Shalkwatar rundunar hadin gwuiwa da ke da cibiya a birnin Ndjamena na kasar Chadi, wadda ta hada da sojojin Najeriya da na Nijar, ta sanar cewa dakarunta sun gudanar da samame tare da sojojin sama a yankin Tafkin Chadi.
Rundunar ta ce sojojin sama sun gano maboyar wasu mayakan Boko Haram a kusa da Tumbun Fulani da Tumbun Rago kuma sun kashe 20 cikinsu.
Sanarwar da kakakin rundunar, Kanar Muhammad Dole, ta fitar ta kuma ce bayan da sojojin sama suka gama luguden wuta, sai dakarun kasa suka kutsa wurin kuma suka fatattaki sauran mayakan na Boko Haram.
Wasu mayakan sun yi watsi da kayayyakinsu da kuma bindigoginsu kafin suka shiga cikin ruwan tafkin Chadi domin tsira da rayukansu.
Sojojin sun ga gawarwakin mayakan da samamen da aka kai ta sama ya halaka, amma wani soja ya rasa ransa a sanadiyyar hare-haren da aka kai a yankin, kuma an raunata wasu sojojin, amma an kai su wani asibitin sojoji domin ba su kulawa ta musaman.
Baya ga makaman da mayakan suka bari.
Sojojin rundunar hadingwiwarsun kuma gano wasu makamai da harsasai masu yawa.#
Kanar Muhammad Dole ya kuma sanar cewa sojojin sun gudanar da ayyukan tsaro a wani yanki da ke cikin kasar Kamaru, kusa da Toumbuma, Kerenua, da kuma Chikingudu inda suka halaka wasu mayakan Boko Haram biyu.
Ya kuma ce sun ci karo da wasu mata guda shida da suka tsere daga hannun mayakan Boko Haram.
Bayan an ba matan kulawa ta musamman domin duba lafiyarsu, dakarun rundunar sun mika su ga jami'an gwamnati a yankn domin a mika su ga 'yan uwansu.
A karshe, sanarwar ta ce bincike ya tabbatar cewa matan da suka tsere wa mayakan Boko Haram sun fito ne daga jihohin Adamawa da Borno da Gombe da kuma Yobe a tarayyar Najeriya, kuma an sace su ne tsakanin watan Oktoban 2020 da na Afrilun 2021.
Sanarwar ta kuma bayyana sunayen matan da shekarunsu, baya ga wuraren da aka sato su kafin mayakan Boko Haram suka yi garkuwa da su.