami'an kiwon lafiya daga Najeriya zuwa kasashen waje babban lamari da ke bukatar hukumomi su sa'ido.

    Bayanai sun ce a yanzu Najeriya ce kasa ta uku a yawan likitocin kasar waje da ke aiki a Birtaniya. Kasashen Indiya da Pakistan su ne kan gaba a yawan likitocin kasar waje a Birtaniya.

  2. Saudi Arabia za ta fara kerawa da sayar da motoci masu aiki da lantarki a 2026

    Ministan Sadarwa da Fasahar Bayanai na Saudiyya, Injiniya Abdullah Al-Swaha ya ce kasar za ta kera tare da fitar da motoci masu amfani da wutar lantarki sama da 150,000 a 2026.Babban kamfanin kera motoci masu amfani da lantarki na Amurka Lucid Motors Company na son ya rika samar da motocin 150,000 a Saudiyyar a duk shekara, daga shekara ta 2027, kamar yadda ministan ya bayyana jiya Laraba.Tun da farko shugaban kamfanin Peter Rawlinson ya ce nan da wani dan lokaci suke son fara aikin kafa masana'antar a Saudi Arabia.

    Ya ce, “Muna son fara kera motocin a 2025 kuma za mu kara yawansu a 2026 da 2027 mu kai motoci 150,000 a duk shekara” Ministan zuba jari na Saudi Arabia, Khalid Al-Falih ya ce kamfanin ya fara gina ma'aikatarsa a kasar a watan Mayu na wannan shekara.

    Ma'aikatar za ta kasance daya daga ciki guda uku na kamfanin mai cibiya a California, wanda Saudiyya za ta mallaki kashi 61 na hannun jarinsa.

  3. Hare-haren Rasha a Ukraine za su janyo katsewar wutar lantarki

    Kamfanin makamashi na Ukraine ya yi gargadin za a fuskanci katsewar wutar lantarki a kasar sakamakon hare-haren makamai masu linzami da kuma jirage marassa matuka da Rasha ke kaiwa kan gine-ginen makamashi na kasar.

    A sanarwar da ya wallafa a shafinsa na Telegram, kamfanin makamashin na kasar ya yi fatan rashin wutar ba zai wuce sa'oi hudu ba, sai dai ya bukaci mutane su dauki matakan riga-kafi.

    A wasu sakonni da aka wallafa a shafukan intanet, kamfanin ya bai wa jama'a shawarar su tanadi safa su kuma kasance suna da barguna domin kare kansu daga sanyi.

    Shugaba Zelensky ya ce karin cibiyoyin makamashi uku ne hare-haren Rasha suka lalata a jiya Laraba.

  4. Donald Trump ya yi rantsuwa a shari'ar ɓata sunan da wata mata ta shigar a kansa

    Tsohon Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi rantsuwa a shari'ar ɓata sunan da wata mata E. Jean Carroll da ya musanta yi mata fyade ta shigar a kansa.

    A tsakiyar shekarun 1990 lokacin ta yi wannan zargi. Sai dai Donald Trump ya mayar da martani ne yana matsayin shugaban Amurka da cewa bai taɓa haduwa da ita ba kuma ba ajinsa ba ce sannan karyata take.

    Mista Trump ya dade yana ta fafutukar neman kotu ta dage shari'ar amma a makon da ya gabata ne alkali ya ki amincewa da bukatarsa.

    Lauyar Trump ta ce wannan ma wata makarkashiya ce da ake yi wa wanda take karewa.

  5. An kashe mutum 15 a rikici tsakanin Hausawa da wasu kungiyoyin adawa a Sudan

    Al'umma da jami'an lafiya a Kudancin Sudan sun ce kimanin mutum 15 ne aka kashe bayan sabanin da aka samu kan fili a jihar Blue Nile.

    Rikicin ya samo asali ne sakamakon ce-ce-ku-ce tsakanin al'ummar Hausawa da kuma wasu kungiyoyin adawa da ke wani karamin gari, mai tazarar kilomita 500 kudu da babban birnin kasar, Khartoum.

    Mazauna yankin sun bayyana cewa sun ji karar bindiga sannan an cinna wa gidaje wuta.

    Ma'aikatan asibitin da ke garin sun ce an kai musu gawarwakin mutane.

    Rikicin ya barke ne duk da tsauraran matakan tsaro a yankin wanda aka kafa dokar hana fitar dare sakamakon rikicin fili a makon da ya gabata inda aka kashe mutane da dama.

  6. Wata tankar mai ta fashe ta kama wuta a titin Lagos-Ibadan

    Wata tanka da ke makare da man fetur ta fashe inda ta kama da wuta da safiyar Alhamis din nan a kan tagwayen hanyar Lagos zuwa Ibadan.

    Fashewar wadda ta auku a garin Araromi kamar yadda rahotanni suka ruwaito, ta haddasa cunkoson ababan hawa a titin.

    Wasu masu motoci da hadarin ya faru a gabansu sun ranta a na-kare domin tsira daga wutar da ta tashi ganga-ganga.

    Hukumar kiyaye hadura ta kasar, reshen jihar Ogun ta ce, kamar yadda rahotanni suka bayyana tana kokarin shawo kan lamarin.

  7. Barkanku da wannan lokaci

    Jama'a barkanmu da wannan lokaci. A yau Alhamis Muhammad Annur Muhammad ne ke muku maraba a wannan shafi da muke kawo muku labaran da suka shafi Najeriya da makwabtanta da sauran kasashen duniya kai tsaye.

    - Allah Ya iya mana.

    Ga wani karin magana mu sashe da shi;

    Da Abokin Daka Ake Shan Gari