A Najeriya wasu daliban jami'a sun yi zanga-zanga dauke da katon allon da aka rubuta “A kawo karshen yajin aikin ASUU,” daliban sun ce za su ci gaba da wannan bore har sai malaman jami'o'in kasar sun janye yajin aikin da suka tafi tare da sake bude jami'o'i domin ci gaba da karatu.
Jaridar Premium Times ta rawaito cewa, daruruwan daliban ne suka rufe manyan hanyoyin da suka taso daga Ibadan da Elesa, da ke kusa da jami'ar Oduduwa.
Wani bidiyo da Premium Times ta samu, daliban na cewa ba sa jin tsoron jami'an tsaro, tare da barazanar zaman dabaro a tituna har sai an bude jami'o'in.
Sun bayyana takaicinsu kan yadda ake ci gaba da yajin aikin, sun kuma nuna takaici kan 'yan siyasa kan yadda sukai shakulatun bangaro da batunsu, ba sa taka rawar da ta dace wajen tabbatar da an biyawa malaman jami'o'in bukatunsu yadda za su koma daukar karatu.
Maimakon hakan sun maida hankali kan sayan fom doin tsayawa takarar zabe a shekara mai zuwa, sun yi tamkar babu abin da ke faruwa.
A farkon makon nan ne, kungiyar malaman jami'o'in ta Najeriya, ASUU, ta sanar da tsawaita wa'adin yajin aikin da suka tafi zuwa makwanni 12 sakamakon rashin cimma matsaya da gwamnati kan bukatunsu.
ASUU ta shiga yajin aikin ne sakamakon abin da ta bayyana gazawar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari wajen aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla a baya game da yadda za a inganta harkokin karatun jami'a na kasar.