Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

'Yajin aikin malaman ASUU ka iya janyo babbar masifa ga Najeriya'

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da ma sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza and Nasidi Adamu Yahaya

  1. An kai mummunan hari kan ayarin motocin da ke dauke da kayan abinci a Somaliya

    Akalla mutum 20 ne suka mutu, wadanda suka hada da mata da kananan yara, a yayin da 'yan bindiga suka kai hari kan ayarin motocin da ke dauke da kayan agajin abinci a tsakiyar yankin Hiiraan.

    Gwamnan yankin ya shaida wa BBC cewa maharan sun saka bom a cikin karamar motar da mutanen ke ciki sannan kuma da tayar da shi.

    Kungiyar 'yan tawaye ta al-shabab ta ce tana kaddamar da hare-hare kan sojojin da ke samun goyon bayan gwamnatin kasar.

    Kasar Somaliya dai na fama da abin da masana ke kira 'tsananin fari mafi muni cikin shakarar 10' da kasar ke fama da shi.

    Kungiyar al-Shabab mai alaka da al-Qaeda wadda ke rike da ikon wurare masu yawa a kudancin kasar, na kokarin fadada ikonta zuwa wuraren da gwamnatin kasar ke rike da su.

  2. NDLEA ta kama mutum takwas da laifin fashi da makami a Legas

    Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA sun kama mutum takwas a wani kungurmin daji da ake zargi da aikata ta’addanci da garkuwa da mutane da kuma fashi da makami a dajin jihar Ondo.

    An kuma samu abubuwa masu fashewa da bindiggi da harsasai da kuma tabar wiwi.

    Wakilin BBC ya ruwaito cewa lamarin na zuwa ne a lokacin da hukumar ta kama wani mutum dan shekara 53 mai suna Ehiarimwiam Osaromo Emmanuel da kwayar Tramadol a zauren a filin jiragen sama na Murtala Muhammed da ke a Legas.

    A sanarwar da Femi Babafemi ya aike wa manema labarai, ya ce jami’an NDLEA sun kaddamar da samamen ne bayan wani rahoto da aka tsegunta musu, sai suka fantsama cikin kungurmin dajin Ala da ke karamar hukumar Akure ta Arewa a jihar Ondo, inda suka kama mutum takwas.

    An kama wadanda ake zargin ‘yan fashin ne a ranar Juma’a, 2 ga Satumba, 2022.

    Abubuwan da aka kwato daga hannunsu sun hada da buhu 25 na ganyen wiwi mai nauyin kilogiram 296, da wasu abubuwa masu fashewa kamar bom guda shida da harsashi shida.

    Akwai kuma babura guda hudu da layu daban daban da suke amfani da su wajen aikata ta'addanci kan mutane da suka sha tsarewa a dajin.

    Wannan na zuwa ne a lokacin da jami’an suka kama wasu mutane masu sarrafa hodar Ibilis da ake kira Metanpethamine a Agbara dake a wajen birnin Legas.

    Kamen hodar methanpethamin ya zo a lokacin da jami’an hukumar suka sake kama wani mutum mai suna Ehiarimwiam Osaromo Emmanuel a zauren masu shirin tafiya a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke a Legas bisa zarginsa da safarar miyagun kwayoyi nau’in Tramadol kimanin kwali dubu biyar da ya boye a cikin jakarsa.

    A Sokoto, jami'an tsaron NDLEA sun kama wata motar bas ta kasuwanci inda aka kwato na'urar kunna CD guda biyu da ke kan hanyar Sokoto zuwa Bodinga inda a gano tabar wiwi mai nauyin kilogiram 5.5 a cikin na’urorin, tare da kama mai kayan Nasiru Ibrahim, mai shekara 37.

    Wata ‘yar kasuwa a Abuja mai suna Onyinye Nwoke mai shekaru 38, dubunta ya cika bayan jami’an leken asiri sun kai samame a gidanta da ke rukunin gidaje na Aldenco Estate, da tabar wiwi da aka noma a bayan gidan.

    A jihar Neja, jami’an hukumar NDLEA a ranar Alhamis da ta gabata sun kama wata mota da ke jigilar dabbobi daga Legas zuwa Kaduna dauke da buhunan tabar wiwi a daskare har guda 449 da wasu buhunan 111 mai nauyin kilogiram 1,531 mallakin wani dila a Zaria.

    An ce an yi lodin miyagun kwayoyi ne a cikin motar daga a Akure, ta jihar Ondo.

    Direban babbar motan mai suna Yahaya Sani da mataimakinsa Samaila Rabiu da yaron motarsa Bilal Ibrahim da wakilin mai tabar wiwi, Auwalu Isyaku da fasinja Mustapha Abdulrahman duk an kama su.

    A jihar Gombe, jami’an ‘yan sanda sun kama sinki-sinki na kwayar Tramadol, dubu dari takwas da sha daya da Diazepam da Exol 5, masu nauyin kilogiram 150 a cikin wata mota da aka yi mata lodi daga Onitsha na jihar Anambra.

  3. Ana sa ran sanar da sabuwar Firaministar Birtaniya

    Ana sa ran sanar da ministar harkokin wajen Birtaniya, Liz Truss, a matsayin shugabar jam'iyya mai mulki ta Conservative - kuma firaiminista ta gaba - nan gaba a yau Litinin.

    Ta jagoranci 'yayan jam'iyyar a gangamin kada kuri'ar neman maye gurbin Boris Johnson, wanda aka tilasta wa yin murabus sakamakon tarin badakala. Mutum ɗaya da a yanzu ke hamayya da ita shi ne tsohon ministan kudi Rishi Sunak.

    Wakilin BBC ya ce Idan ta yi nasara, Ms Truss za ta karɓi mulkin Birtaniya a yanayi na tsadar rayuwa, matsalolin ma'aikata da ta tattalin arziki da ke neman kunno kai.

    Ta yi alkawarin daukar matakai cikin gaggawa domin taimakawa magidanta da matsalar tsadar gas.

  4. Yau ne za a yanke hukunci kan zaben kenya

    An tsaurara matakan tsaro a wannan Litinin din a Kenya, yayinda ake sa ran kotun koli ta yanke hukunci kan kalubalantar sakamakon zaben shugabancin kasar da aka shigar a gabanta.

    Hukumar zabe ta kasar ta bayyana mataimakin shugaban kasa, William Ruto a matsayin wanda ya yi nasara.

    Sai dai abokin hamayyarsa, Raila Odinga, ya zargi cewa an yi aringizon kuri'u. Wakiliyar BBC ta ce, Odinga na son Kotu ta soke sakamakon ko kuma ta sanar da shi a matsayin wanda ya lashe zaben ko kuma ta umarci a sake gudanar da wani zabe.

    Mista Ruto dai ya yi watsi da zarge-zarge Odinga. Mutanen biyu sun ce zasu rungumi hukunci da kotun koli za ta yanke.

  5. Assalamu Alaikum

    Masu bibiyarmu a wannan shafi barkanmu da safiyar Litinin wadda Bahaushe ke yi wa kirari da Mande tushen aiki ko da Nasara na tsoronki.

    Ku kasance da mu a wannan shafi domin samun labarai da rahotanni kai tsaye na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da ma sauran sassan duniya.

    Sunana Abdullahi Bello Diginza, kuma ni zan ja ragamar wannan shafi a wannan lokaci, za kuma ku iya ziyartar shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.