Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Bam da aka tayar a jikin wata bas ya kashe sojoji 18 a Syria

Wannan shafin yana kawo maku labaran da suka shafi Najeriya da makwaftanta da ma wasu sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi and Ahmad Tijjani Bawage

  1. 'Buhari ne zai tantance lokacin da Tinubu zai fara yakin neman zabe'

    Jam’iyyar All Progressive Congress mai mulkin Najeriya ta ce shugaban kasar ne za yanke hukunci kan lokacin da za a fara yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar.

    Mai magana da yawun kwamiti yakin neman zaben dan takarar shugaban kasar Mr Festus Keyamo ne ya bayyana haka bayan kammala taron da shugabannin jam’iyyar suka gudanar tare da gwamnoni da kuma kwamitin yakin neman zaben, a jiya Laraba.

    Jam’iyyar dai ta yi ta dage kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasar, sanadiyyar rashin jituwa game da mutanen da ke cikin kwamitin yakin neman zaben.

    Mr Keyamo dai ya ce kawunan ƴaƴan jam’iyyar a hade suke.

  2. Barkanmu da warhaka

    Jama'a barkanmu da safiyar Alhamis. Da fatan an tashi lafiya.

    Ku kasance da mu a wannan shafi domin karanta labarai da rahotanni na abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Sunana Haruna Ibrahim Kakangi, kuma ni zan ja ragamar shafin.

    Da fatan za ku je shafukanmu na Facebook da Tuwita da Instagram domin bayyana ra'ayoyinku.

    A Youtube kuma za ku iya bai wa idanunku abinci wajen kallon cikakkun bidiyo.