Sai da safenku
Karshen rahotannin kenan a wannan shafi na kai-tsaye.
Sai kuma gobe idan Allah ya kaimu za mu sake dawowa domin kawo muku sabbin labarai.
A madadin sauran abokan aiki, Ahmad Bawage ke cewa mu kwana lafiya.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafin yana kawo maku labaran da suka shafi Najeriya da makwaftanta da ma wasu sassan duniya.
Haruna Kakangi and Ahmad Tijjani Bawage
Karshen rahotannin kenan a wannan shafi na kai-tsaye.
Sai kuma gobe idan Allah ya kaimu za mu sake dawowa domin kawo muku sabbin labarai.
A madadin sauran abokan aiki, Ahmad Bawage ke cewa mu kwana lafiya.
Saudiyya ta yi watsi da zargin Amurka cewa matakin da ta dauka na rage yawan man da ta ke fitarwa na da alaka da siyasa.
Matakin na kasashen OPEC da kuma Rasha ya bakanta ran gwamnatin Amurka.
To amma Saudiyya ta ce batun tattalin arziki ne yasa ta yi haka ba, kuma hakan bai da alaka da rikicin Ukraine.
Sai dai Amurka ta ce za ta sake duba alakarta da Saudiyya.
Matakin na Saudiyya zai haifar da tsadar mai a duniya, kuma zai iya kawo wa Shugaba Biden cikas a siyasarsa, yayin da ake tunkarar zaben tsakiyar wa'adi a watan Nuwamba.
An gudanar da zanga-zangar bazata ta adawa da dokokin korona a Beijing da shugaba Xi Jinping ya yi, kwana guda kafin gudanar da taro na jam'iyyar kwamunisanci mai cke da tarihi.
Hotuna sun nuna masu zanga'zangar na daga alluna a kan wata gada da ke arewa maso yammacin birnin na Beijing, sai dai hukumomi sun ce an dakile zanga-zangar.
Mutane na ci gaba da nuna bacin rai a kafofin sada zumunta kan irin matakan cutar korona da gwamnati da ta sanya..
Hukumomi dai sun saurara matakan tsaro a birnin, inda aka kawo matafiya da yawa cikas, musamman ma mazauna birnin da ke dawowa gida da kuma tilasatwa wasu killace kansu.
Rundunar 'yan sandan Jihar Kaduna ta tabbatar da kashe 'yan bindiga biyu tare da raunata wasu da dama a garin Idasso na Kidandan da ke karamar hukumar Giwa na jihar.
'Yan sandan sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a yau Alhamis, inda ta ce wasu 'yan bindigan sun tsere da raunuka na harsashi.
Kakakin 'yan sandan jihar ta Kaduna DSP Mohammed Jalige, ya ce daruruwan 'yan bindiga ne suka zo yankin domin aikata muggan ayyukansu kafin a dakatar da su.
DSP Jalige ya ce bayan samun bayanai na zuwan 'yan bindigan, rundunar ba ta yi wata-wata ba ta aike da runduna ta musamman zuwa wajen domin tarwasa su.
Ya kara da cewa sun kwato bindigogin AK49 da harsasai da kuma wata babur daga hannun 'yan bindigan.
Faransa ta aikawa Jamus iskar gas a karon farko tun soma wahalar makamashi a fadin Turai sakamakon daina sayarwa kasashen gas da Rasha ta yi.
Faransar ta aike da iskar gas din ta wani bututu, wanda kuma na cikin yarjejeniya tsakanin kasashen biyun domin rage wahalar makamashi tun bayan da Rasha ta rufe bututanta da ke samarwa da Turai gas.
Duk da cewa gas din bai kashi biyu da Jamus din ke bukata ba a kowace rana, amma Berlin ta yi farin ciki da hakan.
Ana dai zargin Rasha da cewa tana amfani da batun samar da iskar gas a matsayin wani makami ga kasashen yamma tun bayan mamayar da ta yi wa Ukraine.
Wasu mutum biyu sun mutu bayan da wani dan bindiga ya ude musu wuta a wajen wata mashaya ta 'yan luwadi a Bratislava, babban birnin Slovakia.
An kuma raunata wani mutum a harin na yammacin jiya Laraba a mashayar Teplaren, kusa da babban birnin kasar.
Sai dai 'yan sanda sun ce an samu gawar wanda ake zargi da yin harbin a safiyar yau Alhamis.
Kafafen yada labarai sun ruwaito cewa mutumin ya wallafa a shafinsa na sada zumunta cewa yana adawa da 'yan luwadi da kuma yahudawa.
Haka kuma kafofin yada labaran Slovakia sun ruwaito cewa mutumin da ne ga wani tsohon dan siyasar kasar.
Firaiministan kasar Eduard Heger, ya yi Alla-wadai da harin, inda ya ce ba za su lamunci duk wani aikin masu tsassaurar ra'ayi ba.
'Yan sandan Jihar Ogun sun kama wani mutumi mai shekara 51, mai suna Oluranti Badejo, saboda zargin kashe matarsa, Folasade Badejo, bayan lakada mata duka.
Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a garin Orimerunmu, Mowe da ke karamar hukumar Obafemi-Owode na jihar ta Ogun.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ya fadawa manema labarai cewa an kama wanda ake zargin ne bayan kai musu rahoto da kanwar marigayiyar ta yi.
A cewar Abimbola, kanwar mamaciyar ta fada musu cewa 'yar karamar sabani ne ta shiga tsakaninsu da kuma ya kai ga mijin lakadawa matarsa duka har ya yi sanadiyyar mutuwarta.
“A lokacin da ya gano cewa matarsa ta mutu, ya yi amfani da dutsen guga wajen kona wasu sassan jikin marigayiyar saboda a ce wutan lantarki ne ya kasheta, sai dai, bai san cewa karamar 'yar su mai shekara takwas na kallonsa lokacin da yake aikata hakan,'' in ji Oyeyemi.
A yanzu dai ana tsare da wanda ake zargin a sashen masu aikata laifin kisa na rundunar 'yan sanda jihar ta Ogun, inda ake ci gaba da bincike.
Babban sakataren kungiyar tsaro ta Nato, Jens Stoltenberg, ya gargadi Rasha da cewa za ta dandana kudarta in ta yi amfani da makamin nukiliya a Ukraine.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito Stoltenberg na cewa kungiyar ba za ta fadi irin mataki da za ta dauka ba,amma martaninsu ba zai kasance mai dadi ga Rasha ba.
Stoltenberg ya fadawa taron manema labarai cewa ba lallai bane Nato ta mayar da martani ta hanyar amfani da makamin nukiliya ga Rasha ba.
Kawayen Ukraine daga kasashe 50 na ci gaba da gudanar da taro a hedkwatar Nato a Brussels, a irin wani abu da kyiv ta kira da abin tarihi.
Kawayen kungiyar Nato sun sanar cewa an fara bai wa Ukraine makaman kariya ta sama a yau Laraba domin kare kata daga hare-haren dakarun Rasha.
Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai, ya ce gwamnatin tarayya ta gaza a bangaren mai da kuma iskar gas, inda ya ce ya kamata ta fice daga bangaren kasuwancin.
El-Rufai ya bayyana hakan ne yayin taron zuba jari da hukumar karfafa zuba jari ta jihar Kaduna ta shirya.
Gwamnan ya ce bangarori da ke aiki a wannan kasa kamar bangaren nishadi da harkar sadarwa da kuma fasaha da sauransu, gwamnati ba ta da hannu a cikinsu.
A cewarsa, babu wani abu da ya sauya tun bayan cefanar da babban kamfanin man fetur na Najeriya a watan Yulin 2022.
Ya kara da cewa duk da irin kokari da shugaban kamfanin na NNP, Mele Kyari yake yi, kamfanin ta gaza a bangaren kasuwancin mai.
“NNPC babbar matsala ce ga Najeriya wacce ta fi karfin mutum daya wanda muddin ba a shawo kan matsalar ba, to za ta iya durkusar da Najeriya,'' in ji El-Rufai.
Rahotanni daga Syria na cewa bam da aka tayar a jikin wata bas ya kashe akalla sojoji 18.
Bam ɗin ya fashe ne a wajen Damascus yau da safe, kuma baya ga rasa rai mutane da dama sun samu munanan raunuka.
Ko a shekarar da ta gabata an kai hare-hare da dama a kan motocin bas na sojojin kasar.
A watan Oktoban bara ma wasu bama-bamai biyu da aka tayar kan bus din soji a Damascus sun kashe mutum 14.
A martanin da gwamnati ta mayar ta yi ruwan wuta a yankin arewa maso yammacin kasar da ke hannu ƴan tawaye.
Wani bincike ya gano cewa ayyukan da bil adama ke yi na mummunar illa ga namun daji a fadin duniya.
Wakilin BBC ya ce an samu raguwar namun dajin da ake da su a duniya da kashi 69 a cewar rahoton, tsakanin shekaru 1970 zuwa 2018.
Gidauniyar kare namun daji da halittun ruwa ta Fund for Nature ta ce Latin Amurka da yankin Carribean, na fuskantar ɓacewar dabbobin dawa da na ruwa da kusan kashi 95.
An ta'allaka matsalar da noma da gurbacewar muhalli da sauyin yanayi da sauran ayyukan da bil adama ke yi da ke cutar da namun dajin.
Shugaban ƙasar Uganda Yoweri Musaveni ya gargaɗi masu maganin gargajiya su daina karɓar masu Ebola da sunan yi masu magani.
Hakan na zuwa ne bayan da wani mutum mai shekara 45 ya mutu bayan ya gudo daga wani ƙauye a yankin Mubende, inda cutar ta ɓulla.
Hukumomi sun ce mutumin ya nemi magani a wurin masu maganin gargajiya kafin zuwa asibitin Kampala, babban birnin ƙasar, inda ya mutu bayan an kwantar da shi.
Yanzu haka dai cutar ta kashe mutum 19 a ƙasar ta Uganda, bayan ɓullar ta kimanin wata ɗaya da ya gabata.
Haka nan kuma shugaban ƙasar ya bai wa jami’an tsaro umurnin kamo duk wani mutum da ya yi hulɗa da mai ɗauke da cutar matuƙar ya ƙi killace kansa.
Wata babbar kotun tarayya da ke zama a garin Dutse ta wanke tsohon gwamnan jihar Jigawa Saminu Turaki daga tuhumar da hukumar EFCC ke yi masa ta almundahana da kuɗi naira biliyan 8.3.
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya ce ta kai tsohon gwamnan, da wasu kamfanoni uku, ƙara tun a shekara ta 2007 kan laifuka 33.
Alƙalin da ya yanke hukunci, mai shari’a Hassan Dikko, ya yi watsi da dukkanin tuhume-tuhume da ake wa tsohon gwamnan bisa hujjar rashin mayar da hankali daga ɓangaren waɗanda suka shigar da ƙara.
Bugu da ƙari kotun ta umurci a mayar wa Saminu Turaki takardunsa na tafiye-tafiye.
Rundunar ƴan sanda a jihar Katsina da ke arewacin Najeriya ta tabbatar da cewa ƴan fashi sun kashe mutum biyu lokacin da suka kai hari a wani ƙauye da ke ƙaramar hukumar Ƙanƙara.
Sai dai rundunar ta ce jami’anta sun samu nasarar koran ƴanfashin tare da ƙwato mutum 18 waɗanda aka yi yunkurin sacewa.
Mai magana da yawun rundunar ƴansanda a jihar ta Katsina, SP Gambo Isa ya ce mutane biyun da suka mutu an hallaka su ne kafin ƴansandan su kai ɗauki.
Maharan a kan babura sun kai farmaki ne a kauyen na Gidan Baushe da tsakiyar daren Laraba.
Sai dai bayan da aka sanar da ƴansanda game da harin, sun kai ɗauki cikin hanzari inda suka kori maharan tare da ƙwato wasu daga cikin mutanen da suka sace.
Rundunar ƴansandan Najeriya reshen jihar Kaduna ta ƙaddamar da bincike kan dalilan da suka sanya aka kulle wani mutum a cikin ɗaki na tsawon shekara 20.
A ranar Laraba ne ƴansandan suka ceto mutumin mai suna Ibrahim Ado, mai kimanin shekara 67 a wani yanki na birnin Kaduna da ake kira Bayajida.
Mai magana da yawun rundunar ƴansanda a jihar Kaduna ASP Muhammed Jalige, ya ce jami’an rundunar sun kai samame a gidan da aka kulle mutumin ne bayan samun bayanan sirri.
Ya ce mutumin mai kimanin shekara 67 ya kwashe tsawon shekarun ne yana garƙame a ɗakin, inda a nan yake cin abinci da kuma duk lamurransa.,, kuma an same shi cikin mummunan yanayi.
Yanzu haka dai mutumin na samun kulawa a asibiti.
Najeriya da kamfanin fasahar zamani na Microsoft sun sanya hannu kan wata yarjejeniyar bayar da horo ga mutanen ƙasar miliyan biyar.
A jiya Laraba ne ministan harkokin sadarwa da fasahar zamani na Najeriya, Isa Ali Pantami ya jagoraci tawagar ƙasar wurin sanya hannu kan yarjejeniyar, a Dubai na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.
Najeriya na sa ran matakin zai taimaka wurin ƙarfafa ƙwarewar matasa kan harkar sadarwa ta zamani, da samar da guraben aikin yi, da kuma bunƙasa tattalin arziki.
Ministan ya shaida wa BBC cewar ana sa ran fara aiwatar da shirin nan ba da daɗewa ba, kuma za a gudanar da shi ne na tsawon shekara biyar.
Ana nuna damuwa a Sudan kan yawaitar kisan da ake yi wa ƴanmta da sunan kare martabar iyali.
Daga farkon wannan shekarar, bayanai sun ce ƴanmata 11 ne ƴan’uwansu suka kashe, wani abu da ya ruɓanya abin da ya faru a bara.
Masu hanƙoron kawo ƙarshen lamarin sun ce akwai yiwuwar asalin yawan waɗanda aka kashen ya zarta yadda aka bayyana.
A wasu lokutan akan kashe mata kan yadda suke amfani da wayoyinsu, idan wani daga cikin ƴan’uwa ya yi zargin cewar suna tura wa samari saƙonni.
A Sudan dai alaƙa tsakanin mace da namiji kafin aure haramun ne.
Shugabar hukumar yaƙi da cin zarafin mata ta Sudan, Sulaima Ishaq Al Khalifa ta ce ana ganin cewar tsattsauran ra’ayin addinin musulunci ne ke iza wutar lamarin.
Ɗaruruwan mutane ne a Najeriya suka gudanar da zanga-zangar nuna adawa da yadda ƴan China ke yanka jakuna ba bisa ƙa'ida ba a ƙasar.
Mutanen na zargin ana ci gaba da kashe jakunan duk da umurnin da gwamnati ta bayar na dakatar da hakan.
Sun kuma zargi ministan harkokin noma da yin sakaci, ta hanyar barin mutane daga ƙasar waje suna gudanar da cinikayyar sassan jikin jakunan.
Yanzu haka dai akwai wani ƙuduri a majalisar dokokin ƙasar na neman a sanya ido kan yadda ake cinikayyar jakunan.
A watan jiya hukumar hana-fasa-kwauri ta Najeriya ta kama mazakutar jaki guda 7,000 a filin jirgin sama na Lagos, waɗanda ake ƙokarin fitar da su zuwa China.
Kasashen Afirka 26 sun kaɗa kuri'ar goyon bayan ƙudurin majalisar ɗinkin duniya na ƙin amincewa da matakin Rasha na ƙwace wasu yankunan Ukraine guda huɗu.
Ƙasashe 19 ne kuma suka ƙi kaɗa ƙuri'a, ciki har da Eritria, wadda a baya ma ta ƙi goyon bayan matakin Majalisar Ɗinkin Duniyar na yin Allah-wadai da ƙasar ta Rasha.
Ƙasashen da ake ganin ƙawayen Rasha ne, kamar Mali, da Jamhuriyar Afirka ta tsakiya, da Habasha, Congo, da Afirka ta kudu, da Sudan, da Uganda, da Zimbabwe duk suna cikin kasashen da suka ƙi kaɗa ƙuri'a.
Uku daga cikin waɗannan kasshe sun karɓi baƙuncin ministan harkokin waje na Rasha, Sergei Lavrov lokacin da ya kai ziyara a nahiyar a watan Juli.
Su kuwa ƙasashen Burkin Faso da Kamrau da kuma Equitorial Guinea dukkaninsu ba su halarci zaman ba.
A cikin wannan wata ne ministan harkokin waje na Ukraine Dmytro Kuleba ya yi rangadi a kasashen Afirka a ƙoƙarin Ukraine na samun goyon bayan ƙasashen yankin.
Bincike ya nuna cewa a cikin kowane minti biyu, yarinya ɗaya ta rinƙa kamuwa da cuta mai karya garkuwar jiki (HIV) a ƙasashen nahiyar Airka, a shekara ta 2021.
Hakan na nufin mutum 4,900 ne suka kamu da cutar a cikin kowane mako.
Bayanin ya ce yara mata daga shekara 15 zuwa 24 sun fi saurin kamuwa da cutar fiye da maza tsararrakinsu a kasashen na Afirka.
Bayanan dai sun fito ne daga wata tattaunawa da aka yi a birnin Dar Es Salaam na kasar Tanzania, wanda majalisar dinkin duniya ta shirya tare da gwamnatin kasar a ranar tunawa da yara mata ta duniya.
Bayanin ya ce yara mata sun kara shiga haɗarin kamuwa da cutar ne sanadiyyar cutar korona.
Mai kula da shirin yaƙi da cutar HIV na Amurka Dr. John Nkengasong ya ce idan har ana son a kawo karshen cutar HIV sai an kara ƙaimi wajen inganta hanyoyin kariya, da magancewa da kuma ilimantar da yara mata game da cutar.