Babu wanda ya faɗa min dalilin da ya sa aka kama ni - Muhuyi Magaji
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.
Rahoto kai-tsaye
Sani Aliyu and Badariyya Tijjani Kalarawi
Rufewa
A nan muka kawo karshen shafinmu na kai tsaye, sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, inda za mu kawo muku wasu labarai da rahotannin daga sassa daban-daban na duniya.
Badariyya Tijjani Kalarawi ke muku fatan alkhairi daga nan sashen Hausa na BBC.
'Yan sandan Najeriya sun kama mutum bakwai da bindiga 57 ƙirar AK-47
Asalin hoton, NG Police
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce ta kama mutum bakwai da take zargi da safarar makamai a jihohin Taraba da Filato na tsakiyar ƙasar.
Wata sanarwa da rundunar ta fitar a yammacin yau Alhamis ta ce ta kama su ne a wani samame da rundunar musamman ta haɗin gwiwa tsakanin FIB da IRT ta kai.
Ta ce ta ƙwace bindigar AK-47 guda 57 daga hannun waɗanda ake zargin. Yayin bincike, wasu daga cikinsu sun faɗa wa 'yan sanda cewa sun sayi bindigar AK-47 da kuma ƙirar SMG kan kuɗi naira 900,000.
Rundunar ta bayyana sunayensu kamar haka: Hamza Zakari mai shekara 20, Abubakar Muhammed shekara 22, Umar Ibrahim shekara 25, da kuma Muhammed Abdulkarim wanda aka fi sani da Dan-Asabe mai shekara 37.
Sauran su ne: Bello Sani, da Venab Puncat, da Yusuf Nahoda.
'Yan sanda sun ce suna ci gaba da bincike kan mutanen kafin gurfanar da su a gaban kotu.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
'Yan kasuwa a Sudan ta Kudu sun bukaci dala miliyan 100 na ciyar da sojoji
Asalin hoton, AFP
Kungiyar 'yan kasuwa su 200 a Sudan ta Kudu, sun kiyasta kashe dala miliyan 100, na abincin da suka dinga kai wa sansanonin horas da sojoji da ke yankin cikin shekaru biyu.
Kwamitin gwamnatin riko ne suka bai wa masu kai kayan abincin kwantiragin kai wa, a lokacin da ake aikitin tabbatar da zaman lafiya tsakanin bangarorin da suke gaba da juna, da kuma suka shiga yakin basasar da aka yi.
'Yan kasuar su na kuma kaiwa sojojin kayan da ba na abinci ba da suka da gada tanti, da zanin gado, da katifu, da barguna. Amma yawanci tun shekarar 2019 ba a biya su hakkinsu ba.
A farkon wannan watan, gwamnati ta yi alkawarin biyansu kudaden a ranar Laraba, amma shiru ba a biya ba.
Mai magana da yawun 'yan kasuwar, Kasha Majok Kuol, ya shaidawa BBC cewa yawancin wakilansu sun tafi ofishin shugaban kwamitin a ranar Alhamis.
“Mun yi mamaki matuka da muka gano jami'an tsaron da aka girke anan saboda zuwanmu.
“Abinda ya faru a yau ya yi matukar daure mana kai da ban mamaki, ganin sojoji da 'yan sanda da suka hana mu shiga ofishin.”
An jiyo ƙarar fashewar abubuwa a birnin Kyiv
An jiyo ƙarar fashewar wasu abubuwa a babban birnin Ukraine Kyiv, a cewar rahoton kamfanin labarai na Reuters.
Rahoton ya ce waɗanda abin ya faru a kan idonsu sun tabbatar da faruwarsa amma babu wani ƙarin bayani game da abin da ya haddasa su.
BBC ba ta iya tabbatar da faruwar lamarin ba zuwa yanzu.
Tsirarun maza 'yan siyasa suna da dabi'ar dabbobi, inji Suella Braverman
Ministar shari'a a Birtaniya Suella Braverman ta ce tsirarun maza 'yan siyasa su na da dabi'ar dabbobi, bayan wasu daga cikin mata 'yan majalisa sun bada bayani kan nuna wariya da tsangwama da cin zarafi.
Da ta ke magana a shirin BBC Womens Hour, Mis Braverman ta ce matsalar ta samo asali ne tun daga al'umma ana kuma bukatar tattaunawa kan batun domin magancewa.
Kalamanta na zuwa ne bayan wata minista da ba a ambaci sunanta ba, ta zargi wani dan majalisar conservative ya na kallon fim din badala a zauren majalisar.
Mis Braverman ta ce abin takaici ne da bakin ci ganin dan mjalisar na sanye da bajon jam'iyyar Conservative.
Tsohuwar minista Baroness Nicky Morgan, ta bayyana ikirarin da abin mamaki, ta kuma ce idan da wannan ta faru a wani wurin aikin na daban, da tuni an kori wanda ya aikata laifin daga bakin aiki. Ta ce amma lamarin ga 'yan majalisa na daban ne, bbau mai daukar mataki akan su ko ma ace an kore.
Guterres ya gana da shugaba Putin don kawo karshen yakin Ukraine
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira ga Rasha da ta bada hadin kai ga kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, a binciken da za ta gudanar kan zargin aikata laifukan yaki a Ukraine.
Mista Guterres na jawabi ne a Bucha, inda ake zargin dakarun Rasha da kisan daruruwan fararen hula.
Ya ce ya na goyon bayan kotun hukunta manyan laifuka ta duniya kan wannan batu, kuma ya na kira ga Rasha da ta baiwa kotun hadin kai.
Ya kuma ziyarci garuruwa da dama a arewa maso yammacin Kyiv, inda Rasha ta yi luguden wuta.
Dama shugaban na MDD, ya isa Kyiv domin ganawa da shugaba Volodomyr Zalensky, kwanaki biyu bayan ganawa da shugaba Putin.
Indonesia ta haramta fitar da man ja daga ƙasar
Asalin hoton, Getty Images
Indonesia za ta daina fitar da danye da ma man jan da aka sarrafa zuwa kasashen waje, saboda fuskantar karancin man a cikin gida.
Shugaba Joko Widodo ya ce dokar ta fara aiki yau Alhamis, kuma sun kakaba ta ne bayan boren da al’umma suka yi saboda yankewar manjan a tukwanensu.
Wakiliyar BBC ta ce matakin hana fitar da danyen man jan da ma sarrafaffe zai haifar da karancinsa a fadin duniya, a daidai lokacin da aka fara fuskantar karancin man girki saboda rikici a Ukraine.
Da ma Indonesia ce ke kan gaba a duniya wurin fitar da man ja, kuma shi ne man da aka fi dafa abinci da shi.
Kazalika ana amfani da shi wurin yin man wankin kai da kuma alawa.
An kashe ɗan Birtaniya a Ukraine, wani ya ɓace
An kashe wani ɗan Birtaniya a Ukraine sannan wani ɗan ƙasar ya ɓace, a cewar Ofishin Harkokin wajen Birtaniya.
Ofishin harkokin wajen bai faɗi ko suna yaƙi ne a Ukraine ɗin ba ko kuma a'a.
Mai magana da yawun ofishin ya ce: "Muna ba da tabbacin cewa an kashe wani ɗan Birtaniya a Ukraine kuma ana ba wa danginsa taimako."
Game da wanda ya ɓata, suka ce: "Muna sane da wani ɗan Birtaniya da ya ɓace a Ukraine kuma muna taimaka wa danginsa. Muna ci gaba da neman bayanai da gaggawa."
Babu wanda ya faɗa min dalilin da ya sa aka kama ni - Muhuyi Magaji
Asalin hoton, Uthman Bala Rimingado
Tsohon shugaban hukumar yaƙi da cin hanci ta Jihar Kano, Muhuyi Magaji Rimingado, ya tabbatar wa BBC Hausa kama shi da 'yan sanda suka yi amma ya ce ba a faɗa masa laifin da ake tuhumarsa da shi ba.
'Yan sanda sun kama tshohon shugaban ne wanda ke neman tsayawa takarar gwamnan Kano a babban zaɓe na 2023 a Abuja yayin da ya je aikin tantancewa da jam'iyyar PDP ta shirya.
"Babu wanda ya faɗa min dalilin da ya sa aka kama ni, ba a faɗi wani laifi ba a takardar izinin kama ni," in ji Muhuyi cikin wani saƙo da ya aike wa BBC.
Wata takarda da aka gabatar wa Muhuyi ta nuna yadda wata kotun majistare a Kano ta ba da umarnin kama shi.
Asalin hoton, Muhuyi Magaji
Yanzu haka yana tsare a ofishin 'yan sanda na Abuja, babban birnin Najeriya.
Gwamnatin Kano ƙarƙshin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta dakatar da Muhuyi ne daga muƙaminsa bayan zargin sa da badaƙala a wasu kwangiloli da kuma aringizo tare da ƙaddamar da bincike kan sa a watan Yulin 2021.
Jami’an ‘yan sanda sun kama Muhuyi Rimingado bayan PDP ta tantance shi a Abuja
Asalin hoton, Other
Bayanan hoto, Muhuyi Rimingado.
Rahoton da muke samu na cewa jami’an ‘yan sanda sun kama tsohon shugaban Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin-hanci da rashawa ta Jihar Kano, PCACC, Muhuyi Rimingado.
Jaridar Daily Nigerian Hausa ta ce an kama Rimingado ne a masaukin Gwamnan Sokoto da ke Abuja, wurin da ya je domin a tantance shi a matsayin ɗan takarar gwamnan Kano a karkashin jam’iyyar PDP.
An jiyo cewa ƴan sandan sun tafi da Rimingado nan da nan bayan an tantance shi, inda su ka wuce da shi ofishin shelkwatar ƴan sanda ta Abuja.
Majiyoyi na tsaro sun ce za a wuce da shi Kano domin a gurfanar da shi a gaban kotu.
A tuna cewa an dakatar da Rimingado ne a watan Yulin shekarar da ta gabata bayan buɗe bincike kan badaƙalar kuɗi da kuma aringizon kuɗaɗen kwangiloli da a ke zargin an baiwa wasu kamfanoni masu alaka da dangin gwamna.
Matan da ake lalata da su kafin a ba su ruwa a Kenya
Bayanan bidiyo, Matan da ake lalata da su kafin a ba su ruwa a Kenya
Danna hoton da ke sama domin kallon bidiyon:
Nairobi, babban birnin kasar Kenya yana fama da matsalar karancin ruwa saboda wasu dalilai da suka hada da tsoffin fayif-fayif da sauyin yanayi.
Mazauna yankunan marasa galihu irin su Kibra suna samun ruwa daga 'yan ga-ruwa.
Masu sayar da ruwa suna yin tasiri sosai kan yadda ake samun ruwan a irin wadannan wurare.
Mutane suna biyan kudin ruwa da na tsaftar muhalli, sai dai hakan yana sa wa ana lalata da mata.
Tuwita ya tabbatar cewa ya kammala yin rajista a Najeriya
Asalin hoton, Getty Images
Kamfanin sada zumunta na Tuwita ya sanar cewa ya yi rajista a matsayin kamfani karkashin dokokin Najeriya, cikin watanni bayan da kamfanin ya amince da sharuddan da gwamnatin kasar ta gindaya kafin ta kyale shi ya ci gaba da aiki a cikin kasar.
Najeriya ta dakatar da kamfanin a watan Yunin bara ne bayan da ya goge wani sako da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya wallafa.
Tuwita ya kare kansa, yana cewa sakon ya taka tsarin aikinsa, sai dai gwamnatin Najeriya ba ta gamsu da matakin ba.
Sai bayan wata bakwai Najeriya ta dage hanin wato a watan Janairun bana, shi ma sai da Tuwita ya amince da wsu sharudda, cki har da yin rajista a kasar kafin karshen watan Maris.
Wani wakilin kamfanin ya tabbatar wa BBC cewa kamfanin ya cika wadannan bukatun.
Mayakan Tigray sun fice daga yankin Afar - TPLF
Asalin hoton, Getty Images
Daukacin mayakan Tigray sun fice baki daya daga yankin Afar na kasar Habasha, kamar yadda kakakin kungiyar TPLF Getachew Reda ya wallafa a shafinsa na Tiwita.
“Sako ga al'ummar kasashen waje, da 'yan kasarmu da suka damu da halin da muke ciki, don haka mu na shaida muku cewa babu mayakin Tigray ko daya a yankin Afar, sun fice baki daya,” in ji sakon da ya wallafa..
Mr Getachew, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters ranar Litinin, cewa ya na fatan wannan matakin zai sanya a kai kayan agaji musamman na abinci ga wadanda ke tsananin bukatar taimako a yankin da ke fama da matsanancin fari.
Tun bayan barkewar yaki tsakanin gwamnatin Habasha da 'yan tawayen Tigray, kasar ke cikin tsaka mai wuya.
Ya yin da yarjejeniyar dakatar da bude wutar da aka cimma a watan jiya, ta bada damar kai manyan motocin kayan abinci 144 kacal zuwa yankin, kamar yadda shirin samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana. Yayin da Majalisar Dinkin Duniya ke cewa akalla motocin abinci 100 ya kamata a dinga kai wa yankin a kowacce rana.
A ranar Litinin, ayarin motocin kayan abinci 70, karkashin sa idon MDD suka shiga Tigray. Shugaban shirin wanzar da zaman lafiya na gwamnati a yankin Afar, Ibrahim Hamed Mohammed ya shaidawa BBC cewa mayakan Tigray sun janye daga yawancin wurare, amma har yanzu akwai da dama daga cikinsu da ba su fice ba.
"Ba dukansu ne suka janye ba. Har yanzu akwai sojojin Tigray a gundumar Araju, da Hida da kuma Magal. Su na nan kusa da iyakokinmu, tafiyar ba ta wuce ta kilo mita 15 ba,'' in ji shi.
Aisha Buhari ta yi wa 'yan Zamfara addu'a
Asalin hoton, Aisha Muhammadu Buhari / Facebook
Uwargidan shugaban Najeriya Aisha Muhammadu Buhari ta wallafa wani sako a shafinta na Facebook inda a ciki ta yi wa al'ummar jihar Zamfara ta arewa maso yammacin kasar addu'ar zaman lafiya.
Aisha Buhari ta wallafa sakon ne da misalin karfe 12:09 na daren Laraba, inda ta roki Allah ya samar wa mutanen jihar - har da sauran 'yan kasar - mafita daga matsalar tsaron da ta addabe ta, musamman a lokacin da Musulmi ke raya dare domin neman falalar Lailatul Kadri:
"Allah ya fitar da mu da mutanen jihar Zamfara daga chikin wannan hali, albarkacin daren Lailatul Kadri, Ameen!"
Baya ga sakon, uwargidan shugaban Najeriyar ta kuma wallafa wani sako na sauti mai tsawon minti 3:53, wanda a ciki ana iya jin wani mutumin da bai fadi sunansa ba yana sanar da wani mutumin da ya kira 'Haji Abdurrahman' labarin wani kamun da 'yan sa-kai suka yi wa wasu barayin daji a yankin Tsafe da Mada na jihar Zamfara.
A farkon sautin ana iya jin muryar wata mata da ke cewa, "Ga shi ku ji me yake fada..." Sai dai ba mu san ko muryar ta uwargidan shugaba Buhari ba ce.
Naira miliyan 44 ta yi batan dabo a sakatariyar jam'iyyar APC ta kasa
Jam'iyar APC na binciken yadda Naira miliyan 44.2 suka yi batan dabo ranar Laraba a sakatariyar jam'iyar da ke Abuja.
Batan kudin ya janyo dakatar da sayar da fom din 'yan takara, musamman 'yan takarar da ke son tsayawa takarar mukaman 'yan majalisar wakilai da na dattawa.
Jam'iyyar ta kafa wasu rumfuna domin sayar da fom din ga masu son tsayawa takara.
Sai dai da misalin karfe 4:15, jam'iyyar ta cire rumfunan kuma ta umarci ma'aikatanta su ci gaba da sayar da fom din a cibiyar gudanar da taruka ta International Conference Centre da ke Abuja.
Wani ma'aikacin jamiyyar da baya son a bayyana sunansa ya ce an cire rumfunan ne bayan da aka gane kudaden sun yi batan dabo.
Ma'aikacin ya ce "Mun ji cewa wani mutum da yazo sakatariyar jam'iyyar, sai dai saboda yawan jama'a bai iya shiga cikin ginin ba da motarsa. Amma yayin da yake kokarin shiga cikin ginin, mun ji wai wani ambulan da yake dauke da shi wanda dala 75,000 ke ciki ya fadi."
Ghana: Ana shirin sake binne Kwame Nkrumah shekara 50 bayan mutuwarsa
Asalin hoton, Getty Images
Jam'iyyar adawa ta Convention People’s Party (CPP) a Ghana ta bayyana wani shirinta na sake binne shugaban kasar na farko, marigayi Kwame Nkrumah a watan Nuwamba mai zuwa.
Jam'iyyar wadda aka kafa tun zamanin da Ghana ta sami ''yancin-kai daga turawan mulkin mallaka na Birtaniya ta ce ba a ba Mista Nkrumah karramawar da ya cancanci samu ba yayin da ya mutu a watan Afrilun 1972.
Jam'iyyar ta ce "ruhinsa bai huta ba."
Nkrumah ya mutu ne shekara 50 da ta gabata bayan da ya yi jinya a birnin Bucharest na kasar Romaniya kuma an binne shi a kauyen da ya fito na Njroful a kudancin Ghana.
Sai dai daga baya an mayar da gawarsa zuwa wani gini na musamman a birnin Accra.
Jam'iyyar CPP ta ce za ta fitar da wani jadawali na ayyukan da za a yi wanda za a karkare da "binne wa ta ainihi" da za a yi wa tsohon shugaban.
Tashar talabijin ta Joy News ta wallafa wani bidiyo na kalaman babban magatakardan jam'iyyar Nana Yaa Jantuah kan shirin sake binne tsohon shugaban.
Mutum fiye da miliyan biyu ne suka yi Qiyamul Layli a Masallacin Harami
Hukumomi a Saudiyya sun bayyana cewa mahajjata fiye da miliyan biyu ne suka yi Qiyamul Layli a Masallacin Harami.
Shafin intanet na Haramain Sharifain ne ya bayyana haka a wani sakon Tuwita.
"Mahajjata da masu ziyara fiye da miliyan biyu ne suka yi tsaiwar Qiyam Al Layl Prayers a Masjid Al Haram, Makkah a daren 27 na watan Ramadan," in ji sakon.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Mahajjata da ma sauran Musulmai dai suna sa ran dacewa da Daren Laylatul Qadri a irin wadannan darare da ake kira mara - wato 21, 23, 25, 27, da kuma 29.
Dubban Musulmai ne suka shiga kasar ta Saudiyya a bana domin aikin Umrar, bayan kasar ta sassauta dokokin cutar korona.
Matar da aka sace a jirgin kasan Abuja-Kaduna ta haihu a hannun masu garkuwa da ita
Asalin hoton, OTHER
Daya daga cikin fasinjojin da 'yan fashin daji suka sace daga jirgin kasan da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna ranar 28 ga watan Maris ta haihu a hannun masu garkuwa da ita.
Tashar talabijin ta AriseTV, wadda ta wallafa wannan labarin, ta kuma ce wani dan uwan matar ne ya sanar da su haka.
Dan uwa nata ya sanar cewa an kai wani likita wurin da ake rike da ita wanda ya taimaka mata wajen haihuwa.
"Matar na da tsohon ciki wanda ya kai wata takwas yayin da aka sace ta da sauran gwamman fasinjoji, kuma ta haihu ne bayan da 'yan ta'addan suka gayyaci likitoci su karbi haihuwar. Sai dai ba mu san halin da abin da ta haifa yake ba," in ji dan uwan matar.
A farkon wannan makon ne dai masu garkuwa da mutanen suka wallafa hotunan fasinjojin da kawo yanzu suka shafe wata guda cur a hannunsu.
Sojan Najeriya ya kashe kansa bayan ya shiga hannu kan tuhumar taimaka wa ISWAP
Asalin hoton, AFP
Rahotanni daga yankin arewa maso gabashin Najeriya na cewa wani sojan kasar ya kashe kansa bayan da aka kama shi bisa zargin aiki tare da mayaka masu ikirari jihadi na kungiyar ISWAP.
Wakilin BBC ya ce wata majiya mai kusanci da rundunar sojojin Najeriya ta sanar da shi cewa lallai sojan na da hannu a wasu hare-hare da aka kai kan wasu al'umomin jihar Yobe a cikin makonni da suka gabata.
Manyan hafsoshin sojin kasar sun fara sa ido kan sojan ne bayan da aka kai wasu hare-hare biyu a garuruwan Geidam da Gashua na jihar ta Yobe, kuma daga nan suka fara bibiyar wuraren da yake zuwa cikin sirri.
An kuma kama shi yayin da yake kokarin tserewa, bayan da ya gane cewa dubunsa ta cika.
Sai dai sojan - wanda kwararre ne wajen sarrafa makamai - ya kwace wata bindiga a hannun daya daga cikin sojojin da ke rakiyarsa kuma ya kashe kansa duk da cewa an saka masa ankwa a hannu.
A makon jiya wasu wadanda ake zargi mayakan ISWAP ne suka kai wani hari kuma suka kashe akalla mutum goma, ciki har da mata.
Wannan harin ya biyo bayan wani harin na daban da aka dasa wani bam wanda ya halaka mutum shida baya ga raunata wasu mutum 19 a jihar Taraba, harin da kungiyar ISWAP ta dauki alhakin kai shi.
Maraba
Barkanmu da wayewar gari wannan rana ta Alhamis!
A yau ma BBC hausa za ta ci gaba da ayyukan sanar da ku da ilmantar da ku abubuwan da ke wakana a sassan duniya.
Sani Aliyu ne yake tare da ku a wannan rana, kuma ni ne zan jagoranci sada ku da labarai da rahotannin da ke tafe.