Sojojin Najeriya sun kashe 'yan Boko Haram 31, sun kama 70

Wannan shafi ne da yake kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Muhammad Annur Muhammad and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Rufewa

    Masu ɓiɓiƴar mu a wannan shafi na labarai kai-tsaye, a nan muka kawo ƙarshen rahotanni da muka dauki tsawon rana muna kawo muku.

    Sai kuma gobe idan mai duka ƴa kaimu.

    Ahmad Tijjani Bawage ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Sojojin Najeriya sun kashe 'yan fashi uku tare da ceto mutanen da aka yi garkuwa da su

    Nigerian Army

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar sojin Najeriya ta sanar da ceto wasu matafiya da aka yi garkuwa da su a kan hanyar Kaduna-Zaria a yau Alhamis bayan samun bayanan sirri, inda sojojin suka sha karfin masu garkuwa da mutanen bayan daukar sa'o'i ana ɓata kashi.

    A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ta hannun ƙakakinta, Onyema Nwachukwu, ta ce ta samu nasarar kashe 'yan ta'adda guda biyu a wasu samame da ta kai Yankin Arewa maso Yammacin Najeriya a ƙauyen Abasia-Amale da ke karamar hukumar Ɓirnin Gwari na Jihar Kaduna a jiya Laraba.

    Ɓirgediya Onyema ya kuma bayyana cewa sojojin sun ƙwato ɓindigar AK-47 da harsasai da kuma wayoyin salula a hannun 'yan ta'addan.

    Wasu rahotanni kuma na cewa a safiyar yau Alhamis ne 'yan ɓindiga suka toshe hanyar Kaduna zuwa Zaria, inda suka yi ta ɓude wuta kan matafiya da garkuwa da mutanen da ba a san adadinsu ba.

    Sai dai, sojoji sun mayar da martani nan take ta hanyar fatattakar 'yan bindigar wanda haka ne ya sanya suka sake wasu matafiya ɓiyar da suka kama tun da farko.

    Shugaban Rundunar Sojin Najeriya, Laftanar Janar Faruk Yahaya, ya yabawa dakarun saboda jajircewa da suke yi wajen ganin sun kawo ƙarshen ayyukan 'yan ta'adda a yankin arewa maso yamma.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  3. Amurka ta zargi Iran da taimaka wa Rasha wajen kai hare-hare da jirgi marar matuki a Ukraine

    Drones

    Asalin hoton, Getty Images

    Amurka ta ce Iran ta jibge kwararru kan harkar soji a yankin Cremia da Rasha ta mamaye don su taimaka wurin kai harin jirage marar matuki na Kamikaze zuwa Ukraine.

    Mai magana da yawun Fadar White House John Kirby ya fada wa manema labarai cewa Amurka za ta kakaba wa Iran sabon takunkumi.

    Dama Burtaniya ta sanar da sabon takunkumi ga wasu kamfanoni da daidaiku da ke da hannu a sayar wa Rasha da jirgin Kamikaze da ta yi amfani da shi kan Ukraine.

    Tun a makon da ya wuce ne Rasha ta fara ruwan wuta ta sama kan birnin Kyiv, lamarin da ya yi sanadin rasa rayuka da lalata gine gine.

  4. Me ya sa ƙwace garin Shire ke da muhimmanci a yaƙin basasar Habasha?

    Bayanan bidiyo, Danna hoton sama ku kalli bidiyo

    Garuruwan da dakarun gwamnatin Habasha ke ƙwacewa daga hannun 'yan tawaye na yankin Tigray na da zuwa a wani lokaci mai muhimmanci a yaƙin da aka shafe shekara biyu ana yi.

    Amma ƙwace garin Shire ne ya fi nuna irin koma-bayan da mayaƙan tawayen ke fuskanta a baya-bayan nan.

    Abdulbaki Jari ya yi bayani game da muhimmancin garin na Shire a yaƙin basarar.

  5. Shugabannin ɗuniya na mayar da martani kan muraɓus din Liz Truss

    BIDEN/LIZ

    Asalin hoton, PA Media

    Jim kadan bayan murabus din Firaiministar Burtaniya, Shugaba Joe Biden ya ce Amurka za ta cigaba da huldar kud-da-kud da kasar, kuma ya gode wa Ms Truss bisa rawar da ta taka wurin agaza wa Ukraine.

    Shima Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce Burtaniya na bukatar magance wannan kwan gaba kwan baya akan Shugabanci da gaggawa.

    Sai dai mai magana da yawun ma'ikatar harkokin wajen Rasha ta ce suna maraba da labarin murabus din Ms Truss, inda ta kara da cewa Burtaniya ba ta taba samun Firanminista da ta zubar mata da kima ba kamarta.

  6. 'Yan banga sun laƙada wa shugaban 'yan jaridu na Jihar Zamfara duƙa

    Nigerian Police

    Asalin hoton, Getty Images

    'Yan ɓangar siyasa sun lakawada shugaban 'yan jarida na Jihar Zamfara, Comrade Ibrahim Musa Maizare duka, inda kuma suka yi barazana ga 'yan jaridu a fadin jihar.

    Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito cewa 'yan bangar sun yi ɗirar miƙiya zuwa ga shugaban 'yan jaridun, sun umurci ma'aikata da ke aikin gyara wasu shaguna na kungiyar a sakatariyarta na jiha da su daina aikin gyara shagon wanda ake son amayar da shi a matsayin ofishin yaƙin neman zaɓe.

    Ɓata garin sun ce ɓa za su ɓar wajen ba saboda wani dan siyasa ya basu, kuma muddin yana raye ba za su bar wurin ba.

    Tun da farko an karɓi hayar shagon ne domin ɓude wajen sayar da abinci, sai dai, bayan wanda suka kama shagon sun fice, 'yan ɓanga sun mayar da shi zuwa ofishin ƴakin neman zaɓe, inda a 2021, wasu 'yan ɓanga na daban suka ƙona shagon.

    Duk da zuwan jami'an tsaro sakatariyar 'yan jaridun, 'yan ɓangar sun ci gaba da zage-zage kan shugabanni da kuma sauran mambobin ƙungiƴar 'yan jaridun na jihar Zamfara.

    Da yake magana jim kadan bayan faruwar lamarin, Sakataren kungiyar, Ibrahim Ahmad Gada, ya yi kira ga jami'an tsaro da su tabbata sun kare rayuka da ma dukiyoyin 'yan jarida a jihar saboda rayuwarsu na cikin ɓarazana a yanzu.

  7. Jami'an tsaro na cikin wadanda aka kashe a zanga-zanga - Gwamnatin Chadi

    Chad Protest

    Asalin hoton, AFP

    Gwamnatin mulkin soji a Chadi ta ce jami'an tsaro na cikin mutanen da suka mutu a zanga-zangar da ake yi a ƙasar.

    Ana ta ƙone-ƙone da farwa gine-gine a Chadi a zanga-zangar da ake yi a fadin ɓiranen ƙasar hada da N'Djamena.

    An kuma farwa wani ofishin 'yan sanda da hedkwatar jam'iyyar sabon firaiministan ƙasar, Saleh Kebzabo.

    Mai magana da yawun gwamnatin ƙasar, Aziz Mahamat Saleh, ya ce akwai gawarwakin mutane da aka kashe da dama. Ya ce zanga-zangar ta rikiɗe zuwa tarzoma.

  8. Buhari ya naɗa Emmanuel Audu muƙaddashin shugaban NDDC

    Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da amince da naɗa Injiniya Emmanuel Audu-Ohwavborua a matsayin mukaddashin shugaban Hukumar Raya Yankin Neja Delta bayan sanar da ƙorar shugaban hukumar Effiong Akwa.

    Kafin naɗa shi, Emmanuel ya kasance babban darektar a ma'aikatar, inda yanzu zai ci gaba da rike muƙamin kafin a naɗa wani sabon shugaba da kuma mambobin gudanarwa na hukumar.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  9. Yadda za a zaɓi sabon firaiministan Birtaniya

    Daga yanzu dai hankali zai koma kan wanda zai zama sabon firaiministan Birtaniya.

    'Yan majalisar jam'iyyar conservative suna da yanzu zuwa ranar Litini domin ayyana 'yan takarar kujerar. Sai mutum ya samu amincewar 'yan majalisar majalisar jam'iyyar 100 kafin ya shiga takarar.

    Ana kuma ganin cewa 'yan takara uku ne kaɗai za su fafata.

    Kowane dan majalisar na da kuri'a daya - in aka samu 'yan takara fiye da biyu - 'yan majalisar ta jam'iyyar conservative daga nan za su kada kuri'a ta intanet a kan 'yan takara ɓiyu da suka rage.

  10. Ronaldo ba zai buga wa United wasa da Chelsea ba

    Ronaldo

    Asalin hoton, Getty Images

    Dan wasan gaban Manchester United Cristiano Ronaldo ba zai buga karawar da za ta yi da Chelsea ba a gasar Firimiyar Ingila ranar Asabar.

    Hakan na zuwa ne bayan ɗan wasan ya fice daga filin wasa tun kafin a tashi a karawa da United ta samu nasara kan Tottenham da ci 2-0 a gasar Firimiya jiya Laraba, bayan da kasa sanya shi cikin wasa.

    Wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, ya ce sauran 'yan wasa na shirye-shirye domin tinƙarar wasan su na gaba.

    Manchester United ta ce Ronaldo mai shekara 37, yana da muhimmiƴar rawa da zai taka mata, amma batun fita daga filin wasa batu ne na ɗa'a.

  11. An kama dubban mutane bayan gano wagegen rami dauke da gawarwaki a Mali

    Malawai

    Asalin hoton, Getty Images

    'Yan sandan Malawi sun kama 'yan Habasha 72 da aka samu suna ɓoye a wani gandun daji a garin Karonga da ke arewacin ƙasar bayan gano wani wagegen rami cike dauke da gawarwaki 25.

    An kuma kama 'yan Malawi 10 wadanda ake zargi da hannu a safarar 'yan Habashar zuwa cikin ƙasar.

    A ranar Laraba ne gwamnati ta gano wani wagegen rami a wani gandun daji da ke lardin Mzimba cike da gawarwaki, inda kuma a kusa da wurin ne aka kama 'yan Habashar.

    An ruwaito cewa wasu matasa a yankin ne da suka je cikin gandun daji domin ɗiban zuma suka fara ganin gawarwakin mutanen a inda har wasu sun fara ruɓa, inda aka iya gano kawunansu da kuma ƴatsu bayan da matasan suka koma suka sanar da 'yan sanda.

    A safiyar ranar Alhamis ne aka kuma sake gano wani rami dauke da gawarwaki hudu kusa da wagegen rami da aka gano a ranar Laraba.

  12. Buhari ya kori shugaban Hukumar Raya Ƴankin Neja-Delta

    Shugaba Buhari

    Asalin hoton, BUHARI SALLAU

    Shugaba Muhammad Buhari ya snaar da ƙorar shugaban Hukumar Raya Yankin Neja Delta Effiong Akwa.

    Darektar ƴada labaru na ma'aikatar harkokin Neja Delta, Patricia Deworitshe ce ta bayyana hakan, inda ta ce shugaban ya kuma sanar da kafa sabon hukumar gudanarwa ta hukumar.

    Sanarwar da aka fitar ta bayyana cewa za a aike da sunayen sabbin mambobin gudanarwa na hukumar zuwa ga Majalisar Wakilai domin amincewa.

    Har ila yau, sanarwar ta bayyana cewa shugaba Buhari ya ce ƙorar Effiong Akwa a matsayinsa na shugaban hukumar raya yankin Neja Delta zai kasance nan take farawa daga yau 20 ga watan Oktoban 2022.

  13. Sojojin Najeriya sun kashe 'yan Boko Haram 31, sun kama 70

    Army

    Asalin hoton, Getty Images

    Hedkwatar tsaron Najeriya ta bayyana cewa ta rundunar ta Operation Hadin Kai, sun kashe 'yan tada-ƙayar baya na Boko Haram 31 da kuma na ƙungiyar ISWAP ta Yammacin Afrika tare kuma da kama wasu 70 a arewa maso gabashin Najeriya.

    Darektan ƴada labaru na hedkwatar tsaron ƙasar, Manjo Janar, Musa Danmadami ne ya bayyana hakan yau a Abuja yayin taron manema labarai kan nasarori da sojojin ƙasar suka samu a makonni biyu da suka gabata.

    Danmadami ya kara da cewa mutum 70 daga cikin wadanda ta kama a yankin arewa maso gabas, 60 daga cikinsu sun kasance suna samar wa da 'yan tada-ƙayar bayan kayaki kamar abinci da makamai da man fetur da sauransuy.

    Mai magana da hedkwatar tsraon ta Najeriya, ya ce dakarun ƙasar sun samu nasarar ceto mutum biyu da aka tsare, inda 'yan tada-ƙayar baya 366 tare da iyalansu suka miƙa wuya.

    Har ila yau, Danmadami ya ce a ranar 11 ga watan Oktoba ne, sojoji suka yi wa 'yan ta'adda kwantan bauna a Bama da Ngala wanda ya kai mutuwar 18 daga cikinsu yayin da wasu suka tsere, inda akakwato makamai da dama.

    Manjo Janar Musa ya kuma ce cikin makaman da aka kwato sun hada da bindigar AK-47 guda ɓiyar da bindigar M21 da buhunan wake 64 da na shinkafa ɓiyar da magunguna da kayan sawa da ƙananan dabbobi da kudi naira 250,000 da da babura 11 da kekuna ɓiyar da sauransu.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  14. 'Yan majalisa maza sun ce kayan da takwararsu mace ta sa na tayar musu da hankali

    Sylvia Masebo

    Asalin hoton, Zambia parliament

    Bayanan hoto, Masebo ta yi mamaki da 'yan majalisar maza suka yi korafi a kan rigar da ta sa bayanta a bude

    'Yan majalisar dokokin Zambia maza sun tilasta wa ministar lafiya ta kasar wadda ita ma 'yar majalisar ce rufe jikinta bayan da wsu suka yi korafin cewa tana tayar musu da hankali.

    dole ta yafa mayafi inda ta rufe kafadarta da bayanta

    Ana tsakar zaman majalisa ne sai wani daga cikin 'yan majalisar na bangaren hamayya ya gabatar da korafi ga shugaban majalisar cewa kayan da takwarar tasu ta sa sun hana maza sakat, suna ja musu hankali.

    Daga nan ne sai Shugaban Majalisar Mulenga Fube ya jefa tambaya cewa ko tufafin da Ms Masebo ta sa sun dace ko ba su dace ba, kasancewar ba su rufe bayanta ba sosai.

    Rigar da ta sa dai ta rufe kafadarta da kirjinta amma kuma ana iya ganin bayanta kusan a fili fayau.

    Duk da cewa shugaban ya ce shi kam bai g wani abu na rashin dacewa da rigar 'yar majalisar ba, to amma ya bukace ta da ta rufe bayan nata saboda korafin da mazan ke yi.

    Daga nan ne Ms Masebo ta aro mayafi daga wata 'yar majalisar ta yafa kafin daga baya ta je ta samo nata ta rufe jikin nata.

    Masu rajin kare hakkin jama'a sun kira lamarin da wariya, inda Mirriam Mwiinga ta kungiyar Kiristoci ta matasa mata ta kasar ta gaya wa BBC cewa lamarin ya nuna wariya ga mata kuma bai tabbatar da 'yancin da y kamata a ce mata suna da shi ba

    Su dai 'yan majalisar dokokin kasar ta Zambia a lokacin zaman majalisa akwai kayan da ya kamata su sa, wadanda suke nuna kamala.

  15. Rakumin dawa ya kashe jaririya a Afirka ta Kudu

    Wata rakumar dawa da danta

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Rakumin dawa ba shi da fada sosai sai dai don kare dansa

    Wata jaririya ta rasu bayan da wani rakumin dawa ya tattake ta a wani gandun namun daji a Afirka ta kudu yayin da mahaifiyar jaririyar ke asibiti cikin mawuyacin hali.

    Jaririyar 'yar wata 16 tana tare ne da mahaifiyarta a wani daga cikin gidaje na alfarma da ke gandun daji na Kuleni Game Park a lardin KwaZulu-Natal.

    'Yan-sanda sun gaya wa BBC cewa har yanzu babu cikakken bayani kan yadda lamarin ya faru, amma dai sun fara gudanar da bincike.

    Ba abu ne da aka saba gani ba rakumin dawa wanda kusan ga shi nan da yawa a gidajen namun daji da gandun daji a Afirka ta Kudu, ya far ma mutane.

    Jami'in 'yan-sanda Laftana Nqobile Madlala ya gaya wa BBC cewa faruwar abin ke da wuya aka garzaya da uwar da jaririyarta zuwa dakin likita da ke kusa inda a can jaririyar ta rasu.

    Ba a dai san takamaimai inda abin ya faru ba a jiya Laraba, a babban gandun wanda yake da masaukin baki na alfarma har guda 14.

    Rakumin dawa shi ne dabba mai shayar da nono mafi tsawo a duniya, kuma ba dabba ce da aka sani da fada ba.

    Sai dai tamata wadda ita ma idan wani abu ya nemi taba 'yarta.

  16. An kashe mutum biyar a zanga-zanga a Chadi

    Chadi

    Asalin hoton, AFP

    Akalla mutum biyar ne suka mutu yayin zanga-zanga a Chadi, inda wasu 'yan kasar ke bukatar Shugaba Mahamat Idris Deby ya sauka kamar yadda ya yi alkawari.

    An gudanar da gangami a babban birnin kasar N'Djamena da wasu garuruwan.

    Sai dai rahotanni sun ce 'yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wurin tarwatsa masu boren.

    An kuma samu rahotanni da ke cewa an cinnawa wani bangare na gidan sabon Firaiminista Saleh Kebzabo wuta.

    Shugaba Mahamat Deby ya hau mulki ne watanni 18 bayan mutuwar mahaifinsa, kuma a wannan watan ne ya yi alkawarin sauka don a gudanar da zabe.

    Chad Army

    Asalin hoton, Reuters

  17. 'Yan Ukraine sun fara rage amfani da wutar lantarki saboda hare-haren Rasha

    jama'a sun fara rage amfani da lantarki a Ukraine

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, Hare-haren Rasha sun lalata wasu hanyoyin samar da lantarki na kasar

    Ministan makamashin Ukraine ya ce jama’a sun fara rage yawan wutar lantarki da suke amfani da ita don kashin kansu saboda karancin wutar a fadin kasar.

    To amma Herman Halushchenko ya ce duk da haka gwamnati ba ta da zabi face ta ci gaba da dauke wuta lokaci zuwa lokaci saboda karancin.

    Ministan ya ce hare-hare sama da 300 da Rasha ta kai musamman a kwanaki 10 da suka wuce sun lalata hanyoyin samar da wutar a garuruwa da dama.

    Shugaba Volodymyr Zelensky ya ce kashi daya bisa uku na Ukraine ya rasa wutar lantarki saboda hare- haren na Rasha.

    Mista Zelensky ya ce ''a ranar Laraba kadai tashoshinmu uku abokan gaba suka lalata, to amma za mu yi duk abin da za mu iya mu ga cewa mun gyara su.

    Wakilin BBC a can ya ce an kashe wutar kan titi a wasu wurare, an kuma umarci al'umma su rage amfani da abubuwa da ke jan wuta sosai a gidajensu.

  18. Amurka za ta taimaka wa mutanen da ambaliya ta shafa a Najeriya

    Shugaba Biden da Shugaba Buhari ( a dama)

    Asalin hoton, Femi Adesina/Facebook

    Gwamnatin Amurka za ta bayar da taimakon da ya kai na dala miliyan 1 ga mutanen da ambaliya ta yi wa barna a Najeriya.

    Tallafin da za ta bayar ta hanyar hukumarta ta raya kasashe masu tasowa (USAID), zai kasance na gaggawa.

    Ruwan sama mai tsanani da ya haddasa ambaliya ya janyo illa ga kusan mutum miliyan 2.8 a fadin kasar.

    Gidaje da dama sun lalace ko ma sun rushe a sanadiyyar matsalar wadda ta tashi miliyoyin mutane daga gidajensu.

    Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da ofishin jakadancin Amurkar ya fitar a Abuja a yau Alhamis.

    Amurkar ta kuma ce ta damu da yuwuwar ruwan ambaliyar da ya taru a wurare zai iya kara hadarin kamuwa da cutar amai da gudawa da sauran cutuka da ake dauka a ruwa, a jihohin Adamawa da Borno da Yobe.

    A wadannan jihohin an samu barkewar cutar kwalara a watan Agusta da Satumba, kuma ta kama mutum akalla 7,750 in ji sanarwar.

    A wannan shekarar da ake ciki an samu rahotannin bullar cutar ta amai da gudawa a jihohi 31 daga cikin 36 na Najeriyar.

    jakadiyar Amurkar a Najeriya Mary Beth Leonard, ta ce suna cike da jimami kan wadanda ambaliyar ta shafa da suka rasa abubuwa da dama - hanyoyin rayuwarsu da gidajensu har ma da 'yan uwansu.

    Ta kara da cewa Amurka za ta ci gaba da kasancewa tare da al'ummar Najeriya a wannan mawuyacin lokaci.

    Sannan za ta yi aiki tare da hukumomin kasar yayin da ake sa ran samun karin ruwan sama da ambaliya a watan Nuwamba, a wasu sassan kasar saboda sauyin yanayi da rashin magudanun ruwa, da nufin samar da karin taimako idan akwai bukatar haka.

  19. Har yanzu ana tsare da masu zanga-zangar EndSARS a Najeriya - Amnesty

    Masu zanga-zangar EndSars

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Amnesty ta ce har yanzu 'yan-sanda na ci gaba da cin zarafin jama'a a Najeriya

    Kungiyar kare hakkin dan-Adam ta duniya Amnesty International ta ce, har yanzu ana tsare da wasu daga cikin wadanda aka kama a lokacin zanga-zangar neman rushe runduna ta musamman ta 'yan sanda masu yaki da 'yan fashi da makami, wadda aka yi wa lakabi da ENDSARS a Lagos.

    Kungiyar ta ce shekara biyu bayan zanga-zangar da aka yi a wasu sassan Najeriya har yanzu wasu daga cikin wadanda hukumomi suka kama sama da 40 na kulle a gidajen yari daban-daban na kasar.

    A wata sanarwa da kungiyar ta fitar a yayin tunawa shekara biyu da zanga-zangar, yau Alhamis, Amnesty International ta ce kwamitocin da hukumomin kasar suka kafa domin gudanar da binciken cin zarafin da 'yan sanda suka yi sun kasa tabbatar da adalci ga daruruwan wadanda aka zalunta.

    Kungiyar da ta ce yayin da har yanzu akwai wasu gomman masu zanga-zangar da aka kama suna tsare a gidan yari, wasu daga cikinsu kuwa an gana musu azaba kafin a sake su ba tare da an tuhume su da kowa ne laifi ba.

    Amnesty ta kara da cewa har yanzu 'yan-sanda na cin zarafi da take hakkin dan-Adam har bayan zanga-zangar ta EndSars shekara biyu da wakana.

    Zanga-zangar da aka yi a watan Oktoba ta watsu wasu sassan Najeriya , inda aka bayar da rahoton cewa 'yan-sanda sun bude wuta a mashigin Lekki da ke Lagos.

    Kungiyar Amnesty ta ce sojoji sun kashe mutum akalla 12 a Lekki da kuma Alausa duka a Lagos.

    A kullum hukumomin kasar suna musantawa zargin kisan kiyashi da ake cewa sun yi wa masu zanga-zangar.

    A sanarwara da ta fitar kungiyar ta ce har yanzu ba a aiwatar da yawancin rahotannin da kwamitocin da hukumomin kasar suka kafa domin bincke ba.

    Sai dai bayanai sun nuna cewa an bai wa wasu da 'yan sanda suka ci zarafi diyya bayan binciken da Hukumar Kare Hakkin dan-Adam ta kasar ta gudanar, wasu jami'an 'yan sandan kuma an bayar da shawarar korarsu da gurfanar da su gaban shari'a.

  20. 'Yan-sanda sun tarwatsa masu tunawa da zanga-zangar EndSars a Lagos

    'Yan sanda

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Matasan na gangamin shekara biyu da zanga-zangar EndSars ne

    'Yan-sanda a Lagos sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa matasan da suka taru domin tuna shekara biyu da zanga-zangar neman rusa rundunar 'yan-sanda ta musamman mai yaki da 'yan fashi a Najeriya wadda aka yi wa lakabi da EndSars.

    Masu zanga-zangar wadanda suka fara taruwa a mashigin Lekki tun da misalin karfe tara na safe domin tunawa da ranar sun rika wakoki na neman a yi adalci kan wadanda suka mutu a lokacin zanga-zangar.

    Wasu daga cikin matasan sun je wurin dauke da akwatunan gawa da ke zaman alamta wadanda suka mutu a zanga-zangar, suna kira da a yi musu adalci.

    Sai dai rahotanni sun ce masu taron sun gamu da fushin 'yan-sanda inda suka tarwatsa su da hayaki mai sa hawaye bayan da 'yan-sandan suka zarge su da yin abubuwan da suka keta doka, inda suka fara hawan ginin mashigin.

    A sakon da ya fitar ta shafinsa na twitter, kakakin 'yan-sanda na jihar ta Lagos Benjamin Hundeyin ya ce an kyale masu zanga-zangar su yi taronsu ba tare da wata tsangwama ba, sai dai jami'ansu sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa wadanda suka nemi wuce gona da iri.

    Kakakin ya ce ba wanda ya yi amfani da sanda ko kulki wajen tarwatsa su. Babu wata maganar harbi. Amma ya ce duk wanda yake da wata sheda ta harbia wurin to suna maraba da ita, ''watakila hoton bidiyo domin mu samu damar daukar mataki,'' in ji shi da yake mayar da martani kan zargin harbi a wurin.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X