Fadar shugaban Najeriya za ta gana da ASUU da shugabannin addinai kan yajin aiki
Nan gaba a yau ne fadar shugaban Najeriya za ta yi wani taron gaggawa tsakanin gwamnati da ƙungiyoyin malamai da ma'aikatan jami'o'i.
Za a yi wannan taro ne a yunƙurin kawo ƙarshen yajin aikin jami'o'in ƙasar.
Farfesa Ibrahim Gambari, shugaban ma'aikata na fadar shugaban ƙasar ne zai jagoranci taro wanda ake sa ran shugabannin addinai ma za su halarta.