Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

'Yan bindiga sun sace limamin coci da matarsa a Kwara

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Halima Umar Saleh and Nasidi Adamu Yahaya

  1. Mu kwana lafiya

    A nan za mu rufe wannan shafi da ke kawo muku labarai da rahotanni kai-tsaye.

    Ku biyo mu gobe da safe domin samun sabbin labaran da suka shafi rayuwarku.

    Kafin nan, kuna iya ci gaba da karanta labaranmu da kallon bidiyo a babban shafinmu bbchausa.com, ko kuma shafukanmu na sada zumunta.

    Mu kwana lafiya.

  2. Yadda mata ke tururuwar karba wa 'ya'yansu madarar tamowa a Katsina

    Danna hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

    Cutar tamowa cuta ce da masana ke alakantawa da rashin samun isasshe da kuma ingataccen abinci ga kananan yara.

    Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya ce kusan yara miliyan biyu ne ke ke fama da tamowa a Najeriya kuma biyu cikin goma ne kawai ke samun magani. Kungiyar samar da abinci ta IPC ta yi hasashen cewa za a samu karuwar yara da ke fama da cutar a Najeriya.

    IPC ta ce mafi yawan lokuta cutar tafi kama yara 'yan kasa da shekara biyar.

    A sibitin na garin Daddara ya kasance matattara ta yaran masu fama da cutar kuma iyayensu na ziyartar asibitin ko wace rana domin nemawa 'ya'yansu madarar tamowa wacce ke ta da komadar yaran.

    Shugaban asibitin Ibrahim Abubakar ya ce suna bai wa yara 500 zuwa 600 maganin tamowa a kowane mako.

    Ibrahim ya ce kungiyar likitoci da ke ba da agaji ta Doctors Without Borders ne ke samar da maganin tamowan.

    Ya kara da cewa matsalar da suke fuskanta itace ta rashin tsaro domin kuwa a wasu lokuta 'yan bindiga na kwace madarar da akayi domin yara marasa lafiya. Sannan wasu matan ma na sayar da madarar maimakon bai wa 'ya'yansu.

  3. Masu ikirarin kishin Musulunci sun kashe fararen-hula 50 Burkina Faso

    Gwamnatin Burkina Faso ta ce wasu da ke zargi masu ikirarin kishin Musulunci ne sun kashe fararen-hula akalla 50 a wani hari da suka kai kauyen Seytenga da ke arewacin kasar.

    Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah-wadai da hare-haren da ake kai wa kan fararen-hula.

    Harin na daya daga cikin mafi muni da aka kai tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Janairu, yayin da manyan sojoji suka hambarar da Shugaba Roch Marc Christian Kabore bisa zargin gaza magance matsalar tsaro.

    Mai magana da yawun gwamnatin Burkina Faso ya ce masu ikirarin kishin Musulunci sun kai hari a Seytenga domin yin raddi ga farmakin da sojoji suka kai musu a makon jiya.

    Ana fargabar cewa adadin fararen-hular da aka kashe a harin na karshen makon jiya zai karu matuka - wasu rahotanni sun ce mutum fiye da 100 aka kashe.

  4. Bidiyon yadda aka rushe gidajen Musulmai bayan zanga-zangar adawa da ɓatanci ga Annabi

    Danna hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

    Hukumomi a Jihar Uttar Pradesh da ke kasar India sun rushe gidajen Musulmai da dama wadanda suka yi zargin cewa suna da alaka jerin zanga-zangar da aka gudanar kwanakin baya wadanda suka rikide zuwa tarzoma.

    An gudanar da jerin zanga-zangar ne bayan wasu jiga-jigan jam'iyyar Bharatiya Janata Party guda biyu sun yi kalaman batanci kan Annabi Muhammad (SAW).

  5. 'Yan bindiga sun sace limamin coci da matarsa a Kwara

    Wasu 'yan bindiga sun sace Bishop na darikar Anglican, Rabarand Oluwaseun Aderogba da ke Jebba a Jihar Kwara ta Tsakiyar Najeriya tare da matarsa da dirabansa.

    Gidan talbijin na Channels TV ya rawaito cewa an sace mutanen ne ranar Lahadi da maraice a kan hanyar Oyo/Ogbomoso da ke Jihar Oyo.

    Kakakin rundunar 'yan sandan Jihar, Adewale Osifeso, ya tabbatar da sace mutanen a wata sanarwa da ya fitar.

    Ya kara da cewa wani mutum mai suna Rabarand Adekunle Adeluwa ne ya kai wa 'yan sanda labarin sace takwaransa.

    A cewar Osifeso, binciken farko ya nuna cewa motar limamin cocin ce ta samu matsala a yayin da suke tafiya daga Yewa da ke Jihar Ogun zuwa Jebba a Jihar Kwara.

    Ya kara da cewa an bai wa mataimakin Kwamishinan 'yan sandan yankin umarnin gano da kuma ceto mutanen.

  6. Za a ƙara samun hauhawar farashi da rashin wuta da abinci da fetur a Najeriya - Bankin Duniya

    Babban Bankin Duniya ya yi hasashen cewa ƴan Najeriya da Angola za su fuskanci ƙarin tsanani na hauhawar farashi da rashin wuta da rashin fetur da kuma ƙarancin abinci.

    Waɗannan matsaloli za su zo ne a yayin da farashin ɗanyen fetur ya kai kai dala 120 duk ganga ɗaya, lamarin da ake sa ran zai amfani waɗannan ƙasashen da dama su ne manyan ƙasashen Afirka da suka fi samar da fetur.

    A wani rahoto da Babban Bankin Duniya ya fitar a ƙarshen mako, ya ce "A ƙasashen kudu da hamadar Sahara da dama, za a samu hauhawar farashi da da ƙarancin wutar lantarki da ƙarancin abinci da man fetur."

    Wannan batu na zuwa ne a daidai lokacin da dama Najeriya ke fuskantar matsannacin hauhawar farashi da ƙarin samun layuka a gidajen mai a faɗin ƙasar.

    • Wahalhalu biyar da 'yan Najeriya ke ciki a wannan lokaci
  7. 'Yan sanda sun yi arangama da daliban Islamiyya a Ghana

    'Yan sanda sun yi arangama da dalibai da ke zanga-zanga a wajen makarantarsu a kasar Ghana. Wasu rahotanni sun bayyana cewa an yi amfani da barkonon-tsohuwa da harsasai ko da yake babu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da hakan.

    An kai akalla daliba 20 na makarantar Islamic Senior High School da ke Kumasi asibiti sakamakon raunukan da suka ji ko da yake babu rahotanni kan ko an harbe su da bindiga ne.

    Suna cikin masu zanga-zangar da ke kira a sanya kabarin-tatsine a kan hanyoyin birnin sakamakon yawaitar hadura, a cewar kafafen watsa labarai na kasar.

    Iyaye da dama da ke cike da damuwa sun je makarantar domin sanin halin da 'ya'yansu suke ciki, a cewar, Citi Newsroom.

    'Yan sandan Ghana ba su tabbatar ko musanta cewa sun yi amfani da harsasai na gaske kan masu zanga-zangar ba.

    Kafar watsa labarai ta Citi Newsroom ta wallafa hotunan babban sifeton 'yan sandan kasar yana kan hanyarsa ta zuwa domin ganawa da shugabannin makarantar:

  8. Bidiyon yadda aka ceto yaro ɗan wata 18 daga rijiya

    Rundunar sojin Indiya ta ceto wani yaro ɗan wata 18 daga wata rijiya mai zurfi a jihar Gujarat da ke yammacin ƙasar.

    Yaron mai suna Shivam ya faɗa rijiyar ne mai zurfin mita 90 a bisa tsautsayi.

    Wasu sojoji ne suka yi gaggawar zuwa ƙauyen Dudapur da ke kusa da wata cibiyarsu don ceton yaron.

    An ciro shi ne ta hanyar amfani da ƙugiyar da aka ɗaure a jikin igiya, sannan aka kai shi asibiti mafi kusa, inda aka sallame shi bayan kwana biyu.

    Danna hoton da ke ƙasa don kallon bidiyon

  9. Musulman Indiya na ci gaba fushi kan kalaman ɓatancin da jami'an jam'iyya mai mulki suka yi

    Al'ummar Musulmai a Indiya na ci gaba da nuna fushinsu kan ɓatancin da mai magana da yawun jam'iyyar BJP mai mulki ta yi kan Annabi Muhammad SAW.

    Wani dandazon jama'a ya kai hari kan wani jirgi a jihar West Bengal.

    An kuma ta yin Allah wadai da yadda aka lalata gidajen wasu Musulmi a jihar Uttar Pradesh da ƴan sanda suka ce suna da hannu a rikicin da ya faru.

    Sai dai hukumomi sun ce ƴan sandan sun lalata gine-ginen da aka yi su ba bisa ƙa'ida ba ne.

  10. Ukraine ta ce sojojin Rasha sun fatattaki rundunoninta daga tsakiyar birnin Severodonets

    Ukraine ta ce sojojin Rasha sun fatattaki rundunoninta daga tsakiyar birnin Severodonetsk - yankin da fada ya yi zafi a baya-bayan nan.

    Sojojin Ukraine sun ce ana ci gaba da gwabza fada a birnin amma wani jagoran mayaƙan sa kai na Rasha ya ce ƴan Ukraine din da ke wajen a yanzu suna da zaɓin miƙa wuya ko mutuwa.

    Ukraine ta bayyana cewa Rasha ta kara shigar da karin makamai da motoci masu sulke zuwa wasu yankuna masu makwabtaka a yunkurinta na yi wa dakarun Ukraine kawanya.

    A cewar wakilin BBC, yaki ne ake kan tituna kuma yana ci gaba da ƙazanta kuma iya abin da muka sani, kowane bangare na tafka asara.

    Rasha na amfani da damarta ta samun atilari wajen kai hare-hare a Ukraine.

  11. DSS ta kama wani babban kwamandan ISWAP a Kano

    Rundunar tsaro ta farin kaya ta DSS a Najeriya ta tabbatar da kama kama wani da take zargin ɗaya ne daga cikin manyan kwamandojin kungiyar ISWAP a Kano.

    Rundunar tsaron ta dai kama wanda ake zargin tare da wasu daga cikin yaransa a daidai lokacin da suke shirya kai wasu hare-hare na ta'addanci a Kano.

    Mutumin, wanda jami'an DSS suka kama da ake yi wa laƙabi da Malam Abba, an kama shi ne a unguwar Samegu a yankin karamar hukumar Kumbotso a Kano.

    DSS ta ce ta sami nasarar kama Malam Abba da waɗanda aka kama shi da su bayan samun wasu bayanan sirri.

    Sannan wanda ake zargin shi ne mai bayar da horo, da shirya hare-haren da ISWAP din za ta kai a jihar.

    Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da babban hafsan tsaro Najeriya janar Lucky Irabor ke cewa rudunar tsaron kasar ta daƙile wani yunƙurin kai hari a Kano wanda suka ce zai iya zama "mafi muni" a ƙasar.

    Janar Irabor ya ƙara da cewar sun daƙile harin ne a Kano cikin makon da aka kai hari wata coci da ke garin Owo na Jihar Ondo, wanda 'yan bindiga suka kashe fiye da mutum 40.

    Sannan sun gano kayayyakin da ake haɗa abubuwan fashewa da su, tare da ƙwace ƙunshin makamai masu yawan gaske da miyagu ke ƙoƙarin yin amfani da su a sassan ƙasar ciki har da Abuja.

    Idan za a iya tunawa a ranar 17 ga watan Mayu aka sami fashewar wata tukunyar gas a titin Aba da ke Sabon gari a Kano, da ya yi sanadiyar mutuwar mutum tara tare da jikkata wasu da dama.

    Sai dai an sami rabuwar kai tsakanin al’umma mazauna yankin da jami’an tsaro, inda mazauna yankin ke cewa bom ne, yayin da jami’an tsaro ke cewar tukunyar gas ce da ke waje ta fashe.

    Haka zalika kwanaki kadan da faruwar wannan al’amari rudunar ƴan sandan Kano ta ce ta ga wata mota maƙare da kayan hada bom a unguwar Bugaje a yankin karamar hukumar Kumbotso.

    Jami'an tsaron sun yi zargin cewar an shiga da motar ne daga jihar Jigawa da ke maƙwabtaka da Kanon.

    Tuni dai hukumomi a Najeirya suka tabbatar da ayyukan Mayakan ISWAP a jihar Kaduna da wasu dazuzzuka da ke arewa maso yammacin Najeirya, da ake fama da matsalolin masu garkuwa da mutane.

  12. Wane ne daliget, kuma mene ne aikinsa?

    A filinmu na Amsoshin takardunku na wannan makon mun amsa tambayar da aka aiko mana a kan Wane ne daliget, yaya ake zarbarsa, kuma mene ne aikinsa?

    Awwal Ahmad Janyau ya tuntuɓi wani tsohon an siyasa Alhaji Garba Kwaccido wanda ya amsa tambayoyin.

    Danna hoton da ke ƙasa don sauraron shirin:

  13. Fafaroma ye bai wa ƙasashen Afirka biyu haƙuri kan fasa ziyararsu da ya yi niyya

    Fafaroma Francis ya nemi afuwar Jamhuriyyar Dimokradiyyar Congo da Sudan ta Kudu kan fasa ziyarar da ya yi niyyar kai wa a watan Yuli saboda yanayin jikinsa.

    Ya shirya kai ziyarar biranen Kinshasa da Goma na Jamhuriyyar Dimokradiyyar Congo da a ranar 2 da 5 ga watan Yuli kafin daga bisani ya wuce Juba, babban birnin Sudan ta Kudu, a ziyararsa ta kwana biyu.

    Haka kuma, fadar Vatican a ranar Juma'a ta sanar da cewa fafroman mai shekara 85 ya ɗage ziyarar ne saboda ciwon gwiwa da yake fama da ita .

    Fafaroman ya shaida wa dubban mutane a dandalin St Peter cewa "ina mai ba ku haƙuri, saboda ciwon ƙafata, dole ta sa na fasa ziyarar da na yi niyya zuwa ƙasashenku."

    Ya bayyana cewa yana fatan zai sake sanya ranar ziyarar "a nan kusa."

  14. Gwarzon direban da ya tuƙa tanka mai cin wuta don kare mutane a Najeriya

    An yi ta kwarzanta wani ɗan Najeriya saboda sayar da rayuwarsa da ya yi ya tuƙa wata tankar fetur da ta kama da wuta a ƙoƙarinsa na fitar da ita daga wajen da mutane suke don kar a yi ɓarna a birnin Warri na jihar Delta.

    Ejiro Otarigho ya shai da wa BBC cewa "Abu ɗaya ne ya zo raina shi ne in tuƙa tankar mai cin wuta har zuwa wajen kogi mafi kusa.

    "Mataimakina ne ya ankarar da ni cewa tankar tamu ta kama da wuta. Kuma wuta ce ganga-ganga ta kama," a cewarsa.

    Mista Ejiro ya sauke wani lodi kenan daga tankar tasa sannan ya kama hanyar zuwa wani wajen sai abin ya faru.

    Ba tare da ɓata lokaci ba, ya shaida wa mataimakin nasa ya sauka daga motar inda shi kuma ya ƙara mata wuta don ficewa daga cikin mutane don gudun jawo ɓarna.

    A wannan yanayin, duk wani dan kukure daga Mista Otarigho ko kuma a sau wata fashewa, da za su iya jawo mummunan bala'i.

    "Niyyata ita ce na tuƙa motar har zuwa wajen kogi. Amma da na isa can sai sitiyarin motar ya cije sai na kasa ci gaba da tuƙawa," ya faɗa.

    "Na ce idan na tuƙa kai tsaye, motar na iya faɗuwa kuma za ta iya ƙara jawo matsala. Don haka dole na tsaya a wani buɗaɗɗen waje."

    A ƙarshe Mr Otarighoya samu nasarar kawar da tankar daga cikin mutane, kuma a wani bidiyo da ya yaɗu an ga yadda muatne suka baibaye shi suna murna.

    Mr Otarigho ya tsira lafiya ba abin da ya same shi sai hayaƙi da ya shaƙa da kuma ƴan raunuka da ji a jikinsa.

  15. Al-Shabab na tursasa wa manoma biyan haraji a Somaliya

    Haraji mai tsanani da ƙungiyar al-Qaeda mai ƙawance da al-Shabab ta ƙaƙaba wa mutane a wasu yankunan Somaliya ya sa manoma ba sa iya girbe amfanin gonarsu a yayin da ake fama da matsannacin fari.

    Abdirahman Abdishakur Warsame, jakada na musamman ga shugaban ƙasar Hassan Sheikh Mohamud a kan batun farin, ya ce harajin na al-Shabab na tursasa wa manoma tserewa su bar gonakinsu da gidajensu.

    Mr Warsame ya shaida wa shugaban ƙasar da shugabannin gundomomin ƙasar hakan ne a jiya Lahadi a wani taro da aka shafe kwana biyu ana yi.

    Ya ce fiye da ƴan Somaliya miliyan bakwai ne fari ya shafa. Kuma mutum 250,000 daga cikinsu na fuskantar matsananciyar yunwa.

    Al-Shabab na yawan amfani da yunwa da ake fama da ita a ƙasar don ƙara fito da kanta da kuma bayar da tallafi ga jama'a.

  16. 'Zai yi wuya INEC ta iya yi wa ƴan Najeriyar da ke son yin katin zaɓe rijista'

    Wasu daga cikin ƙungiyoyi masu zaman kansu a Najeriya sun ce zai yi wuya hukumar zaɓen ƙasar ta iya yi wa ƴan ƙasar da ke son yin katin zaɓe rijista, saboda rashin wadatattun kayan aikin.

    Kungiyoyin dai sun ce hukumar zaben kasar na da ƙarancin wadatattun ma'aikatan da suka kamata wajen yi wa 'yan kasar rijista, da ƙalubalen da ke tattare da na'urorin da ake amfani da su wajen yin rijistar.

    Jihar Kano na daga cikin jihohi a Najeriya da ake da ƙarancin waɗanda ba su fito yin katin zaɓen ba, inda kungiyoyin su ma suka alaƙanta hakan da gajen haƙurin waɗanda suka yi rijista zuwa ofishin hukumar zabe don a dauki bayanansu.

  17. Babban layin lantarki na Najeriya ya ƙara samun matsala, karo na biyar cikin wata biyu

    Babban layin wutar lantarki na Najeriya ya samu matsala inda aka ɗauke wuta a kafatanin ƙasar a jiya Lahadi 12 ga watan Yuni.

    Wannan lamari shi ne karo na huɗu da babban layin wutar lantarkin ya samu matsala tun watan Afrilun da ya gabata, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

    Wani kamfanin wutar lantarki ya ce an ɗauke wutar ne da misalin ƙarfe 6 na yamma bayan da wutar da ake samarwa a tasoshi daban-daban a fadin ƙasar ta ragu.

    Kamfanin rarraba wutar lantarkin na ƙasa TCN ya ce wutar da ake samarwa ta ragu amma bai faɗi abin da ya jawo hakan ba.

    A ranar 12 ga watan Mayu ma sai da babban layin wutar lantarkin ya samu matsala, inda mafi yawan yankunan ƙasar suka rasa wuta.

    Sannan ranar 8 ga watan Afrilu ma matsalar ta sake faruwa ciki har da babban birnin ƙasar Abuja.

  18. Rasha na ci gaba da samun kuɗi wajen sayar da fetur da gas duk da takunkumin Amurka

    Wani sabon bincike ya gano cewa Rasha na ci gaba da samun makuɗan kuɗi wajen sayar da mai da kuma iskar gas ɗinta, duk da takunkumin da take fuskanta daga wasu kasashen bayan data fara mamaya a Ukraine.

    Wata Cibiyar bincike a kan makamashi da kuma iska mai tsafta, ta ce Rasha ta samu kusan dala biliyan 100 a kan manta a lokacin da ta cika kwana 100 da fara yaki a Ukraine.

    Wakilin BBC ya ce binciken Cibiyar ya gano cewa takunkumin da aka sanyawa Rasha ya sa abin ya zame mata gobarar titi a Jos, saboda farashin mai da iskar gas dinta ya ninka a kan na baya.

  19. Koriya ta Kudu ta damu da gwajin atilari da Koriya ta Arewa ta yi

    Mahukunta a Koriya ta Kudu sun gudanar da wani taro na tsaro don tattaunawa a kan gwajin makaman da Koriya ta Arewa ta yi a baya-baya nan.

    Rundunar sojin kasar ta ce Koriya ta Arewan ta harba makaman atilari da dama a safiyar jiya Lahadi, kwana guda bayan Kim Jong-Un, ya sha alwashin inganta ƙarfin sojin kasarsa.

    A yayin taron, jami'an kasar sun ƙara tabbatar da matsayarsu ta mayar da martani a nutse kuma cikin hikima.

    Koriya ta Arewa dai ta yi gwajin jerin makamai a shekarar nan duk da tana fuskantar takunkumin kasashen duniya, sannan Koriya ta Kudu da kuma Amurka sun yi gargadin cewa Koriya ta Arewan na shirin gwajin wani sabon makamin nukiliya.

  20. 'Ƙoƙarin gwamnatin Najeriya ya yi tasiri wajen raguwar kai hare-hare da kashe-kashe a Mayu'

    Wani rahoton tsaro a Najeriya ya ce ƙoƙarin gwamnatin ƙasar ya yi gagarumin tasiri wajen raguwar kai hare-hare da kashe-kashe da kuma satar mutane don neman kuɗin fansa a watan Mayu, musamman idan an kwatanta da na Afrilu.

    Rahoton na Kamfanin Beacon Consulting ya ce a watan na jiya, an samu hare-hare 421 a fadin Nijeriya, lamarin da ya janyo sace mutum 265 da kuma kashe mutum 913.

    Don jin ƙarin bayani, BBC ta tuntuɓi Dr. Kabiru Adamu, shugaban kamfanin inda Muhammad Annur ya fara da tambayarsa, ko a wanne sashe ne aka fi samun hare-hare cikin watan na Mayu?

    Sai ku latsa hoton nan na ƙasa don sauraron hirar: