Sai Litinin za a yi Sallah a Saudiyya saboda ba a ga wata ba

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.

Rahoto kai-tsaye

Awwal Ahmad Janyau and Umar Mikail

  1. Mu kwana lafiya

    Nan muka zo ƙarshen rahotanni a wannan shafi.

    Mu haɗu da ku gobe samun wasu sabbin rahotannin kai-tsaye. Kafin lokacin, ku duba ƙasa don karanta labaran da muka wallafa a yau Asabar.

  2. 'Yan sandan Isra'ila sun ce sun harbe matashin Bafalasɗine

    Masallacin Ƙudus

    Asalin hoton, EPA

    Dakarun Isra'ila sun kashe wani Bafalasɗine a wani samame da suka kai yankin gabar yamma da Kogin Jodan.

    Ma'aikatar lafiya ta Falasdinawa ta ce matashin mai shekara 27 da ake kira Yahya Ali Adwan, an harbe shi ne a kauyen Azzun da ke kusa da Qalqiyya.

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce dakarunta sun yi harbi ne bayan da Falasdinawa suka jefa musu bam.

    Sun kuma kutsa domin neman wasu 'yan bindiga biyu da aka ce sun kashe wani Bayahude a ranar Juma'a.

    An kama mutane da dama an kuma kwace makamai masu yawa yayin binciken.

  3. Jamus ta kai Italiya ƙara kotun duniya kan Yaƙin Duniya na II

    Kotun Duniya

    Asalin hoton, Getty Images

    Jamus ta kai ƙarar Italiya gaban babbar kotun kotun Majalisar Ɗinkin Duniya sakamakon yunƙurin wasu 'yan Italiyan na neman a biya diyyar laifukan yaƙi da gwamnatin Jamus ɗin ƙarƙashin Nazi ta aikata.

    Cikin koken da ta shigar gaban International Court of Justice (ICJ), Jamus ta ce Italiya ta ƙyale ƙararraki a kotunan ƙasar duk da wani umarnin kotu a 2012 da ya ce ƙararrakin ba su cancanci a saurare su ba.

    Ta ce tun bayan umarnin, an shigar da sabbin ƙararraki 25 a Italiya.

    Wasu daga cikin shari'o'in sun umarci Jamus ta biya diyya.

    Jamus ta ce ta shigar da ƙarar ce a yanzu saboda wasu ƙararraki biyu da za su iya sakawa a ƙwace wasu kadarorin ƙasar da ke Italiya don biyan diyyar.

  4. Labarai da dumi-dumi, Real Madrid ta lashe gasar La Liga karo na 35

    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta lashe babbar gasar La Liga ta Spaniya karo na 35 a tarihi.

    Real ta cimma wannan tarihi ne bayan doke Espanyol 4-0 a yammacin Asabar a filin wasa na Santiago Bernabéu.

    An sallama wa Real kofin ne duk da cewa saura wasa huɗu a kammala gasar.

    Daga cikin wasannin da suka rage wa Real har da na hamayar birnin Madrid tsakaninta da Atletico. Sauran su ne Levente da Cadiz da Real Betis.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  5. Akwai yiwuwar a yi azumi 30 a Nijar

    Masana ilimin taurari a Nijar - kamar Najeriya da Saudiyya da Faransa - sun ce akwai yiwuwar a yi azumi 30 saboda babu tabbas ko za a ga watan Shawwal a yau Asabar.

    Babban malamin Musulunci Sheikh Bourema Abdou ya ce hatta a garuruwan Zinder da kuma Diffa, inda rana ke riga faɗuwa, babu tabbas ko za a ga watan.

    Tuni Saudiyya ta sanar cewa sai Litinin za ta yi bukukuwan Ƙaramar Sallah, inda za a yi azumi 30.

  6. Musulman Faransa ma sai Litinin za su yi Sallah

    Majalisar Musulman ƙasar Faransa da ke Turai ta sanar cewa bayanaui sun nuna cewa ba za a ga watan Shawwal ba na Hijira ta 1443 a yau Asabar.

    Wata sanarwa da majalisar ta fitar ta ce hakan na nufin za su cika Azumin Ramadana 30 kuma sai ranar Litinin za a yi bikin Ƙaramar Sallah.

    Sanarwa

    Asalin hoton, Musulman de France

  7. Labarai da dumi-dumi, Ba a ga watan Sallah ba a Saudiyya

    Hukumomi a Saudiyya sun ce ba a ga watan Shawwal ba a yau Asabar, abin da ke nufin za a yi Azumin Ramadana 30 a bana.

    Da ma masana ilimin taurari sun yi hasashen cewa ba za a ga jaririn watan ba ranar Asabar saboda wata zai riga rana faɗuwa a yammacin yau.

  8. An fara shirin hangen wata a Saudiyya duk da cewa 'ba lallai a gan shi ba'

    Masu ganin wata a Saudiyya

    Asalin hoton, Haramain Sharifain

    Mahukunta a Saudiyya sun fara shirin hangen jaririn watan Shawwal, wanda zai kawo ƙarshen watan Azumin Ramadana a yau Asabar na shekarar ijira ta 1443.

    Sai dai alamu na nuna cewa da wahala a ga watan, kamar yadda masana ilimin taurari suka yi hasashe.

    "Sararin samaniya fayau yake ta yadda za a iya ganin watan Shawwal amma a kimiyyance, watan zai riga rana faɗuwa, abin da ke nufin zai yi wuya a ga (sabon) watan a yau," in ji Shugaban Masana Ilimin Taurari na Saudiyya Abdullah Khudairi.

    A Najeriya ma masana na da irin wannan hasashen, inda suke tunanin watan Ramadana zai cika kwana 30 kafin a yi bikin Ƙaramar Sallah ranar Litinin - maimakon Lahadi.

    A tsarin kalandar Musulunci, kowane wata kwana 29 ne amma idan ba a ga sabon wata ba sai a cika shi ya zama kwana 30 kafin a shiga sabo washegari.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  9. Ɗan majalisar Birtaniya ya ajiye muƙaminsa saboda kama shi yana kallon batsa a majalisa

    Neil Parish

    Ɗan Majalisar Dokokin Birtaniya, Neil Parish, ya faɗa wa BBC cewa ya sauka daga muƙaminsa bayan ya amsa cewa ya kalli bidiyon batsa sau biyu a cikin majalisar.

    Mista Parish - wanda ke wakiltar mazaɓun Tiverton da Honiton da ke Devon - ya ce "yanayi ne na rashin hankali" kuma "ba na alfahari da abin da na aikata".

    Ya ƙara da cewa karon farko tsautsayi ne bayan ya kalli wasu motocin noma, amma karo na biyun da gangan ya yi.

    A ranar Juma'a ne jam'iyyar Conservative ta dakatar da shi saboda zargin.

    Wasu mata biyu 'yan majalisa sun yi iƙirarin cewa sun gan shi yana kallon batsa a wayarsa lokacin da yake zaune kusa da su.

    "Abin da ya faru shi ne - motocin noma nake kallo, abin dariya. Na shiga wani shafi da ke da irin wannan sunan kuma na ɗan kalla duk da cewa bai kamata ba. Amma laifina - babban laifina - shi ne cewa na sake kallo a wani lokacin daban."

  10. Ko tsamar Saudiyya da Iran za ta kawo ƙarshe?

    Iraq

    Asalin hoton, Getty Images

    Firaministan Iraƙi Mustafa al-Kademi ya yi iƙirarin cewa tsamar da ke tsakanin Saudiyya da Iran na dab da kawo wa ƙarshe.

    Firaministan na Iraƙi da ke maƙwabtaka da ƙasahen biyu ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi aka wallafa a ranar Asabar da kamfanin dillacin labaran AFP ya ruwaito.

    Fiye da shekara ɗaya, Iraƙi ta jagoranci tattauna karo biyar tsakanin Saudiyya da Iran. Hukumomin Iraki sun bayyana kyakkyawan fata a tattaunawar baya bayan nan tsakaninsu a da aka yi a Bagadaza.

    Saudiyya da Iran sun daɗe suna tsama tsakaninsu kuma waɗanda ke goyon bayan ɓangarorin da ke rikici kamar Yemen, inda Iran ke goyon bayan mayaƙan Houthi, yayin da kuma Saudiyya ke marawa gwamnati baya.

    Masu zanga-zanga sun farwa ofishin jekadancin Saudiyya a 2016, bayan ta zartar da hukuncin kisa kan wani malamin Shi'a.

  11. Alassane Ouattara ya kai ziyara Ƙabarin Manzon Allah

    Shugaban Ivory Coast Alassane Ouattara ya kai ziyara Masallacin Manzon Allah da ƙabarinsa a Madina.

    Shafin Haramain Shrifain ya wallafa hotunan shugaban a Masallacin Manzon Allah a ranar Asabar.

    Ya kuma yi Sallah a Rauda a cikin Masallacin Manzon Allah (SAW), wurin Annabi ya ce yana daga cikin dausayin Aljannah.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  12. Abin da ya sa jarirai ke samun matsalar zubar gashi

    Likitoci sun bayyana cewa jarirai suna samun matsalar zubewar gashi kamar yadda ake gani a manya.

    Bayanan sautiShirin Lafiya Zinariya
  13. Tinubu ya sayi fom ɗin naira miliyan 100 na takarar shugaban ƙasa

    Tsohon gwamnan Legas Bola ahmed Tinubu ya shiga sahun waɗanda suka lale naira miliyan 100 suka sayi fom na takarar shugaban ƙasa a jam'iyyarsa ta APC.

    Tsohon sakataren gwamnatin tarayya Babachir Lawal ne ya jagoranci tawagar ƙungiyar yaƙin neman zaɓen Tinubu TSG zuwa karɓo wa Tinubu fom na takarar shugaban ƙasa a jam'iyya mai mulki a Najeriya.

    Kauce wa X, 1
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 1

    Tsohon gwamnan Kogi James Abiodun Faleke ya wallafa hotunan magoya bayan Tinubu inda ya ce tare da shi da Babachir Lawal ne suka jagoranci tawagar magoya bayan Tinubu wajen karɓo wa tsohon gwamnan fom na takatar shugaban ƙasa da kuma na gwamnan Legas Babajide Sanwo-Olu

    Kauce wa X, 2
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 2

  14. Waɗanda ba Musulmi ba sun taya Musulmai azumin Ramadan a Saudiyya

    Saudiyya

    Asalin hoton, Getty Images

    Waɗanda ba Musulmi mazauna Saudiyya sun taya Musulmai yin azumin watan Ramadan da nufin ƙara kusanci da abota tsakaninsu da Musulmai.

    Sun ɗauki azumi tare da kiyaye dokokinsa da kuma shan ruwa tare da abokanansu Musulmi a Saudiyya, kamar yadda jaridar Arab News ta wallafa a shafinta na intanet.

    Ta ambato ɗaya daga cikinsu yana cewa: “Bai kamata ku yi Ramadan ku ƙadai ba - Wannan lokaci ne na ƙarfafa abokantaka da karimci.”

    Wasu daga cikinsu sun ce Azumi ya ƙara masu kusanci da abokansu Musulmi.

    A cewar jaridar, duk da cewa akwai bambancin addini, amma ƴan ƙasashen waje waɗanda ba Musulmi na ƙara rungumar al’adun Saudiyya..

    Baya ga kasancewar Ramadan watan Ibadah da tasirinsa ga ƙara kusantuwa ga Allah, bincike ya nuna yin azumi na kaucewa ci da sha daga fitowar al fijr zuwa faɗuwar rana yana da fa’ida wajen inganta lafiyar ɗan adam.

  15. Ukraine ta zargi Rasha da sace mata kayan abinci

    Shugaba Zelensky

    Asalin hoton, Getty Images

    Mataimakin ministan noma na Ukraine ya zargi Rasha da sace wa Ukraine ton 100,000 na kayan abinci yankunan da dakarunta suka mamaye.

    Taras Vysotskiy ya ce yana fargabar cewa Rasha za su iya wawushe shaguna ton miliyan daya da rabi na amfanin gona.

    Ukraine ta ce kwasar ganimar kayan abinci da kuma toshe hada-hadar jirage a tashoshin ruwanta na iya yin barazana ga samar da abinci a duniya.

    Kakakin Kremlin ya musanta zargin na satar abinci.

    Wannan na zuwa yayin da jirgin farko da ke cike da kayan abinci na Ukraine ya bar tashar ruwan Romania a ranar Juma'a, wanda ya ba Ukraine damar kaucewa takunkumin Rasha.

  16. PDP ta haramtawa ƴan takara biyu yin takarar shugaban ƙasa

    PDP

    Asalin hoton, PDP

    Rahotanni sun ce babbar jam'iyyar hamayya ta PDP a Najeriya ta hana wa biyu daga cikin 'yan takarar shugaban kasa 17 a zaben 2023 yin takara ƙarƙashin jam’iyyar.

    Jaridar Premium Times da ta ruwaito labarin ta ce shugaban kwamitin tantance ƴan takarar David Mark, bai bayyana sunayen waɗanda aka hana wa yin takarar ba da kuma dalilin rashin cancantarsu.

    Daga cikin ƴan takarar da aka tantance a ranar Juma’a a hedikwatar jam’iyyar a Abuja sun ƙunshi tsohon mataimakin shugaban ƙasa Alhaji Atiku Abubakar da tsohon shugaban Majalisar dattawa kuma tsohon gwamnan Kwara Sanata Bukola Saraki da gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal da gwamnan Bauchi Bala Muhammad da Peter Obi da Pius Anyim.

  17. An buɗe wa Firaministan Pakistan ƙofar Ka'aba a Makkah

    An buɗe wa sabon Firaministan Pakistan Shehbaz Sharif kofar Ka'aba a lokacin da yake gudanar da Umrah a Makkah a yau Asabar.

    Shafin Haramain Sharifain ya wallafa hotunan Firaministan a Twitter lokacin da yake Ibadah

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  18. Sarki Salman ya isa Makkah don kammala azumin watan Ramadan

    Sarki Salman

    Asalin hoton, @hsharifain

    Sarki Salman ya isa fadar Al-Safa da ke Makkah daga Jeddah a daren Juma’a domin kammala azumin watan Ramadan, kamar yadda kafofin yaɗa labaran Saudiyya suka ruwaito

    Hotunan da kamfanin dillacin labarai na Saudiyya SPA ya fitar a safiyar ranar Asabar sun nuna sarkin yana addu'a a Masallacin Harami.

    Sarki Salman

    Asalin hoton, @hsharifain

    Sarkin zai kammala watan Ramadan a Makkah tare da yin sallar idi a can.

  19. Rasha ta ce ta kwashe mutum miliyan ɗaya daga Ukraine

    Ministan harkokin wajen Rasha, Sergei Lavrov, ya ce sama da mutane miliyan daya aka kwashe daga Ukraine zuwa Rasha tun daga ranar 24 ga watan Fabarairu -- lokacin da aka kaddamar da yaki.

    Ukraine ta sha zargin Rasha da kawshe mutane tana tsallakar da su iyaka ba da son ran su ba.

    A wata hira da kafar yada labaran China, Mista Lavrov ya ce cikin milyoyin mutane da aka kwashe, dubu 120 baki ne, sai kuma mutanen da aka kwashe daga Donetsk da Luhansk -yankunan da Rasha ke dauka a matsayin wadanda suka ɓalle.

    Ya kuma zargi kungiyar tsaro ta Nato da haifar da cikas a kokarin daidaitawa ko sulhu kan yakin da Ukraine.

    Har yanzu ba a tsaigaita luguden wuta a arewacin Kharkiv ba, jami'ai na cewa an kashe mutum biyar a hare-haren baya-bayan nan.

  20. Maraba

    Muna maku maraba da kasance da mu a wannan shafin da muke kawo maku labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.