Dubban mutane sun taru domin tarbar Sarki Charles lll a birnin Cardiff
A nan gaba kadan ne a yau Sarki Charles lll zai ziyarci yankin Wales, inda dubban mutane suka taru domin yi masa maraba.
A ziyararsa ta farko a matsayin Sarkin Birtaniya, Sarkin tare da matarsa za su halarci taron addu'o'in da za a yi wa Sarauniya a majami'ar Llandaff
Jude daga birnin Cardiff na daga cikin dubban mutane da suka taru domin ganin sarkin, ta kuma ce ''Ina son mika sakon ta'aziyyar Sarauniya, domin kuwa shi ne babban abin da ya dace da ni."
Anne Gainger, mai shekara 58, wadda ta je Landan domin mika sakon ta'aziyyarta ga rasuwar Sarauniya, yanzu haka tana birnin Cardiff domin tarbar sabon sarkin.
Ta ce ''ina son kasancewa a nan yau ne domin taya shi murnar zama sabon Sarki."