Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

'Yan bindiga sun sace limamin coci da matarsa a Kwara

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Halima Umar Saleh and Nasidi Adamu Yahaya

  1. Matasan Afirka ba su da ƙwarin gwiwa a kan alƙiblar ƙasashensu - Rahoto

    Wani sabon bincike ya gano cewa kaso biyu bisa uku na matasan Afirka ba su da ƙwarin gwiwa a kan alƙiblar ƙasashensu, to amma suna cike da ƙwarin gwiwa a kan burin da suka sanya a gaba.

    Masu binciken sun tattauna da matasa fiye da 4,000 a ƙasashen Afirka 15 don gudanar da binciken.

    Fiye da rabinsu sun ce suna so su bar ƙasarsu su tafi wata kasa, yayin da kashi 80 cikin 100 nasu kuma ke da burin fara kasuwanci da kansu.

    Matasan sun ce ya kamata gwamnatocinsu su samar da ayyukan yi masu kyau fifiko, abin da zai iya rage cin haci da rashawa da kuma yakin da ake da sauyin yanayi.

    Kuma hakan zai matuƙar taimakawa kasashen wajen samun ci gaba.

  2. Barka da safiya

    Masu shigowa shafin BBC Hausa barkanmu da safiyar Litinin.

    Ku kasance da mu a wannan sahar domin karanta labarai da rahotanni na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya.

    Sunana Halima Umar Saleh, kuma ni zan ja ragamar shafin, kafin daga bisani abokin aikina Nasidi Adamu Yahaya ya karbe ni.