Kamfanin rarraba wutar lantarki a Najeriya da ke bai wa yankunan Abuja da jihohin Nasarawa da Kogi wuta ya nemi afuwar kwastomminsa, yana mai bayyana matakan da yake ɗauka wajen inganta samar da lantarkin.
Cikin wata sanarwa da babban daraktan kamfanin, Adeoye Fadeyibi, ya fitar a yau Asabar ta ce kamfanin na Abuja Elecricity Distrubution Company (AEDC) ya ƙaddamar da wasu shirye-shirye don haɓaka samar da wutar.
A cewar Mista Fadeyibi, AEDC zai sayo wasu sabbin na'urorin raba wuta 34 ta cikin shirin 40 Quick WIn Projects don rage yawan lodin da ke kan wasu na'urori a sassan Abuja.
Kazalika, kamfanin ya ce zai duƙufa wajen gyara wasu na'urorin da suka kai 78 duka a cikin shirin.
Najeriya na fama da ɗaukewar wutar lantarki a lokuta da dama a baya-bayan nan sakamakon lalacewar babban layin lantarki na ƙasa.
Gwamnati kan zargi 'yan daba da lalata bututan iskar gas da ke bai wa tashoshin wutar makamashin aiki.
-
Mene ne babban layin wutar lantarki na Najeriya kuma yaya yake aiki?