Sarkin Musulmi ya bukaci Musulman Najeriya su fara duba watan Sallah

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.

Rahoto kai-tsaye

Sani Aliyu and Badariyya Tijjani Kalarawi

  1. An yankewa mamban IS dan Birtaniya daurin rai da rai

    An yanke wa mamban IS din nan dan asalin Burtaniya Alexanda Kotey hukuncin daurin rai da rai a Amurka.

    Hakan ya biyo bayan kama shi da laifin garkuwa da kuma kisan wadanda ake garkuwar da su a Syria.

    Kotu ta ce Mr Kotey na da hannun a kisan yan jarida da masu aikin jin kai.

    Mahaifiyar daya daga cikin wadanda ake zargin IS din da kashewa wato Peter Kassig ta ce ta ki yadda ta saka kiyayyar Mr Kotey a zuciyarta, don babu abinda hakan zai haifar sai karuwar kiyayya da dacin rai.

  2. Sojin Amirka sun fara bai wa sojin Ukraine horon amfani da manyan makamai

    Amurka ta ce sojojinta sun fara bai wa na Ukraine horo kan yadda za su yi amfani da manyan makaman yaki da ta ba su don tunkarar Rasha a gabashin Ukraine.

    Mai magana da yawun Pentagon John Kirby ya ce za a gudanar da bada horon ne a wajem Ukraine, da sansanin sojin Amurkar da ke Jamus, sai kuma wani wuri na daban a Turai.

    Fada na kara kazanta a yankin Donbas, kusa da biranen Luhansk da Donetsk.

    Hakama ana bata kashi tsakanin dakarun Rasha da na Ukraine a yankin Kharkiv.

  3. Mai Otal din Tahir da ke jihar Kano ya rasu a Labanun

    Tahir Fadhallah ya rasu ya na da shekaru 74 a duniya

    Asalin hoton, TAHIR GUEST PLACE

    Fitaccen mai harkar otal din nan na Kano Tahir Fadlallah ya rasu yana da shekara 74.

    Mamallakin fitaccen otal din Tahir dake unguwar Nasarawa a Kanon ya rasu ne a birin Beirut na kasar Labanon, wadda nan ne tushensa bayan doguwar jinya.

    Jaridar Daily Nigerians ta rawaito cewa marigayin ya ba da wasiyyar cewa duk lokacin da ya rasu a kai gawarshi Kano a yi masa sutura a can, ko da a ina kuwa ya rasu.

    Tun ranar 23 ga watan Aprilun 2020 ne aka garzaya da Tahir zuwa kasar Labanon, bayan kamuwa da cutar korona, kuma iyalensa sun shaida wa jaridar cewa tun daga nan ne kuma ya dinga fama da rashin lafiya

    Marigayin ya mutu ya bar mata daya da ‘ya’ya biyar.

  4. Bincike; Zuma zai iya komai kan iyalan Gupta a Afirka ta Kudu

    Dan Jacob Zuma Duduzane (dama) ya dade ya na aiki da kamfanin Gupta

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani bincike da aka gudanar, ya bayyana cewa tsohon shugaban Afirka ta Kudu, Jocb Zuma zai iya yin komai domin ya farantawa iyalan Gupta, wani attajiri dan asalin Indiya, haihuwar Afirka a lokacin wa'adin mulkinsa na farko, kamar yadda kwamitin binciken danbarwar cin hanci da rashawa ya bayyana.

    Kwamishinan kwamitin zargin cin hanci da rashawa da ya mamaye gwamnatin Zuma da aka yi wa lakabi da ''State Capture'' a turance, ya ce shugaban ya bada damar an aikata dambarwar rasha iri-iri, kuma iyalan Gupta sun fo kowa samun wannan tagomashin.

    Haka kuma Iyalan Gupta, sun lura cewa Zuma irin mutanen nan ne da za a iya amfani da su, domin sauya tunanin 'yan Afirka ta Kudu, su kuma su bunkasa na su kasuwancin.

    An bayyana wannan batu ne lokacin karkare binciken da aka kammala, da kuma mika rahoton a ranar Juma'a.

    Har kullum iyalan Gupta da Mista Zuma sun sha musanta aikata ba daidai ba, inda Zuma ke cewa bi ta da kullin siyasa ne.

  5. An kama mutum biyar da zargin cin zarafin mata a Masallacin Annabi na Madina

    Masallacin Annabi

    Asalin hoton, Getty Images

    'Yan sanda a garin Madina na Saudiyya sun kama mutum biyar sakamakon cin zarafin wata mace da abokan tafiyarta 'yan ƙasar Pakistan a farfajiyar Masallacin Annabi Muhammadu S.A.W. na Madina.

    Mai magana da yawun 'yan sandan Madina ya ce an miƙa mutanen 'yan asalin Pakistan ga hukumomin da suka dace don ɗaukar matakin da ya dace.

    Ya ƙara da cewa ayyukansu sun saɓa wa alfarmar wurin da kuma jefa masu ziyara cikin barazana.

    Ana zargin mutanen ne da cin zarafin matar ta hanyar zagin ta.

    Sabon Shugaban Pakistan Shehbaz Sharif na ziyara a Saudiyya yanzu haka, inda shi da muƙarabbansa suka gudanar da sallah a masallacin na Madina.

  6. Ana nuna damuwa kan ƙaruwar hukuncin kisa a Iran

    'Yan Iran mazauna Landan sun yi ta zanga-zanga kan hukuncin kisa da ake yankewa a kasarsu

    Asalin hoton, ANADOLU AGENCY

    Wani sabon rahoto da aka fitar ya nuna damuwa kan karuwar zartar da hukuncin kisa da kashi 25 cikin 100 a shekarar da ta gabata a Iran, jim kadan bayan zabar sabon shugaba mai tsaurin addini Ebrahim Raisi.

    Aan zartar da hukuncin kisa kan aƙalla mutum 333, kamar yadda rahoton hadin gwiwa da kungiyar Human Rights mai mazauni a kasar Norway da ta Faransa mai suna France's Together Against the Death Penalty suka fitar.

    Adadin wadanda aka zartarwa hukuncin kisa kan alaka da laifin safarar muggan kwayoyi ya kai 126, inda ya rubanya sau 5 idan aka kwatanta da shekarar 2020.

    Dukkan adadin an same su bayan hukumomi Iran sun sanar da haka, ya yin da kungiyoyin kare hakkin dana dam suka samu tabbaci daga kasar.

    Ko a watan Oktoba, masu rajin kare hakkin dan adm na Majalisar Dinkin Duniya sun yi gargadin dukkan hukuncin kisan da ake yankewa a Iran sun take hakkin dan adam.

    Sun yi kira ga gwamnatin kasar ta kawo kasrshen zartarwa da aiwatar da hukuncin kisan, wanda ya sabawa dokokin kasa da kasa.

  7. An kai hari masallaci a Afghanistan

    Tsohon hari a Afghanistan

    Asalin hoton, AFP

    An ji karar abin fashewa mai karfin gaske a wani masallaci da ke yammacin birnin Kabur na Afhanistan a lokacin da ake yin sallar juma'a.

    Jami'an Afghanistan sun ce akalla mutane 10 ne suka mutu a wannan hari, wasu da dama kuma suka ji mummunan rauni.

    Mai magana da yawun ma'aikatar cikin gida Besmullah Habib, ya ce an kai harin ne masallacin Khalifa Shib da ke Kabul.

    Tun farkon azumin watan Ramadan ake zafafa kai hare-hare a wuraren ibada da taruwar jama'a a Afghanistan.

    Kawo yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai wannan hari na ranar Juma'a.

  8. Sarkin Musulmi ya bukaci Musulman Najeriya su fara duba sabon watan Shawwal

    Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III

    Asalin hoton, Sultan Sa’ad Abubakar III / WIKIPEDIA

    Bayanan hoto, Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III

    Yayin da shekarar 1443 Hijira ke kawo karshe, Fadar Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ta fitar da wata sanarwar da ke kira ga Musulman Najeriya su fara neman sabon watan Shawwal daga ranar Asabar.

    Sanarwar wadda Arc. Zubairu Haruna Usman-Ugwu - wanda shi ne shugaban gudanarwa na hukumar NSCIA - ya sanya wa hannu, ta ce "Kwamitin Ganin Wata na Kasa (NMSC), Sarkin Musulmi ya umarci al'ummah Musulmi a Najeriya su fara duba sabon watan Shawwal daga Asabar 30 ga watan Afrilu 2022, wanda yyayi daidai da 29 ga watan Ramadan, 1443 AH.

    Sanarwar ta ci gaba da cewa: "Idan Musulmai masu daraja suka ga jinjirin watan, sai Mai Alfarma Sarkin Musulmi zai sanar da ranar Lahadi 1 ga watan Mayun 2022 a matsayin ranar 1 ga watan Shawwal kuma ranar Idul Fitr ke nan. Amma, idan ba a ga jinjirin watan ba a wannan ranar, ranar Litinin 2 ga watan Mayun 2022 ta zama ranar Idul Fitr ke nan.

    A karshe sanarwar ta ce ana iya tuntubar dukkan jagororin al'umma a dukkan sassan kasa, da mambobin Kwamitin Ganin Wata na Kasa (NMSC), domin a sanar da su sahihan wuraren da aka ga watan Shawwal 1443 AH.

  9. An bai wa kocin Man United Rangnick aikin horar da tawagar Austria

    Tuni Manchester United ta sanar da cewa kocin Ajax Erik ten Hag ne zai maye gurbin Ralf Rangnick a ƙarshen kakar bana

    Asalin hoton, Getty Images

    An bayyana kocin riƙon ƙwarya na Manchester United Ralf Rangnick a matsayin kocin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Austria.

    Duk da haka Rangnick zai karɓi muƙaminsa na mai ba da shawara a ƙarshen kakar nan a Man United kamar yadda aka tsara.

    "Na zaƙu na ba da gudummawata wajen dawo da kimar United," a cewarsa.

    Ɗan ƙasar Jamus ɗin mai shekara 63 ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara biyu da Austria kuma zai fara aikin ne bayan kammala gasar Premier League a watan Mayu mai zuwa.

    Karanta cikakken labarin a nan.

  10. Musulmai fiye da 500,000 ne suka yi sallar Juma'ar karshen watan Ramadan a Masallacin Annabi

    Fiye da masallata rabin miliyan ne suka halarci sallar Jumu'ah a masallacin Annabi da ke birnin Madina.

    Haramain Sharifain

    Asalin hoton, Haramain Sharifain

    Haramain Sharifain

    Asalin hoton, Haramain Sharifain

    Haramain Sharifain

    Asalin hoton, Haramain Sharifain

    Haramain Sharifain

    Asalin hoton, Haramain Sharifain

  11. Sojoji sun ceto mutum 669 da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su

    Kidnapped victim

    Asalin hoton, Getty Images

    Akalla mutum 669 aka ceto daga hannun wadanda ke garkuwa da su cikin mako uku da ya gabata, kamar yadda jaridar The Nation ta wallafa.

    Shakwatar tsaro ta sojojin Najeriya (DHQ) ta ce an kashe mayaka da 'yan bindiga 23, kuma an kama 19 sannan mayaka 1,158 tare da iyalansu sun mika kawunansu ga dakarun Najeriya.

    Babban jami'i mai kula da harkokin yada labarai na rundunar sojojin Najeriya, Manjo-Janar Bernard Onyeuko, ya ce "dakarun kasar sun kuma kama wani Abdurrazaq Hudu wanda ya ce yana sayar wa kungiyar ISWAP kayayyakin yaki ne, inda aka kama shi a Mutum Biyu da ke karamar hkumar Gassol ta jihar Taraba.

    Manjo-Janar Onyeuko ya ce cikin mutum 1,158 din, akwai maza 164 da mata 367 da kuma yara 627.

  12. An kama mutum 116 kan tuhumar satar mutane a jihohin Nasarawa da Ogun

    Arrested suspected kidnappers and cultists in Nasarawa state.

    Asalin hoton, Other

    Rundunar 'yan sandan Najeriya a jihar Nasarawa ta sanar da kama mutum 50 wadanda ta ke tuhuma da satar mutane a jihar.

    Cikin wani rahoto da jaridar The Nation ta wallafa, ta ce Kwamishinan 'yan sanda a jihar Adesina Soyemi, wanda ya nuna wa jama'a mutanen da ake tuhumar a Lafia babban birnin jihar, ya ce an kama su ne a wurare daban-daban cikin jihar.

    Ya kara da cewa an kama wasunsu ne saboda aa tuhumarsu da kashe shanu 29 ta hanyar basu guba, wasunsu kuma an kama su ne kan tuhumar gama baki da wasu domin su aikata miyagun laifuka, da zama mambobin kungiyoyin asiri da kuma aikata kisan kai.

    Kwamishinan 'yan sandan ya kuma ce jami'ansa sun kama wasu mutum 11 da ake tuhumar suna aikata fashi da makami.

    A jihar Ogun da ke kudu maso yammacin kasar, 'yan sanda sun nuna wa jama'a wasu mutum 52 da ake tuhuma da zama mambobin kungiyoyin asiri da tayar da hankulan al'ummar jihar.

  13. Ana iya shafe shekaru ba a kawo karshen yakin Ukraine ba - NATO

    Mircea Geoana

    Asalin hoton, NATO

    Bayanan hoto, Mataimakin sakatare-janar na Nato Mircea Geoana

    Mataimakin sakatare-janar na kungiyar tsaro ta Nato Mircea Geoana ya shaida wa BBC cewa ana iya shafe shekaru ba a ga karshen yakin Ukraine ba.

    Yayin wata hira da yayi da BBC, Mista Geoană ya ce: "A bayyane yake cewa cikin kwanaki da makonni masu zuwa, ana iya sauya alkiblar yakin - sai dai yana iya wuce wannan hasashen nawa."

    Ya ce yakin na iya kai wa makonni ko watanni, ko ma shekaru ba a kawo karshensa ba.

    Ya kuma yi fatan Ukraine ce za ta yi nasara a karshe.

    Jiya Alhamis Rasha ta harba wasu makamai masu linzami kan birnin Kyiv, yayin da sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya ke ziyara a babban birnin.

  14. Rasha ta kama ma'aikatan agaji 'yan Birtaniya biyu a Ukraine

    The city of Zaporizhzhia took in many people fleeing besieged Mariupol, but was also shelled itself

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata kungiyar agaji ta ce Rasha ta kama wasu ma'aikatan agaji biyu 'yan Birtaniya.

    Kungiyar agajin mai suna Presidium Network ta ce an tsare mutanen ne a wani shingen da Rasha ta kafa kusa da birnin Zaporizhzhia a kudancin Ukraine tun ranar Litinin.

    Daya daga cikin jagororin kungiyar ta Presidium Dominic Byrne, ya ce ma'aikatan na kokarin ceto wasu 'yan gida daya ne da yakin ya rutsa da su.

    "Sun sami wuce wani wurin bincike da sojojin Ukraine suka kafa a hanyar su ta zuwa kudancin yankin sai dai zuwa ranar Litinin ba mu kara ji daga garesu ba," kamar yadda ya sanar da wani shirin talabijin na BBC Nreakfast.

    Ya ce mutanen da ke jiran su ceto su sun rika samun sakonnin tes daga wayar 'yan Birtaniyan biyu, kuma bayan sa'o'i biyu sai sojojin Rasha suka kutsa cikin gidan, sun tambayarsu alakarsu da ma'aikatan agajin, wadanda a hganinsu 'yan leken asiri ne.

    Ma'aikatar harkokin wajen Birtaniya ta ce tana kokarin sanin halin da suke ciki.

  15. Dubban 'yan Kenya sun hallara domin binne tsohon Shugaba Mwai Kibaki

    Kibaki funeral service under way

    An fara gudanar da shirye-shiryen binne tsohon shugaban Kenya Mwai Kibai a Nairobi babban birnin kasar.

    Shugaban ya mutu ranar Alhamis da ta gabata yana mai shekara 90 da haihuwa.

    Shugabannin kasashen dniya ciki har da na wasu kasashen Afirka da dumbin 'yan Kenya tuni suka hallara a babban filin wasa na kasar, Nyayo National Stadium wanda ke cikin birnin.

    Gabanin wannan lokacin, wani ayarin motocin sojojin kasar sun dauko gawar marigayi daga wani gidan da ake ajiye gawa zuwa fadar shugaban kasar.

    The soldiers have been marching in a procession to the venue of the service from State House.

    Asalin hoton, State House Kenya

    Sojojin na gudanar da wani fareti zuwa babban filin wasa na kasar, wurin da za a kammala shirin binne marigayi Mwai Kibaki

    State House Kenya

    Asalin hoton, State House

    'Yan Kenya na kwarara zuwa wurin da za a gudanar da wannan shiri na binne tsohon shugaban kasar, inda kimanin kashi 40 cikin 100 na filin ya cika da misali karfe 9 na safiyar Juma'a, kamar yadda wakilin BBC da ke wurin ya sanar.

    State House Kenya
  16. Rwanda: An daure limamin masallaci saboda ya kashe alade

    It is estimated that 10% of Rwanda's population is Muslim

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, Kimanin kashi 10 cikin 100 na 'yan Rwanda Musulmi ne

    Wata kotu a Rwanda ta daure wani malamin addinin Islama har na tsawon shekara biyar a kurkuku saboda ya kashe wani alade a harabar wani masallaci.

    Wasu shaidu uku sun shaida wa kotun cea sun ga limamin mai suna Sadate Musengimana yana dukan aladen da wani katako matakin da ya kashe shi nan take.

    Sai dai lauyansa ya shaida wa kotun cewa ba da gangar ya kashe aladen ba, yana cewa ya yi kokarin koran shi daga harabar wani masallaci da ke gundumar Kayonzo a gabashin kasar ne cikin watan Fabrairu.

    "Da yaji yara na cewa wani alade ya shiga masallacin, sai ya fito da wata sanda domin ya kore shi. Ya daki aladen kuma ya mutu, amma bai yi niyyar kashe shi ba," kamar yadda lauyansa Yusuf Nsengiyumva ya shaida wa BBC.

    Lauyan ya ce ya daukaka kara kan wannan hukuncin "mai tsanani".

    Tun watan Fabrairu ake tsare da Liman Musengimana, watan da ya kashe aladen.

  17. Sojojin Najeriya sun halaka wasu shugabannin ISWAP/Boko Haram a Borno

    NIGERIAN ARMY

    Asalin hoton, NIGERIAN ARMY / TWITTER

    Rundunar sojojin Najeriya ta ce sojojinta da ke yaki da kungiyoyin Boko Haram/ ISWAP sun kashe mayakan kungiyoyin da dama, ciki har da shugaban addini na Galta, a wani samame da ta kai musu.

    Sanarwar da rundunar ta wallafa a shafinta na Tuwita ta ce samamen ya auku ne a yankin Manjo Ali Qere da ke jihar Borno a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

    Sanarwar ta kuma ce harin ya auku ne ranar Alhamis 28 ga watan Afrilun 2022, kuma ta ce an kama makamai da harsasai.

    NIGERIAN ARMY

    Asalin hoton, NIGERIAN ARMY / TWITTER

    NIGERIAN ARMY

    Asalin hoton, NIGERIAN ARMY / TWITTER

  18. An sake yin arangama tsakanin Falasdinawa da 'yan sandan Isra'ila

    A baya an sha yin irin wannan arangama tsakanin bangarorin biyu

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, A baya an sha yin irin wannan arangama tsakanin bangarorin biyu

    Akalla Falasdianwa 12 ne suka jikkata a masallacin Kudus a wani sabon rikici da 'yan sandan Isra'ila da sanyin safiyar wannan Juma'ar.

    Jami'an tsaro sun rinka jefa hayaki mai sa kwalla da harba harsasan roba domin tarwatsa masu zanga-zanga.

    A cewarsu sun dauki wannan mataki ne ganin yadda Falasdinawa ke ta jifa da duwatsu da abubuwan wuta - akasari a bangon da Yahudawa ke gudanar da addu'o'insu.

    Kuma a wannan lokacin ma 'yan sandan Isra'ila sun ce sun shirya tunkarar dubban Falasdinawa da ake sa ran za su je sallah Juma'a yau a Masallacin.

  19. Zan hana masu magudin zabe sakat a 2023 - Buhari

    Buhari

    Asalin hoton, Instagram/Buhari Sallau

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gargadi masu shirin yin magudin zabe a 2023 da su guji yin hakan, yana mai shan alwashin hana su sakat.

    Ya bayyana haka ne a ranar Alhamis da daddare yayin da ya shirya buda-baki ga jakadun kasashen waje da ke aiki a Najeriya.

    Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Femi Adesina ya fitar, ta ambato Shugaba Buhari yana cewa "ya kamata wadanda suke shirin yin magudin zabe a zabuka masu zuwa su sake tunani saboda na sha alwashin kare martabar al'ummar Najeriya a yayin da suke kada kuri'unsu."

    Kazalika Shugaba Buhari ya gargadi kasashen waje da su guji yin katsalandan a zabukan kasar da ke tafe.

  20. Barka da Juma'a

    Barkanmu da wayewar garin wannan rana ta Juma'a, Haji babbar rana!

    A yau ma BBC Hausa za ta ci gaba da ayyukan sanar da ku da ilmantar da ku abubuwan da ke wakana a sassan duniya.

    Sani Aliyu ne yake tare da ku a wannan rana, kuma ni ne zan jagoranci gabatar muku labarai da rahotannin da suka shafi rayuwarku.

    Sai ku ci gaba da kasancewa da BBC Hausa.