Rufewa
A nan za mu rufe wannan shafi da ke kawo muku labarai da rahotanni kai-tsaye.
Ku kasance da mu gobe da safe idan Allah ya kai mu, domin samun sabbin labaran da suka shafi rayuwarku.
Mu kwana lafiya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da ma sauran sassan duniya
Abdullahi Bello Diginza and Nasidi Adamu Yahaya
A nan za mu rufe wannan shafi da ke kawo muku labarai da rahotanni kai-tsaye.
Ku kasance da mu gobe da safe idan Allah ya kai mu, domin samun sabbin labaran da suka shafi rayuwarku.
Mu kwana lafiya.

Asalin hoton, EPA
Rundunar sojin Isra'ila ta bayyana cewa watakila daya daga cikin sojojinta ne ya kashe Ba'amurka kuma 'yar Falasdinu, sannan fitacciyar 'yar jarida Shireen Abu Aqla.
Gogaggiyar 'yar jaridar da ke aiki a matsayin mai daukowa gidan talbijin na Al Jazeera, ta gamu da ajalinta lokacin da aka harbe ta a ka, lokacin daukar rahoton samamen sojin Isra'ila a yammacin gabar Kogin Jordan a watan Mayu da ya wuce.
Wannan ita ce hanya daya tilo da sojojin suka kusan amincewa sojin Isra'ila ne ya aikata.
Wani babban jami'in soji ya ce an fara gudanar da bincike kan sojojin da ake zargi da hannu, domin fara gudanar da binciken gadan-gadan.
Iyaye da 'yan uwan Abu Aqla sun ce ba su yi mamaki da wannan ba, ganin yadda a baya aka yi ta kokarin rufa-rufa kan lamarin da kokarin kaucewa fuskantar shari'a da nemawa 'yarsu hakkinta.
Ranar 11 ga watan Mayun 2022, Abu Aqla ta isa sansanin Jenin domin daukar rahoto kan mamayar da sojojin Isra'ila suka kai yankin, inda sukai taho mu gama da mayakan Falasdinu.
Duk da tana sanye da rigar kariya daga harsashin bindiga, dauke da rubutu mai shaidar aikin jarida, da hular kwano, hakan bai hana sojin Isra'ila harbinta ba.

Asalin hoton, FESTUS KEYAMO/TWITTER
Kungiyar tsofaffin daliban jami'i'on gwamnatin Najeriya, ta yi gargadin cewa yajin aikin da kungiyar malaman jami'a ta ASUU ke yi ka iya zama babban bala'i ga kasar.
A wata wasika da kungiyar ta fitar a ranar Litinin, ta yi kira ga gwamnati da ASUU su sake zama teburin sulhu domin magance matsalar.
Sama da watanni shida kenan da ASUU ta tsunduma yajin aiki a daukacin Najeriya, ko da yake wasu gwamnatocin jihohin Najeriya sun kira malamai su koma bakin aiki, idan ba haka ba babu mai biyansu albashi.
Malaman Jami'o'in na bukatar a kara musu albashi, da alawus-alawus da sauran bukatu.
Daya daga cikin abubuwan da ke kara tunzura yajin aikin shi ne, rashin biyan jami'o'i kudaden shiga da suka kai sama da Naira Tiriliyan 1.

Asalin hoton, Getty Images
Mahukunta a kudancin Pakistan na ta fadi tashin ganin sun kare babban tekun yankin daga ballewa saboda kada ruwa ya cinye garuruwa da ke kusa da shi.
Ministan lardin Sindh ya ce yawan ruwan da ke tekun ya kai ba a iya ganin karshensa kuma yana neman ya balle duk da tare shin da aka yi.
A yanzu ana ci gaba da kiraye kirayen yadda za a samar da abubuwan da za su tare ruwan.
Tuni dai daruruwan mazauna kauyukan da ke kusa da kogin suka koma garuruwa makwabta. Fiye da mutane 1300 ne suka mutu sakamakon ambaliyar ruwan da ta afkawa kasar.
Ana ta kiraye-kirayen a sake yi wa tekun hanyoyin da ruwan zai wuce, a daidai lokacin da ya kara tumbatsa, sakamakon hadewa da kogin Indus.
Daruruwan mazauna kauyuka mafi kusa na ta kwashe komatsansu domin kaura zuwa garuruwa makofta kamar su Sehwan, domin tsira daga bala'in ambaliyar ruwa.
Sama da mutane 1,300 ambliyar ta hallaka a Pakistan a watan da ya gabata, lokacin da aka shafe makonni ana sheka ruwan sama a kasar.

Asalin hoton, Getty Images
Kafar yada labaran China ta rawaito cewa akalla mutane 46 ne suka mutu lokacin da wata mummunar girgizar kasa ta afka wa kudu maso gabashin kasar.
Girgizar kasar, mai karfin sama da maki shida, ta faru ne da misalin karfe daya na rana a agogon yankin Sichuan, ta kuma yi tafiyar kilomita 10 cikin kankanin lokaci.
Kafar yada labaran yankin ta rawaito cewa girgizar kasar ta shafi turakun sadarwa da haddasa zabtarewar kasa, da lalata gine-gine.
A makon jiya ne hukumomi suka gargadi mazauna babban birnin yankin Sinchuan, wato Chengdu su miliyan 21 su zauna a gida saboda barkewar cutar korona.
Har wa yau, hukumar da ke kula da ibtila'in girgizar kasa a China, ta ce inda girgizar ta fi shafa shi ne Lunding, wani gari da ke saman tsauni, mai nisan kilomita 226 daga Chengdu.
Gidan talbijin din CCTV ya rawaito cewa mutane 11 sun mutu a birnin Ya'an, yayin da wasu 22 suka mutu a makwabciyar yankin Ganzi. Da yammacin nan an kara tabbatar da mutuwar wasu karin mutane 16, wasu 55 ba a san inda suka shiga ba.
Ana yawan fuskantar girgizar kasa a wasu sassan China, musamman inda ake da tsaunuka.

Asalin hoton, Twitter/Bazoum Mohamed
Kungiyar Jama'atul Kitabu Was-sunnah a Jamhuriyar Nijar ta fara wani zama na kwanaki bakwai da zummar karawa juna sani tsakanin malamai, da ba su horo kan dabarun yin wa'azi ba tare da amfani da kalamai ko lafuzan da ka iya ta da zaune tsaye ba.
Malaman da kungiyar ta gayyato daga wurare daban-daban, za su bai wa malaman jihohi 8 wannan horo, da nufin tsaftace harkokin wa'azi da abin da yta shafi addini a kasar.
Kungiyar Kitabu Was-sunna na aikin na hadin gwiwa tsakaninta da ofishin ministan cikin gida, manufar ita ce magance tsattsauran ra'ayin addfinin Islama, da kaucewa kalaman batanci ga addinin.
Malaman Abdussamad Yahaya shi ne daraktan harkokin addinai a ofishin ministan cikin gida a jamhuriyar Nijar, ya shaida wa BBC cewa: ''Horas da malamai dangane da abin da ya shafi harkokin addfini yana da muhimmanci, da tabbatar da zaman lafiya, saboda mun lura malaman da ke wa'azi ko aikewa da sako da wadanda ke Khuduba a ranar Juma'a, suna bukatar sanin makamar abin da suke yadawa domin kauce wa ta da hankali.''
Ana yawan korafi kan yadda wasu malamai ke zafafawa ko fadar abin da ya zo bakunansu lokutan wa'azi, inda kan tunzura mabiya har a samu barkewar tashin hankali tsakanin mabiya addinai daban-daban, ko ma wadanda ke cikin addinin guda.

Asalin hoton, Getty Images
Hukumomi a Jihar Jigawa da ke arewacin Najeriya sun tabbatar da mutuwar mutane biyar sakamakon hatsarin da kwale-kwalen da suke ciki ya yi.
Lamarin ya faru ne a karamar hukumar Gwaram.
'Yan sanda sun tabbatar da faruwar lamarin, kuma hakan na zuwa kasa da mako guda da wani kwale-kwalen ya yi hatsari a karamar hukumar Miga, inda matasa biyu suka mutu lokacin da suke kan hanyar dawowa daga gona.
Kamar wasu jihohin Najeriya, ana amfani da kwale-kwale a matsayin hanyar sufuri a jihar Jigawa, sai dai ana dora mutane fiye da kima, da rashin rigar kariya idan hatsari ya afku, da sauransu.
Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Jigawa, Lawan Ahmad ya shaida wa jaridar Premium Times cewa hatsarin baya-bayan nan mutanen na dawowa daga sallar Juma'a, lokacin da sukai hatsarin.
Ya kara da cewa: “Mutane biyar ne suka mutu, an kuma yi nasarar kubutar da mutane hudu a a hatsarin.Lamarin ya faru ne da rana misdalin karfe biyu na rana, kuma jirgin ruwan na dauke da fasinjoji tara lokacin da lamarin ya faru,“in ji Lawan.

Asalin hoton, Getty Images
Masu fafutuka sun ce an yanke wa masu rajin kare hakkin 'yan luwadi biyu hukuncin kisa a kasar Iran.
Kungiyar kare hakkin dan adawa ta The Hengaw Organization, ta rawaito wata kotu a Urmia ta samu Zahra Seddiqi Hamedani, mai shekara 31,da Elham Choubdar, 'yar shekara 24, da laifin yada rashawa a duniya.
Ta ce masu shigar da kara na gwamnati sun zargi matan biyu da yada luwadi, da addinin Kirista ta hanyar mu'amala da kafafen yada labaran da gwamnatin Iran take adawa da su.
An shaida wa matan biyu hukuncin da aka yanke musu a kotun da ke Urmia. Kawo yanzu babu wani martani da fannin shari'a ya fitar, sai dai yawancin Iraniyawa sun fantsama shafukan sda zumunta inda suke kiran a janye hukuncin kisan da aka yanke wa matan biyu.
Kungiyar Hengaw ta ce Seddiqi Hamedani, wadda ake kira da sunan Sareh, Ba'Kurdiyya ce da ta fito daga garin Nagesh da ake yammacin yankin Azerbaijan mai iyaka da kasar Turkiyya.

Mutum biyar ne suka mutu sannan gida 3,813 suka lalace sakamakon wani ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi a kananan hukumomi 13 da ke Jihar Katsina a Najeriya.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Jihar ce ta bayyana haka ranar Litinin din nan.
A yayin da yake hira da manema labarai, kakakin hukumar, Malam Umar Muhammad, ya ce mutum uku sun mutu a karamar hukumar Kankara yayin da mutum biyu suka rasu a Mai’adua.
Ya bayyana cewa gwamnatin Jihar tana yin dukkan abin da ya kamata domin ambaliyar ruwa ba ta auku a jihar ba, yana mai cewa an kafa kwamitin gaggawa wajen ganin ba a fuskanci barkewar amai da gudawa ba.
Ya ce: “A Kankara, gidaje 176 sun rushe, a Danja kuma gida je 125 suka lalace, sai kuma Kankia inda gidaje 86 suka rushe, yayin da a birnin Katsina gidaje 620 suka lalace, Musawa 482, Batagarawa 361, Kusada 311 yayin da Sabuwa gidaje 111 suka rushe.
“A Zango, ruwan saman ya lalata gidaje 105, a Batsari, ya rusa gidaje 443, a Funtua gidaje 258 sun rushe, a Safana gidaje 581 sai kuma Ingawa kusan gidaje 154 suka rushe.
“Kazalika gidaje 176 sun rushe yayin da mutum uku suka rasu a ibtila'in a Kankara yayin da gidaje 154 suka lalace a Ingawa.”

Asalin hoton, Getty Images
Wani matashi, mai shekara 18, ya rasa ransa sakamakon yunkurin kubutar da saniyarsa da ta fada cikin wani tafki.
Lamarin ya faru ne dai a unguwar Magina da ke karamar hukumar Buji a jihar Jigawa.
A wata sanarwa da hukumar tsaro ta Civil Defence ta fitar ta ce matashin mai suna Adamu Musa ya rasa ransa ne lokacin da ya yi yunkurin tsamo saniyar tasa wacce ta fada cikin tafki a lokacin da yake kiwo.
Sanarwar ta ci gaba da cewa daya daga cikin shanun nasa ne ta fada cikin tafki, abin da ya sa Adamu ya shiga tafkin domin kubutar da ita.

Asalin hoton, Getty Images
'Yan bindiga sun yi garkuwa da matafiya da dama a kan babbar hanyar Benin zuwa Owo a karamar hukumar Ose da ke jihar Ondo ta Najeriya.
Jaridar Daily Trust ta ambato wata majiya na shaida mata cewa matafiyan na cikin wata babbar motar bas ne da ta taso daga jihar Edo zuwa jihar Ondo da ke kudu maso yammacin kasar.
A yayin da take tabbatar da lamarin, mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Ondo, Funmilayo Odunlami, ta ce ba za ta iya tabbatar da adadin mutanen da lamarin ya rutsa da su ba.
To amma ta ce tuni jami'an tsaron kasar suka fara bincike domin gano tare da kubutar da mutanen.

Asalin hoton, NEMA
Hukumar bayar da agajin gaggawar ta Najeriya ta ce an samu karin adadi na wadanda suka mutu sakamakon ruftawar wani gini a birnin Legas da ke kudu maso yammacin kasar.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar ta shaida wa BBC cewa an samu karin gawarwaki uku a yau Litinin yayin da ake ci gaba da aikin ceto a wajen da ginin ya fadi.
A ranar Lahadi ne dai ginin mai hawa bakwai da ke tsakiyar birnin ya rufta
Kawo yanzu dai ba a bayyana dalilin ruftawar ginin ba.
A wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar, ta ce kwamishinan tsara birane na jihar Dakta Idris Salaka ya yi murabus a wani matakin farko na sauya fasalin hukumar, an kuma gargadi duka sauran ma'aikatar hukumar da su girmama doka.
Faduwar gine-gine dai ba sabon abu ba ne a birnin Legas, inda ake zargin mazauna birnin da yin watsi da dokokin da hukumar tsare birane ta jihar ta gindaya kafin aiwatar da gini a birnin.

Asalin hoton, PR Nigeria
Shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya Dakta Daniel Okoh, ya umarci shugabannin Kiristoci da majami'un da ke fadin kasar da kada su shiga harkokin zaben kasar.
Jaridar punch a Najeriya ta ambato mista Okoh na umartar 'yan kasar da su yi nazari mai zurfi wajen zabar wanda zai jagoranci kasar a zaben shugaban kasar da ke tafe.
Mista Okoh ya yi wannan kira ne a birnin Onitsha lokacin bikin zagayowar ranar haihuwar shugaban Cocin Mission International, Bishop Paul Nwachukwu.
Ya ce ya yi imanin cewa akwai muhimmiyar rawa da majami'u za su taka wajen samar da shugaban kasar na gaba.
''Bai kamata majami'u su saka hannu cikin al'amuran zabe ba, to amma ya wajaba a kansu su tabbatar da cewa sun taimaka wa mutane wajen zabar shugaban da ya dace, saboda makomar kasar na hannunsu'', in ji shi.

Asalin hoton, NG police
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bankaɗo wasu kadarori 14 mallakar tsohon shugaban rundunar tattara bayanan sirri ta hukumar 'yan sandan kasar DCP Abba Kyari.
Jaridar Punch a Najeriya ta ruwaito cewa kadarorin sun hadar da manyan kantunan sayayya, da gidaje, da filin wasan polo, da filaye tare kuma da gonaki.
An zargi Kyari da kin bayyana kadarorin nasa dake wurare daban-daban a birnin Tarayya, Abuja da birnin Maiduguri na jihar Borno.
An kuma gano sama da naira miliyan 207 da euro 17,598 a asusun ajiyarsa na bankunan GTB, da UBA, da kuma bankin Sterling.
A cikin sabbin tuhume-tuhume 24 da daraktan hukumar gabatar da kara da ayyukan shari'a ya gabatar, ya ce babban lauyan gwamnatin kasar ya yi zargin cewa Abba kyari ya ki bayyana wa hukumomi wasu ƙaɗarorin nasa.
Haka kuma gwamnatin tarayya ta shigar da wasu tuhume-tuhume daban guda 24 a kan Sunday Ubua, tsohon mataimakin Abba Kyarin, wanda shi ma tuni aka dakatar da shi.

A yau ne Kungiyar masu dillacin man fetur na arewacin Najeriya suka fara yajin aiki, bayan da suka zargi hukumomin da ke kula da safarar man fetur ta ruwa da na tudu da rike musu kudin dako tsawo watanni 8.
Wannan dalili ne yasa suka fara yajin aikin gargadi na tsawon kwana uku, tare da dakatar da kai mai zuwa duk wani gidan mai dake jihohin arewacin kasar.
Wakilinmu da ke Kano da ya ziyarci NNPC defo da ke unguwar Hotoro ya ruwaito cewa ya ga wasu motocin makare da mai, amma an hana su tafiya sakamakon yajin aikin.

Asalin hoton, bbc



Asalin hoton, others
Dan takarar majalisar dattawan Najeriya a jam'iyyar APC, Bashir Machina, ya musanta wasu rahotonni da ke cewa ya janye daga takarar da yake yi ga shugaban majalisar dattawan kasar Sanata Ahmad Lawan.
Wata wasika ce dai da ta karade shafukan sada zumunta ta bayyana cewa Machina ya janye takarar da yake yi ta Sanatan Yobe ta Arewa, kuma ya fice daga jam'iyyar APC.
Amma a sanarwar da ya fitar, Bashir Machina, ya ce wannan wasika ba daga hannunsa ta fito ba, sannan sakon da take dauke da shi ba gaskiya ba ne.
Ya kuma yi kira ga shalkwatar jam'iyyar APC ta kasa da ta yi watsi da wannan wasika, yana mai cewa ya umarci lauyoyinsa da su dauki matakin shari'a ga wadanda suka kirkiri wasikar.

Asalin hoton, Getty Images
Kotun Kolin Kenya ta tabbatar da William Ruto a matsayin zababben shugaban kasar, a yayin da ta yi watsi da karar da da aka shigar gabanta ana neman ta soke zaben shugaban kasar.
Abokin karawar tasa a zaben, Raila Odinga, tare da wasu mutane ne suka shigar da karar, inda suke zargin tafka magudi a zaben da aka gudanar ranar 9 ga watan Agusta.
Mista Ruto ya yi nasara da kashi 50.5 cikin dari na kuri'un da aka kada.
A mako mai zuwa ne za a rantsar da Mista Ruto, mai shekara 55, a matsayin shugaban kasar na biyar.

Asalin hoton, Getty Images
Wasu takardu da BBC ta gani sun nuna yadda Tarayyar Turai ke duba yiwuwar daukar tsauraran matakai domin shawo kan matsalar tsadar makamashi.
Daftarin na kunshe da tsayar da farashi na wucin-gadi, da rage amfani da wutar lantarkin da kuma taimaka wa kasuwar makamashi.
Ana cikin damuwa sosai tun bayan da Rasha ta sanar da cewa ba za ta sake buɗe kafar tura gas Turai ba.
Ministocin makamashin kasashen Turai za su gudanar da taro domin tattauna matsalar a cikin wannan makon.

Asalin hoton, saudi gazzet
Shugaban kasar China, Xi Jinping, ya aike da wasika zuwa ga Sarki Salman na Saudiyya, domin bayyana yadda alaka tsakanin kasashen biyu ke kara yaukaka.
Shugaban ya bayyana yadda kasarsa ke goyon bayan kudurin Saudiyya na karbar bakuncin bikin bikin baje-kolin hajoji da fasahohi na duniya da za a yi a shekarar 2030.
Yayin da yake karbar wasikar a birnin Riyad, karamin ministan harkokin kasashen waje na Saudiyya, Waleed bin Abdulkarim Al-Khuraiji, ya bayyana yadda kyakkyawar alaka tsakanin kasashen biyu, ke taimaka wa al'umomin kasashen ta fannoni da dama.

Asalin hoton, others
Mutum tara sun mutu yayin da wasu goma suka samu raunuka a wani mummunan hadarin mota da ya auku a yankin Yangoji-Abaji da ke Abuja babban birnin Najeriya
Jami'in hulda da jama'a na hukumar kiyaye hadura ta Najeriya FRSC, Bisi Kazeem ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai.
Kamfanin dillacin labaran kasar NAN ya ambato Mista Kazeem na cewa hadarin ya auku ne jiya da safe.
Ya kara da cewa motar daukar fasinjan, wadda ta taso daga Osun zuwa Katsina, ta yi karo da motar daukar kaya.
Sanarwar ta ce ''Lamarin ya rutsa da mutum 22, kuma dukkansu maza ne, goma sun samu raunuka, yayin da tara suka mutu''.
A Najeriya dai ana yawan samun haduran mota a kan titinan kasar, lamarin da masana ke alakantawa da rashin kyawun hanyoyin kasar, tare da gudun wuce-kima, da tukin ganganci da ake yawan zargin direbobin da aikatawa