Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An saka gawar Sarauniya cikin taskar adana gawa
Wannan shafi ne da zai kawo muku labarai da rahotanni kai-tsaye na abubuwan da ke faruwa dangane da jana'izar Sarauniya Elizabeth ta Ingila.
Rahoto kai-tsaye
Nasidi Adamu Yahaya, Mustapha Musa Kaita and Abdullahi Bello Diginza
Ana gudanar da jana'izar Sarauniya Elizabeth
Mawaƙan kwaya na ci gaba da waƙoƙin neman gafara da jawo ayoyi daga Injila a yayin da ake jana'izar Sarauniya.
Idan aka yi waƙoƙin na ɗan wani lokaci sai kuma a ɗan tsahirta a karanto waɗannan ayoyi.
'Sojoji na da kyakyawar alaƙa da Gidan Sarautar Birtaniya'
Kamar mutane da dama a nan, Dave Luker yana sanye da lambobin girman da ya samu.
Ya shafe sama da shekara 40 a aikin soja: ɗaya daga cikin ayyukan farko da ya yi shi ne gadin mataimakin Hitler, Rudolf Hess a lokacin da yake jiran shari'a.
Luker ya taɓa haɗuwa da Sarauniya a baya, a lokacin da ya jagoranci jami'ai zuwa gare ta. Haka kuma ya taɓa haɗuwa da mijin Sarauniya Yarima Philip.
Lokacin da ya ɗauka yana wannan aikin ne ya sa ya zo wannan wuri a yau.
Abubuwan da aka ɗora kan akwatin Gawar Sarauniya
Iyalan Sarauniya na bin akwatin gawarta a baya
Muna iya ganin Sarki Charles III da ƙanwarsa Gimbiya Anne da ƙannansu Yarima Andrew da Edward.
Haka kuma cikin waɗanda ke biye da gawar Sarauniya akwai Yarima William da Harry da Peter Phillips wanda ɗa ne ga Gimbiya Anne kuma ɗaya daga cikin sauran jikokin Sarauniya.
An soma kashi na farko na jana'izar Sarauniya
Da misalin 10:44 na safe - lokacin da aka sa na fara kashi na farko na jana'izar, an soma tafiya da Gawar Sarauniya daga babban ɗakin taro na Westminster zuwa Cocin Westminster domin jana'iza.
Sarki Charles, Yariman Wales da Duke na Sussex sun isa Westminster
Sarki Charles III da Yarima William da Yarima Harry sun shiga Westminister kafin dauko gawar Sarauniya Elizabeth II.
Tsofaffin Firaiministocin Birtaniya sun iso wurin jana'iza
Sarauniya Elizabeth II ta yi zamani da Firaiministoci 15 a zamaninta, tun daga Winston Churchill wanda yake kan mulki a lokacin da ta soma mulki zuwa Liz Truss.
A halin yanzu John Major da Tony Blair da Gordon Brown da David Cameron da Theresa May da Boris Johnson duk sun isa wurin tare da matansu.
Shugaban Amurka Joe Biden ya isa wurin jana'iza
Shugaban Amurka Joe Biden da matarsa Jill sun isa Cocin Westminster Abbey domin halartar jana'izar Sarauniya Elizabeth II.
Sun isa London ne a ranar Asabar.
Sun haɗu da Sarauniya a watan Yunin bara a Fadar Windsor inda suka sha shayi da rana a tare.
Ƙarin mutane na ci gaba da isowa wurin jana'iza
Su wa ake sa ran za su halarci jana'izar Sarauniya a yau?
Kusan mutum 2,000 ne ake sa ran za su halarci jana'izar Sarauniya Elizabeth a yau, a bikin da ake gani mafi girma da aka taɓa yi tsawon shekaru a Birtaniya.
A hukumance, ba a wallafa wasu sunaye na baƙin da ake sa ran za su halarci jana'izar ba, amma ga dai abubuwan da muka sani na waɗanda za su halarci jana'izar da kuma waɗanda ba za su je ba.
Sarakunan ƙasashen waje
Manyan ƴan gidajen sarauta daga faɗin Turai za su halarci wannan jana'iza. Sun haɗa da sarakai da sarauniyoyi na Belgium da Netherlands da Sifaniya.
Haka kuma kuma akwai Sarkin Japan Naruhito da matarsa Masako da za su halarci wannan jana'iza.
Manyan shugabannin duniya
Shugaban Amurka Joe Biden da mai ɗakinsa Jill Biden tuni suka tafi zuwa London domin halartar jana'izar. Sauran shugabannin duniya da ake sa ran za a gansu a yau sun haɗa da Shugaban Faransa Emmanuel Macron da Firaiministan Australia Anthony Albanese da Firaiministan Canada Justin Trudeau da kuma wasu shugabanni daga ƙasashen rainon Ingila. Tuni shi ma Shugaban Afrika Ta Kudu Cyril Ramaphosa ya isa da takwaransa na Kenya William Ruto.
Shugabannin Rasha da Belarus da Syria ba su cikin waɗanda za asu halarci jana'izar.
Ƴan siyasar Birtaniya da jami'a
Akwai sanannun ƴan Birtaniya da za su halarci wannan jana'iza.
Firaiminista Liz Truss wadda Sarauniya ta naɗa kwana biyu kafin ta rasu za ta halarci jana'izar tare da wasu manyan jami'an gwamnatin ƙasar, da kuma ƴan siyasa waɗanda ke ɓangaren adawa.
Yadda kafafen watsa labaran duniya suka kasa suka tsare
Yadda aka kafa fararen tantuna kenan inda suka zagaye Fadar Buckingham.
A cikin tantuna, akasari ƴan jarida ne da masu gabatar da shirye-shirye a manyan kafafen watsa labarai na duniya inda duka suka saka baƙaƙen kaya daga sama har ƙasa.
Ƴan jaridan suna ci gaba da hira musamman ta talabijin da baƙi.
Hotuna: Ƴan sanda na shirye-shirye, jama'a sun taru
Abubuwan da ake sa ran za su faru yau dangane da jana'izar Sarauniya
Akwai abubuwa da dama da ake sa ran za su faru a yau a ranar da za a yi jana'izar Sarauniya Elizabeth II.
- 6:30 - Da misalin shida da rabi na safiyar yau ne aka kawo ƙarshen ba jama'a dama su yi bankwana da gawar Sarauniya.
- 8:00 - Za a buɗe ƙofofin cocin Westminster Abbey ga baƙi 2,000 da ake sa ran isowarsu, a daidai lokacin da ake rufe ƙofar babban ɗakin da ake ajiye da gawar Sarauniya.
- 10:44 - Da wannan lokaci ne ake sa ran za a soma tafiya da gawar Sarauniya, inda Sarki Charles da manyan ƴan Gidan Sarautar Birtaniya za su kasance a bayan gawar Sarauniya, inda sojojin ruwan ƙasar za su soma tura akwatin a amalanken da ake girke bindiga.
- 11:00 - Za a soma jana'iza
- 11:55 - Za a yi bushe-bushen algaita na ƙarshe ga Sarauniya.
- 12:00 Za kammala jana'izar, haka damisalin 12:15, jerin mutanen da ke biye da gawar Sarauniya za su raka ta zuwa Wellington Arch.
- 13:00 - Za a tafi da akwatin gawar a cikin mota zuwa Fadar Windsor ina a kan hanya ake sa ran mutane za su rinƙa gaisuwar ban girma.
- 15:00 Za a soma tafiya ta uku ranar, zuwa wurin binne Sarauniya a St George’s Chapel
- 16:00 - Za a yi addu'o'i ga Sarauniya.
- 19:30 - Iyalan Gidan Sarautan Birtaniya za su koma wurin da za a binne Sarauniya Elizabeth II tare da mijinta Duke na Edinburgh
Barkanmu da safiya
Jama'a barkanmu da safiyar Litinin, 19 ga watan Satumbar 2022. Labarai da rahotannin da za mu kawo a wannan shafin na musamman ne domin kuwa a yau ne ake jana'izar Sarauniya Elizabeth II.
Za mu kawo muku rahotanni kai-tsaye kan yadda ake gudanar da wannan jana'iza da kuma wasu rahotannin da suka shafi bikin jana'izar.