Daukacin mayakan Tigray sun fice baki daya daga yankin Afar na kasar Habasha, kamar yadda kakakin kungiyar TPLF Getachew Reda ya wallafa a shafinsa na Tiwita.
“Sako ga al'ummar kasashen waje, da 'yan kasarmu da suka damu da halin da muke ciki, don haka mu na shaida muku cewa babu mayakin Tigray ko daya a yankin Afar, sun fice baki daya,” in ji sakon da ya wallafa..
Mr Getachew, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters ranar Litinin, cewa ya na fatan wannan matakin zai sanya a kai kayan agaji musamman na abinci ga wadanda ke tsananin bukatar taimako a yankin da ke fama da matsanancin fari.
Tun bayan barkewar yaki tsakanin gwamnatin Habasha da 'yan tawayen Tigray, kasar ke cikin tsaka mai wuya.
Ya yin da yarjejeniyar dakatar da bude wutar da aka cimma a watan jiya, ta bada damar kai manyan motocin kayan abinci 144 kacal zuwa yankin, kamar yadda shirin samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana. Yayin da Majalisar Dinkin Duniya ke cewa akalla motocin abinci 100 ya kamata a dinga kai wa yankin a kowacce rana.
A ranar Litinin, ayarin motocin kayan abinci 70, karkashin sa idon MDD suka shiga Tigray. Shugaban shirin wanzar da zaman lafiya na gwamnati a yankin Afar, Ibrahim Hamed Mohammed ya shaidawa BBC cewa mayakan Tigray sun janye daga yawancin wurare, amma har yanzu akwai da dama daga cikinsu da ba su fice ba.
"Ba dukansu ne suka janye ba. Har yanzu akwai sojojin Tigray a gundumar Araju, da Hida da kuma Magal. Su na nan kusa da iyakokinmu, tafiyar ba ta wuce ta kilo mita 15 ba,'' in ji shi.