Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

An fara ƙirga ƙuri'u a zaɓen gwamnan Jihar Ekiti

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Mustapha Musa Kaita and Umar Mikail

  1. An soma kaɗa ƙuri'a a zaɓen gwamna a Ekiti

    An soma tantance masu kaɗa ƙuri'a da kuma dangwala ƙuri'a a wasu rumfunan zaɓe tun da misalin 8:30 na safe.

    Wasu daga cikin rumfunan zaɓen da wakilan BBC suka ziyarta a Ado-Ekiti musamman mazaɓar Oke-Inyimi, tuni aka fara zaɓe a rumfa mai lamba biyu da mai lamba uku da huɗu da shida.

    Owolabi Comfort ita ce mace ta farko da ta soma zaɓe a rumfa mai lamba biyu.

    Ana amfani da sabuwar na'urar Bvas wurin tantance masu zaɓen.

    Na'urar Bvas wato Bimodal Voter Accreditation system, an soma amfani da ita ne a zaɓen gwamna a Anambra a 2021 duk da cewa an samu tangarɗa a wasu wuraren.

    Sai dai a zaɓen Ekiti, hukumar ta INEC ta ce za sake inganta na'urar ta Bvas inda ta ce tana sa ran za ta yi aiki da kyau.

  2. 8:30 na safe za a soma zaɓe da tantance ƴan takara a Ekiti - INEC

    Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya INEC wadda ita ce alhakin zaɓe a Najeriya ya rataya a wuyanta ta ce za a soma tantance ƴan takara da kuma gudanar da zaɓe da misalin 8:30 na safe a kuma a kammala 2:30 na rana.

    Hukumar ce ta bayyana haka a shafinta na Twitter inda ta ce duk wanda ya bi layin zaɓen kafin 2:30 na rana za a bar shi ya dangwala.

  3. 'Jami'an INEC sun isa rumfunan zaɓe da wuri'

    Wasu daga cikin mazauna Jihar Ekiti sun soma fita zuwa rumfunan zaɓe domin kaɗa ƙuri'a a zaɓen gwamnan jihar.

    Tun ƙarfe 7:15 na safe jami'an hukumar INEC suka soma isa rumfunan zaɓe a Ado-Ekiti babban birnin jihar.

    Wannan na zuwa ne bayan INEC ɗin ta kammala rarraba kayayyakin zaɓe tun da misalin ƙarfe 3:00 na asuba.

    Wasu daga cikin masu zaɓen sun shaida wa BBC cewa jami'an na INEC waɗanda akasarinsu masu yi wa ƙasa hidima ne na NYSC sun isa wuraren zaɓen da wuri.

  4. Yadda masu zaɓe suka yi samako zuwa rumfunan zaɓe a Ekiti

    Jama'a da dama a Jihar Ekiti sun yi samako inda suka fita zuwa rumfunan zaɓe.

    Ana sa ran da misalin ƙarfe 8:30 na safe za a soma tantance masu zaɓe da gudanar da zaɓen.

  5. A yau ake gudanar da zaɓen gwamna a Ekiti

    A yau Asabar ake gudanar da zaɓen gwamna a Jihar Ekiti da ke kudancin Najeriya.

    `Yan takara goma sha shida ne suke fafatawa a zaben.

    Duk wanda ya yi nasara a zaɓen zai maye gurbin gwamna mai barin gado Kayode Fayemi na Jam'iyyar APC, wanda a cikin shekarar nan wa'adin mulkinsa zai ƙare.

    Tun a watan Janairu ne jam'iyyu suka gudanar da zaɓukan fitar da gwanayensu, kuma sunayen waɗanda hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasar INEC ta tantance ne kawai za su kasance a kan ƙuri'ar zaɓen.

    Ga dai bayanan wasu ƴan takarar da INEC ɗin ta tantance. An zaɓe su ne bisa waɗanda BBC ta iya samun su ko bayanansu a intanet, ba don wani ya fi wani ba.

    • BIODUN ABAYOMI OYEBANJI - APC
    • BISI KOLAWOLE - PDP
    • OLUSEGUN ONI - SDP
    • ADEBOWALE RANTI AJAYI - YPP
  6. Barkanmu da safiya

      • Marubuci, Mustapha Musa Kaita
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multi-Media Broadcast Journalist

    Jama'a barkanmu da safiyar Asabar, 18 ga watan Yunin 2022. A yau ma za mu ci gaba da kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za ku iya ziyartar shafinmu na Facebook ko Twitter ko kuma na Instagram domin bayyana ra'ayoyinku kan irin labaran da muke wallafawa ko kuma tafka muhawara a kai.