Rufewa
A nan muka kawo karshen labarai da rahotanni na kai tsaye, da muke ba ku a wannan shafi.
Sai ku tare mu gobe domin samun sabbin labarai da rahotanni daga sassa daban-daban na Duniya.
Badriyya Tijjani Kalarawi ke sallama da ku, mu kwana kalau.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.
Sani Aliyu and Badariyya Tijjani Kalarawi
A nan muka kawo karshen labarai da rahotanni na kai tsaye, da muke ba ku a wannan shafi.
Sai ku tare mu gobe domin samun sabbin labarai da rahotanni daga sassa daban-daban na Duniya.
Badriyya Tijjani Kalarawi ke sallama da ku, mu kwana kalau.

An yi jana'izar gwamman wadanda suka mutu a jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya, sakamakon gobarar da ta tashi a wurin matatar mai ba bisa ka'ida ba.
Ma'aikatan agajin gaggawa sun ce kawo yanzu an tabbatar da mutuwar mutum 110 a ibtila'in na ranar Juma'ar da ta gabata, ya yin da sama da mutum 70 ke kwance a gadon asibiti cikin halin rai kwa-kwai-mutu-kwakwai.
Yawancin wadanda lamarin ya rutsa da su sun hada da ma'aikatan matatar man, da kwastomomi da suka zo sayen mai a wurin da aka kafa ba bisa ka'ida ba.
Mutanen sun kone kurmus, wasu sun salube ta yadda babu wanda za a iya ganewa. Sai dai jami'ai sun ce wasu iyalan sun dauki gawar 'yan uwansu da ba su kone kurmus ba, wasu kuma sun dauke yan uwansu domin yi musu jana'iza.
Ana yawan samun karuwar fashewar bututan mai a kudancin Najeriya, a yankin Naija Delta mai arzikin mai sakamakon yadda ake samun karuwar kafa matatun tace mai ba bisa ka'ida ba a cikin dazuka.
Kawo yanzu ba a san musabbabin tashin gobarar ba, sai dai wasu sun danganta hakan da fashewar bututun iskar gas, tuni hukumomi suka ayyana neman ainahin mai matatar man ruwa a jallo.

Asalin hoton, Reuters
Hukumomi a birnin Shanghai na China, sun yi amfani da korayen karafa wajen katange kofofin gidajen mutane da na shaguna a tituna sakamakon karuwar masu cutar korona a birnin.
Mazauna unguwannin sun wayi gari da ganin korayen karafan da aka shinge gidajensu da shi ba tare da an sanar da su ba.
Wani mazaunin Shanghai ya shaidawa BBC cewa, ya wayi garin ranar Talata da ganin koren karfen tokare a kofar gidansa babu kuma wanda ya yi masa bayanin komai.
Makwannin da suka gabata dai rabin birnin Shanghai mai al'umma miliyan 25 ya kasance karkashin dokar kulle, saboda sake barkewar cutar korona.
An wallafa hotunan jami'ai sanye da tufafin kariya, su na rufe kofafon gidaje da kantuna, d mkarantu da wuraren taruwar jama'a.
Yawancin karafan sun kai tsahon mita biyu, kuma yankin da aka sanya karafan mutum daya ne kadai gwaji ya nuna ya na dauke da cutar korona.
Hukumar Hizba a jihar Kano da ke arewacin Najeriya, ta kama wasu matasa takwas da ake zargi da kwacen waya a masalallacin al-Fur'an da ke karamar hukumar Nasarawa da ke jihar.
Kwamandan Hizba Sheikh Harun Ibn Sina, ya tabbatar da hakan ga manema labarai a ranar Talata.
Ya ce an kama wadanda ake zargin da ranar Allah suna shan muggan kwayoyi da sauran ababen maye a kusa da masallacin.
Ibn Sina ya bayyana dabi'ar matasan da haramtacciya da ba ta dace ba a wannan wata mai alfarma na Azumin Ramadan.
Ya yi kira ga jama'a su kara sanya ido da kai rahoton duk wani abu da suka ga ya na faruwa da bai gamsar da su ba, ko wani mutum, su kuma hukumarsu ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen daukar mataki da hukunta wanda aka samu da laifi.

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Masar ta yi amai ta lashe kan matakin hana sallar Tahajjud a fadin kasar.
Hakan ya biyo bayan sukar da ta sha daga al’umma musamman Musulmi da suka saba haduwa a goman karshe na watan Ramadana.
Ministan lamurran addini Muhammad Mokhtar sun so hana haduwa masallatai Sallar daren ne don gudun yada cutar korona.
Amma Musulmi sun ƙalubalanci matakin gwamnatin, wadda ta amince mabiya addinin kirista haduwa don gudanar da bikin Easter makon da ya wuce da kuma filaye wasanni da ake cika makil.

Asalin hoton, @antonioguterres
Sakataren majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya fada wa Sakataren harkokin wajen Rasha Sergie Lavrov cewa dole a yi duk yadda za a yi a kawo karshen yaki tsakanin Rasha da Ukraine.
Sai dai Mr Lavrov ya ce yana sa ran za a kawo karshen rikicin ta hanyar kulla yarjejeniya, duk da a zahiri babu alamun yakin zai kare nan kusa.
A ziyarar da ya ke yi a Moscow Mr Guterres zai kuma gana da Shugaba Vladimir Putin.
Guterres yace makasudin ziyarar tasa shine samar da hanyar tattaunawar sulhu tsakanin kasashen biyu, da zai haifar da zaman lafiya a karshe.
A na sa ran Mr Guterrez zai gana da Volodymyr Zelensky na Ukraine a ranar Alhamis.
Gwamnatin Jamus ta sanar da shirin aikewa da Ukraine tankokin yaki 50 don tunkarar hare-haren Rasha.
Hakan na nufin Jamus ta sauya matsayarta na kin aike wa da manyan kayan yaki ga kasashen da ke tsakiyar yaki.
An zargi shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz da jan kafa wurin aikewa Ukraine da manyan makaman yaki, amma a yanzu gani ya kori ji game da sanin bangaren da Jamus take a wannan yaki.
Haka kuma matakin na zuwa a dai-dai lokacin da ministoci daga kasashe 40 ke ganawa da NATO a wani sansanin sojin Amurka da ke Jamus don tattauna aikawa da karin makamai zuwa Ukraine.

Asalin hoton, AFP
Rundunar sojojin Najeriya ta ce dakarunta sun kashe wasu 'yan kungiyar IPOB biyu da ke neman ballewa daga Najeriya a wani ba-ta-kashi da suka yi.
A wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na Tuwita ranar Talata, ta ce dakarun nata sun kuma kama 'ya'yan kungiyar ta IPOB guda hudu a Orlu da ke jihar Imo a kudu maso gabashin kasar ranar 25 ga watan Afrilun 2022.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Sanarwar ta kara da cewa binciken da aka gudanar a wayoyin salula na mutanen ya nuna hotuna da bidiyo na mutanen da aka kashe a wuraren wuraren bauta na gargajiya.
Kazalika an gano bindigogi da sauran miyagun abubuwa a hannun mutanen, in ji rundunar sojin.

Asalin hoton, Reuters
Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta kara kiyasin da ta yi na mutanen da ake sa ran za su tsere daga Ukraine a wannan shekarar sakamakon yaki, zuwa mutum miliyan takwas da dubu dari uku.
A kiyasin da ta yi a watan Maris, ta bayyana cewa 'yan gudun hijira miliyan hudu ne za su bar kasar, sai dai tuni kiyasin ya zarta hakan.
Ya zuwa yanzu mutum fiye da miliyan biyar ne suka tsere daga kasar tun lokacin da Rasha ta kaddamar da yaki a kasar a watan Fabrairu, yayin da tuni yakin ya raba karin mutum miliyan bakwai da dubu dari bakwai daga muhallansu.

Asalin hoton, Getty Images
Tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya ce ba shi da niyyar komawa Twitter ko da an dawo masa da shafinsa shafin da aka rufe yayin yana shugaban kasar.
Jagoran jam'iyyar adawa ta Republican ya ce zai ci gaba da amfani da nasa shafin sada zumuntan da ya kaddamar mai suna Truth Social.
Sai dai sau daya kawai ya wallafa wani abu a shafin tun bayan da aka kaddamar da shi a watan Fabrairu:
"Ba zan koma Twitter ba, zan yi zamana a shafina na TRUTH ne," inji Mista Trump.
An dai rufe shafinsa na Twitter na dindindin ne bayan da aka tsige shi daga mukaminsa na shugaban kasa a karo na biyu - kuma bayan da magoya bayansa suka afka wa ginin majalisar kasar.

Asalin hoton, Getty Images
Jagoran kungiyar 'yan aware ta IPOB a kudu maso gabashin Najeriya ya shigar da kara a watan kotun tarayyar kasar yana neman ta soke wani umarni da bangaren shari'a ya fitar a farko wannan watan da ke cewa za a daina sauraren dukkan shari'u na ta'addanci a bainar jama'a.
Nnamdi Kanu ya sanar da kotun ta hanyar lauyoyinsa cewa umarnin ya taka tsarin mulki da wasu dokokin kasar kuma ya kamata ta soke shi.
A ranar 8 ga watan nan ne mai shari'a John Terhemba Tsoho ya bayar da umarnin daina sauraren shari'un da ke da alaka da ta'addanci a bainar jama'a domin kiyaye tsaron dukan wadanda ke da alaka da shari'ar.
Alkalin ya hana 'yan jarida halartar zaman kotunan da ke sauraren irin wadannan shari'un.
Baya ga alkalin da zai saurari shari'ar, mutanen da aka amince musu shiga dakin shari'ar su hada da wasu zababbun ma'aikatan kotun da jami'an tsaro.
Mista Kanu ya musanta aikata wani alifi.

Rahotanni na cewa gwamnatin tarayyar Najeriya ta fara aiwatar da tsarin nan na 'babu aiki, babu albashi' kan malaman jami'o'in kasar da ke yajin aiki.
Idan ba a manta ba, kungiyar malaman jami'a a Najeriya ASUU ta tsunduma yajin aikin mako hudu a ranar 14 ga watan Fabrairu, wanda ta sabunta bayan ya kare.
Jaridar Vanguard ta ce shugaban kungiyar National Association of Academic Technologists Comrade Ibeji Nwokoma, ta malaman jami'a ya tabbatar cewa ba a biya mambobin kungiyar albashinsu na watan Maris ba.
Sai dai Mista Nwokoma ya ce wannan matakin na gwamnati ba zai hana su neman hakkokinsu ba.
Ma'aikatar tsaron Rasha ta yi ikirarin kashe sojojin Ukraine 500 jiya da daddare yayin wasu hare-hare ta sama da ta kai a wurare 87 a Ukraine.
Bataliyoyin soji biyu da ke Kharkiv na cikin wuraren da rahotanni suka ce sojin Rasha sun kai wa hari.
Ma'aikatar ta wallafa wani bidiyo a shafinta na intanet da ke nuna wuraren da dakarunta suka kwace daga hannun sojojin kasa na Ukraine.
Bidiyon ya kuma nuna tankokin yaki da wasu motoci.
Bayanai sun nuna cewa sun samu makamai da wasu takardu da sauran kayayyaki na sojojin Ukraine a wuraren.
BBC ba ta iya tabbatar da gaskiyar wannan ikirari ba.

Asalin hoton, KNCA/REUTERS
Shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong-un, ya sha alwashin hanzarta kera makaman nukiliya tare da sanya su cikin shirin don fara amfani da su nan take.
Da yake magana a wajen faretin bikin cika shekaru 90 da kafa rundunar sojin kasar, Mista Kim ya yi gargadin shafe duk wata kasa da ke neman jan-zare da Pyongyang a kan wannan aniya.
Wakiliyar BBC ta ce hotunan da kafafen watsa labaran kasar suka wallafa sun nuna babban makami mai-linzamin kasar na Hwasong-17 wanda aka kammala gwajinsa a watan jiya, bayan tabbatar da cewa zai iya kai wa Amurka.
Wasu hotunan tauraron dan adam na baya-bayan nan sun nuna cewa ana ci gaba da aikin dawo da ramukan kera makaman da aka lalata a shekarar 2017 bayan Kim Jong-un ya tattauna da tsohon shugaban Amurka Donald Trump.

Asalin hoton, AFP
Yayin da 'yan Najeriya ke shirin gudanar da bukukuwan sallah karama a farkon mako mai zuwa, yawancin kamfanonin sufurin jirgin sama sun kara farashin tikitin jirgin sama na cikin-gida.
Sai dai ba dukkan wurare ne wannan karin ya shafa ba.
Matafiya tsakanin biranen Legas zuwa Abuja da Legas zuwa Port Harcourt da kuma Legas zuwa Uyo za su ci gaba da sayen tikitin a farashin da ke kusa da Naira 50,000 da ake biya a baya-bayan nan.
Karin ya fi bayyana ne idan matafiyi ya nufi biranen da ke arewacin kasar daga kudanci, inda farashin tikitin ya tashi zuwa Naira 122,000.00 na zuwa kawai banda na dawowa.
Jaridar Daily Trust ta ce wannan matakin zai tilastawa wasu 'yan Najeriya sauya shirin da suka yi na tafiya garuruwansu domin bukukuwan sallah.

Asalin hoton, Getty Images
Mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya ce ya ci amanar kasa idan bai tsaya takarar mukamin shugaba kasa ba a shekarar 2023.
Mista Osinbajo ya bayyana haka ne ranar Litinin yayin wata ziyara da ya kai jihar Ondo, kuma ya gana da gwamnan jihar Rotimi Akeredolu da masu ruwa-da-tsaki na jam'iyyar APC.
Ya kuma ce rike mukamin mukaddashin shugaban kasa da ya yi a wasu lokuta ya ba shi kwarewar da yake bukata domin ya jagoranci Najeriya.
"Mutane na mutuwa a kowace rana, saboda haka zai kasance cin amanar kasa idan na yi ritaya kuma na koma Legas ko Ikenne bayan wa'adin mulkinmu. Ban yi wa kasar nan adalci ba," in ji Osinbajo.
A nasa bangaren, Gwamna Akeredolu ya ce duk da cewa 'yan deleget na jihar suna son sa kuma suna mutunta shi, ubangiji ne kawai ke bayar da mulki.
Osinbajo ya sanar da aniyarsa ta neman mukamin shugaban Najeriya a ranar 11 ga watan Afrilu, kuma tun ranar yake kai ziyara sassan kasar yana neman goyon bayan 'yan kasar.
Barkanmu da safiyar Talata daga Sashen Hausa na BBC.
A yau ni Sani Aliyu ne zan jagoranci sanar da ku halin da duniya ta ke ciki ta hanyar wallafa rahotanni da labarai daga Najeriya da yankin Afirka ta Yamma da ma sauran kasashen duniya.
Sai ku kasance da BBC Hausa.