Mu kwana lafiya
Ƙarshen rahotannin ke nan a wannan shafin.
Sai kuma gobe, inda za mu wasu sabbi.
Fatan alheri daga BBC Hausa!
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman batutuwan da suka shafi Sallah karama.
Awwal Ahmad Janyau and Umar Mikail
Ƙarshen rahotannin ke nan a wannan shafin.
Sai kuma gobe, inda za mu wasu sabbi.
Fatan alheri daga BBC Hausa!
Manchester United ta kwashi kashinta a hannu a wajen Brighton, abin da ya tabbatar da cewa ba za ta buga gasar Zakarun Turai ta Champions League ba a kaka mai zuwa.
Kazalika, wannan ne karon farko da Cristiano Ronaldo zai rasa gurbin shiga Champions League cikin shekara 19.
Moises Caicedo ne ya fara jefa ƙwallo a ragar United, kafin ƙungiyar ta shiga mummunan hali bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.
Marc Cucurella ya ƙara ta biyu bayan Leandro Trossard ya ba shi ƙwallon, sai kuma Trossard da ya haddasa ƙwallo ta uku da Pascal Gross ya sakaɗa a raga.
Ba a tashi ba sai da Trossard ɗin ya ci tasa bayan VAR ta duba ta saboda zargin taɓawa da hannu.
Da wannan sakamako, an ɗura wa Man United jimillar ƙwallaye 56 a tsawon kakar bana a Premier League, wanda shi ne adadi mafi yawa da aka taɓa zira mata a tarihin gasar.
Wani kofur ɗin ɗan sanda da ke aiki da rundunar 'yan sandan Najeriya reshen Jihar Ebonyi ya shiga hannu sakamakon nuna goyon bayansa ga wata ƙungiyar asiri.
An ga Matthew Isaac a wani bidiyo da ya karaɗe intanet yana rawa tare da ɗaga bindigar da ke hannunsa yayin da yake yabon ƙungiyar asirin.
Kakakin 'Yan Sanda na Ƙasa CSP Muyiwa Adejobi ya faɗa cikin wata sanarwa cewa a yau Lahadi cewa Sufeto Janar Usman Alkali Baba ya yi Allah-wadai da aikin kofur ɗin kuma ya umarci a ɗauki matakin da ya dace.
Sanarwar ta ce "aikin ɗan sandan yunƙuri ne na shafa wa rundunar 'yan sanda baƙin fenti".
"Abin da ya aikata ya saɓa wa dokokin amfani da shafukan sada zumunta da sauran dokokin ɗa'ar dukkan 'yan sanda," in ji shi.
Gwamnatin Najeriya ta roƙi kamfanonin jiragen sama na ƙasar da kada su dakatar da aiki kamar yadda suka yi barazana daga Litinin ɗin nan.
Kafofin yaɗa labarai a ƙasar sun ruwaito wata sanarwa daga ofishin Ministan Sufurin Jiragen Sama Hadi Sirika na cewa hakan zai yi tasiri kan tattalin arziƙin ƙasa "wanda da ma yake a ƙuntace".
Ministan ya bayyana damuwarsa kan "wahalhalun da kamfanonin ke fuskanta wajen samun man jirgin" amma ya ce ma'aikatarsa ba za ta iya yin wani abu ba.
"Abin damuwar shi ne samar da man jirgi ba a ƙarƙashin ma'aikatarmu yake ba, saboda haka iya abin da za ta iya yi shi ne ta tattauna da hukumomi da mahukuntan da za su iya sama wa kamfanonin sauƙi. Tuni aka fara aiwatar da hakan ƙarƙashin minista," in ji sanarwar da Dr. James Odaudu ya fitar.
Kungiyar kamfanonin sufurin jiragen ta AON ta sanar cewa mambobinta za su dakatar da aiki daga ranar Litinin mai zuwa saboda tsadar farashin man fetur, wanda ya kai naira 700 kan kowace lita.
Makamai masu linzami da dama sun afka wa garin Odesa na Ukraine a yau Asabar, kamar yadda kakakin gwamnatin yankin na kudancin ƙasar ya bayyana.
Serhiy Bratchuk bai ba da ƙarin bayani ba kan mutanen da harin ya ritsa da su da kuma irin ɓarnar da ya haifar.
Ya ƙara da cewa tun farko a yau makamai masu linzami huɗu sun afka wasu wurare a birnin.
Hotunan da aka yaɗa a shafukan zumunta sun nuna yadda baƙin hayaƙi ya turnuƙe sararin samaniyar birnin.
Gwamnan Babban Bankin Najeriya na CBN Godwin Emefiele ya ce bai yanke shawarar tsayawa takarar shugabancin Najeriya ba tukunna a babban zaɓen 2023.
Mista Emefiele mai shekara 60 na mayar da martani ne bayan rahotannin da suka karaɗe kafofin yaɗa labarai a ciki da wajen Najeriyar cewa ya sayi fom ɗin takarar ranar Juma'a.
Rahotannin sun ce zai yi takarar ne a ƙarƙashin jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar.
"Ina godiya da sha'awar da wasu ƙungiyoyi ke nunawa gare ni don na fito takarar shugaban ƙasa," in ji shi. "Sai dai idan na yanke hukuncin neman takarar zan yi amfani da kuɗin da na tara daga aikina na banki tsawon shekara 35 don sayen fama-faman."
Ya ƙara da cewa "wannan babban mataki ne da ke buƙatar taimakon Allah: nan da 'yan kwanaki kuma Allah zai yi min jagora," cikin wani saƙon Twitter a ranar Asabar.
Wasu daga cikin waɗanda suka ayyana yin takara a APC sun haɗa da Mataimakin Shugaban Najeriya Yemi Osinbajo da kuma tsohon Gwamnan Legas Bola Tinubu.
Jam'iyyun siyasa a Najeriya na da ƙasa da wata ɗaya su tsayar da 'yan takarar dukkan muƙamai na babban zaɓen da za a yi a watan Fabarairun 2023.
Shirin Ra'ayi Riga na wannan makon ya tafka muhawara ne kan 'yancin 'yan jarida da kuma ƙalubalen aikin a ƙasashen duniya albarkacin Ranar 'Yancin 'Yan Jarida da aka yi a makon nan.
Dakarun Isra'ila sun rusa gidan wani Bafalasdine da ake zargi ya kai wa wani mazauni yankin da Isra'ila ta mamaye a bara.
Wata sanarwa da rundunar sojin Isra'ila ta fitar ta ce an rusa Omar Jaradat a garin Al-Silah Al-Harithiya, yammacin Jenin a arewacin gaɓar Yamma da Kogin Jordan.
Sanarwar ta nuna cewa mazauna yankin sun ta jifar sojojin Isra'ila, yayin da kuma suka mayar da martani.
Rikicin ya yi sanadin raunata wasu Falasdinawa
A watan Maris, jami'an suka tarwatsa gidaje uku na mambobin Jaradat a Silat Al Harthiya.
Isra'ila ta sha rusa gidajen mutanen da take zargi sun kai wa ƴan ƙasarta hari a Gabar Yamma da Kogin Jordan da kuma gabashin Kudus.
Hukumomin lafiya a Ingila sun ce an samu wani mutum da gwaji ya tabbatar da ya kamu da cutar ƙyandar biri da ba a saba gani ba a ƙasar.
Sun ce ya kamu da cutar ne bayan balaguro zuwa Najeriya da ke yammacin Afrika.
A cikin wata sanarwa Hukumar lafiya ta Birtaniya (UKHSA) ta ce ana kula da lafiyar mutumin a hannun ƙwararru a ɓangaren cutuka masu yaɗuwa a asibitin Guy's and St Thomas' NHS Foundation Trust a London.
“Yana da mahimmanci a jaddada cewa cutar kyandar biri ba ta saurin yaɗuwa tsakanin mutane kuma haɗarin yaɗa cutar ba ya da girma, ”in ji babban jami’in asibitin ta UKHSA Colin Brown.
Kyandar biri da ake kira Monkey pox cuta ce mai yaɗuwa da aka kawar da ita a shekarar 1980.
Makiyaya a baya-bayan nan sun zama kurar baya ta fuskar ilimi, sakamakon koma-baya da ilimin makiyaya na Nomadic Education.
Wasu masana dai na alakanta rashin ilimin da daya daga cikin dalilan da ke sa ‘yan ta’adda ke ribatarsu.
Domin dakile hakan ne wasu jihohi a arewacin Najeriya suka fito da wani tsari na ilmantar da ‘ya’yan makiyayan a makarantun gwamnati a lokacin hutu.
Jihar Bauchi ce ta fara bullo da wannan shiri, kuma kwamishinan ilmin jihar, Dr Aliyu Usman Tilde ya shaida wa Usman Minjibir yadda tsarin yake.
Hukumar da ke kula da harkokin sadarwa ta Najeriya ta ce ta samu takarda daga ƙungiyar kamfanonin sadarwa na ƙasar na neman yin ƙarin kuɗin kiran waya da kuma datasakamakon tsadar gudanar da ayyukansu.
Rahotanni a Najeriya sun ce takardar da ƙungiyar ta gabatar na neman yin ƙarin kashi 40 cikin 100 na farashin kiran waya da aika saƙo.
Kamfanonin na son yin ƙarin ne na kira dgaa N6.4 zuwa N8.95, farashin aika saƙo kuma zai koma N5.61 maimakon N4.
Sai dai Hukumar Sadarwa ta Najeriya NCC ta ce za a iya samu
dalilai masu ma'ana don buƙatar tana mai cewa babu ƙarin kuɗin da za a yi ba tare da nazarin farashi ba domin ƙayyade yadda ya dace, kamar yadda kamfanin dillacin labarai na Reuters ya ruwaito.
Hauhawan farashi a Najeriya kusan ya shafi ko wane ɓangare, yayin da masu saye da sayarwa suka fi jin tasirinsa.
Taɓarɓarewar darajar naira ya ƙara haifar da tsadar kayayyakin, musamman a ƙasar da ta dogara da shigo da kayayyakin buƙatu na yau da kullum daga waje.
Japan da Koriya ta Kudu sun ce Koriya ta Arewa ta sake yin gwajin wani makami mai linzami.
Ta yi gwajin ne a ranar Asabar, kamar yadda jami'an Japan da na Koriya ta Kudu suka bayyana.
A bikin sabuwar shekara, gwamnatin Pyongyang ta yi gwaji makamai da dama, na baya bayan nan shi ne wanda ta yi a ranar Asabar.
Tun a ranar Juma'a ma'aikatar harakokin wajen Amurka ta ce Koriya Ta Arewa na shirin gwajin makamin nukiliya.
An rantsar da Emmanuel Macron a hukumance a matsayin shugaban Faransa a wa'adinsa na biyu
An yi bikin ne a fadar Elysee, makwanni biyu bayan ya doke abokiyar hamayyarsa Marine Le Pen mai ra’ayin riƙau.
An rage girman shagalin bikin inda ba a gudanar da faretin soja ba a fadar shugaban Faransa Elysees.
Macron ya yi jawabi inda ya gabatar da manufofinsa kan Faransa.
Ana tunanin nan ba da jimawa ba zai nada sabon Firaminista, wanda zai ƙarfafa jam'iyyarsa kafin zaɓen 'yan majalisar dokoki a wata mai zuwa.
Hukumar EFCC da ke yaƙi da rashawa a Najeriya ta ce tana sa ido kan tushen kuɗaɗen da ake amfani da su wajen sayen fom ɗin takara na jam'iyyun siyasa.
Shugaban Hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa, ne ya bayyana haka a wata hira da kafar talabijin ta Channels ta yi da shi a ranar Juma’a.
Ya ce hukumarsa ta EFCC na haɗa kai tare da hukumar zaɓe mai zaman kanta INEC domin gano inda aka samo kuɗaɗen da ƴan siyasa ke sayen fom.
“Gaskiya kuɗi ne masu yawa, domin za ka iya kwashe tsawon rayuwarka kafin ka tara naira miliyan 40 ko kuma miliyan 100,” in ji shi.
Shugaban na EFCC ya ce hukumar za ta yi ƙoƙarin tabbatar da masu “kashi a gindi” ba su kai ga samun muƙaman shugabanci a Najeriya ba.
Bawa ya ce “EFCC na aiki a ɓoye domin bankaɗo irin waɗannan marasa gaskiya.”
Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya tana sayar da fom na shugaban ƙasa kan farashin naira miliyan 100 yayin da babbar jam’iyyar adawa ta PDP ke sayar da nata kan naira miliyan 41.
Ya zuwa yanzu kusan mutum 20 ne suka saye fom ɗin APC na shugaban ƙasa yayin da aƙalla mutum 17 suka sayi na PDP.
Gwamnatin Taliban a Afganistan ta umurci matan ƙasar su rufe fuskokinsu yayin da suke a bainar jama'a.
Ma'aikatar hana baɗala da inganta kyawawan ɗabi'u ta gwamnatin Taliban ta ce muharrami ko mahaifin mace zai iya fuskantar ɗauri idan har wadda ke ƙarƙashinsa ta kasa rufe fuskarta.
Taliban ta buƙaci mata su sanya hijabin da za ta rufe dukkanin jikinsu.
Matakin ya fusata masu fafutukar kare haƙƙin mata, wadanda suka ce watanni tara bayan ƙwace mulki, Taliban na tauye haƙƙin mata.
Dokar ta kuma ce idan mace ba ta da wani muhimmin abu da za ta yi a waje, zai fi kyau ta zauna a gida.
Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta ce an cimma yarjejeniyar sayar da kungiyar ga wani attajirin ɗan kasuwar Amurka, Todd Boehly, wanda ke cikin wadanda suka mallaki Los Angeles Dodgers.
Mai Chelsea, ƙungiyar da ke London, Roman Abramovich ya saka ta a kasuwa, kafin a sanya masa takunkumi kan alakarsa da Vladimir Putin.
Chelsea ta ce kudin sayenta dala biliyan uku, za a saka su a asusun da aka sanyawa takunkumi, kafin daga bisani a bayar da su don ayyukan agaji.
Cinikin zai faɗa idan aka samu amincewar hukumar kwallon kafa ta Ingila da gwamnatin Birtaniya.
Aƙalla sojoji 11 rahotanni suka ce an kashe a wani harin kwantan bauna guda biyu da aka kai a arewacin Burkina Faso da ke fama da rikici.
Rundunar sojin ta ce an kai harin farko a kusa da garin Solle a ranar Alhamis din da ta gabata wanda ya yi sanadin mutuwar sojoji biyu da wasu farar hula hudu da ke taimaka wa sojoji yayin da wasu dakarun sa-kai guda biyar suka halaka a wani farmakin da aka kai a Ouanobe.
“Ƴan ta’adda” ne suka kai harin a cewar runduna sojin ƙasar.
Mutane 9 ne suka jikkata, in ji sanarwar, an kuma gano gawarwakin maharan kimanin 20 a yayin gudanar da aikin fatattakar mayaƙan
An kuma kama ko lalata makaman yaki da alburusai da kayan sufuri da na sadarwa.
Mayaƙa masu alaƙa da Al Qaeda da IS sun sha kai hare-hare a yankin arewa da gabashin Burkina Faso tun 2015, inda suka kashe sama da mutum 2,000 da raba miliyoya da gidajensu.
Wani malamin addinin musulunci a kasar Kenya ya buƙaci kotu da kada ta sake shi daga gidan yari duk da cewa an wanke shi daga laifukan ta'addanci.
Guyo Gorsa Buru ya ce yana fargabarza a iya sace shi ko kashe shi da zarar an sako shi kamar yadda ake zargin ya faru da wasu da ake zargi da aikata ayyukan ta’addanci.
An kama shi ne a 2018 kuma an tuhume shi da mallakarabubuwan da ke nuna yana da alaƙa da ƴan ta’adda da kuma haɗa kai da mayakan al-Shabab na Somaliya.
Kotun da ke babban birnin ƙasar ta ba shi damar ci gaba da zama a gidan yarin na tsawon kwana 30.
Lauyansa ya roƙi kotun ta ba shi tabbaci na kariya idan har an sake shi.
Sojojin Ukraine sun ce sun ƙwato wasu ƙauyuka biyar a yankin Kharkiv da ke arewa maso gabashin Ukraine, yayin da suke ci gaba da gumurzu da sojojin Rasha da ke ta ruwan bama-bamai a birnin.
Sojojin sun ce za su cimma burinsu na fatattakar Rasha da ke birnin da ya kasance na biyu mafi girma a Ukraine.
Rahotanni na cewa manyan makamai da kasashen yamma ke taimakawa kasar da su, sun soma tasiri a wannan yaki.
A yankin kudanci kuma, Rasha na ci gaba da zafafa hare-hare a yankin Donbas, sai dai har yanzu ba ta yi wani nasara ba, duk da luguden wutar da take yi babu kakautawa.
A Mariupol, an sake kwashe wasu fararan-hula 50 daga yankin Azovstal mai masana'antu a ranar Juma'a, amma 'yan Ukraine na cewa ana karya sharuɗɗan yarjejeniyar tsagaita wuta.
Emmanuel Macron zai sha rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban kasar Faransa a karo na biyu a yau Asabar, bayan nasarar tazarce kan mulki da ya yi a zaben watan da ya gabata.
Sai dai rahotanni na nuna cewa yanayin da ake ciki a yanzu a Faransa ba zai bada damar bukukuwa ba, don haka Bikin da za a gudanar a fadar shugaban ta Elysee, za a takaita wasu shagulgula da aka saba gani a baya-- kamar irinsu faratin sojoji, musamman saboda zarcewa zai yi da mulkin.
Mahalarta taron za su saurari jawabin da zai gabatar wanda ake sa ran Mista Macron din zai zayyana manufofinsa.
Ana sa ran nan ba da jimawa ba zai sanar da sabon Firaminista, domin sake kimtsa jam'iyyarsa da ke mulki kafin zaben 'yan majalisa da ke tafe a wata mai kamawa.