Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

An dakatar da daukar sabbin 'yan sanda aiki a Najeriya

Wannan shafin na kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a fadin Najeriya da sauran lungu da saƙo na duniya.

Rahoto kai-tsaye

Aisha Shariff Bappa and Sani Aliyu

  1. Ana tuhumar 'yan sanda kan kama amarya da laifin sata a wajen biki

    Rundunar 'yan sanda a Uganda na tuhumar wasu jami'anta hudu da laifin kama wata amarya a wajen biki inda suke zarginta da laifin sata.

    Mai magana da yawun rundunar, Fred Enanga, ya ce ana tuhumar 'yan sandan da yin abin da bai dace ba lamarin da ake gani zai sa su iya rasa aikinsu.

    'Yan sandan sun kama amaryar ne ana tsaka da biki ranar Asabar da daddare inda suka kai ta ofishinsu da ke Mbararata, a yammacin kasar ta Uganda ta kuma shafe daren ranar sai washegari da safe aka sake ta.

    Rundunar ta ce jami'an nasu sun kama matar ne ba tare da kwakkwarar hujja ba.

    Mr Enanga ya ce lamarin sam bai yi dadi ba, domin ga amaryar, ranar farin cikinta ya zame mata ranar bakin ciki.

    Jami'in dan sandan ya ce yanzu haka an kama daya daga cikin 'yan sandan da suka aikata wannan rashin kirki, sauran ukun kuma sun buya in da ake nemansu ruwa a jallo.

    Shugaban wajen da amaryar ta yi aiki a baya ne ya zargeta da sata shi ya sa ya fada wa 'yan sandan hudu su kuma suka dira wajen biki tare da awon gaba da uwar biki.

  2. Ba zan mika jami'oin gwamnatin tarayya ga jihohi ba - Atiku

    Dan takarar shugaba Najeriya a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce ba zai mika wa gwamnatocin jihohin kasar ragamar tafiyar da jami'o'in gwamnatin tarayya ba.

    Cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Paul Ibe, ya fitar ya ce sun lura cewa an juya maganar da dan takarar shugaban kasar na PDP ya yi a wajen wani babban taro na kungiyar lauyoyin Najeriya da ya gudana a Legas a kan batun da ya shafi bangaren ilimi da hanyoyin da zai bi wajen warware matsalolin da bangaren ke fuskanta.

    Ya ce a cikin bayanan Atiku, bai ce zai mika ragamar kula da jami'in gwamnatin tarayya ga jihohi ba idan har aka zabe shi a zaben shugaban kasa mai zuwa.

    Wannan ba daidai ba ne don bai hadi haka ba a lokacin da yake bayar da amsa a kan tambayoyin da aka yi masa game da manufofinsa in ji shi.

    Ya ce abin da Atiku Abubkar yake nufi shi ne matakan da zai bi daki-daki na rage wa gwamnatin tarayya nauyin tafiyar da jami'on da ke karkashinta.

    A don haka batun cewa zai mika wa gwamnatocin jihohi raga,ar tafiyar da jami'oi ba gaskiya ba ne.

  3. Assalamu Alaikum

    Barkanmu da hantsin Talata tare da fatan mun tashi lafiya.

    Ku biyo ni Aisha Shariff Bappa domin sanin halin da duniya ke ciki, musamman a Najeriya da Nijar da maƙotansu.

    Mu je zuwa!