Kudin aikin Hajji na bana ba zai gaza Naira miliyan biyu da rabi ba - NAHCON

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya and Sani Aliyu

  1. Sallama

    Mun kawo karshen wannan yini na sanar da ku abubuwan da ke faruwa a sassan duniya daga Sashen Hausa na BBC.

    Sai ku biyo mu gobe domin sanin yadda duniya ta tashi.

    A madadin Umar Mika'il da sauran abokan aikina, ni Sani Aliyuke muku fatan alheri.

    Bari in bar ku da wannan hoton, na wani yaro a kasuwar kaji a birnin Addis Ababa na kasar Habasha.

    Photo of a young boy at a livestock market in Ethiopia's capital, Addis Ababa:

    Asalin hoton, Getty Images

  2. Sojoji sun kashe 'yan Boko Haram 20, sun ceto matan da aka yi garkuwa da su

    Shalkwatar rundunar hadin gwuiwa da ke da cibiya a birnin Ndjamena na kasar Chadi, wadda ta hada da sojojin Najeriya da na Nijar, ta sanar cewa dakarunta sun gudanar da samame tare da sojojin sama a yankin Tafkin Chadi.

    Rundunar ta ce sojojin sama sun gano maboyar wasu mayakan Boko Haram a kusa da Tumbun Fulani da Tumbun Rago kuma sun kashe 20 cikinsu.

    Sanarwar da kakakin rundunar, Kanar Muhammad Dole, ta fitar ta kuma ce bayan da sojojin sama suka gama luguden wuta, sai dakarun kasa suka kutsa wurin kuma suka fatattaki sauran mayakan na Boko Haram.

    Wasu mayakan sun yi watsi da kayayyakinsu da kuma bindigoginsu kafin suka shiga cikin ruwan tafkin Chadi domin tsira da rayukansu.

    Sojojin sun ga gawarwakin mayakan da samamen da aka kai ta sama ya halaka, amma wani soja ya rasa ransa a sanadiyyar hare-haren da aka kai a yankin, kuma an raunata wasu sojojin, amma an kai su wani asibitin sojoji domin ba su kulawa ta musaman.

    Baya ga makaman da mayakan suka bari.

    HQ MNJTF NDJAMENA

    Asalin hoton, HQ MNJTF NDJAMENA

    Sojojin rundunar hadingwiwarsun kuma gano wasu makamai da harsasai masu yawa.#

    Kanar Muhammad Dole ya kuma sanar cewa sojojin sun gudanar da ayyukan tsaro a wani yanki da ke cikin kasar Kamaru, kusa da Toumbuma, Kerenua, da kuma Chikingudu inda suka halaka wasu mayakan Boko Haram biyu.

    Ya kuma ce sun ci karo da wasu mata guda shida da suka tsere daga hannun mayakan Boko Haram.

    HQ MNJTF NDJAMENA

    Asalin hoton, HQ MNJTF NDJAMENA

    Bayan an ba matan kulawa ta musamman domin duba lafiyarsu, dakarun rundunar sun mika su ga jami'an gwamnati a yankn domin a mika su ga 'yan uwansu.

    A karshe, sanarwar ta ce bincike ya tabbatar cewa matan da suka tsere wa mayakan Boko Haram sun fito ne daga jihohin Adamawa da Borno da Gombe da kuma Yobe a tarayyar Najeriya, kuma an sace su ne tsakanin watan Oktoban 2020 da na Afrilun 2021.

    Sanarwar ta kuma bayyana sunayen matan da shekarunsu, baya ga wuraren da aka sato su kafin mayakan Boko Haram suka yi garkuwa da su.

    HQ MNJTF NDJAMENA

    Asalin hoton, HQ MNJTF NDJAMENA

  3. Sophie Wilmes: Ministar harkokin wajen Belgium da ta ajiye aiki domin kulawa da mijinta da ke jinya

    Ms Wilmes said her husband has been diagnosed with "aggressive cancer of the brain".

    Asalin hoton, Getty Images

    Ministar harkokin waje ta kasar Belgium ta ce za ta ajiye aikint ana wani lokaci domin kulawa da mijinta wanda ke jinyar cutar kansar kwakwalwa.

    Sophie Wilmes wadda ke rike da mukamin mataimakiyar firaministar kasar ta ce za ta dauki hutu "zuwa karshen watanni masu zafi" inda a lokacin ita da 'yan uwanta za su sake duba halin da mijin nata ke ciki kafin ta yanke shawarar abin da za ta yi.

    Cikin wata sanarwa da ya fitar, firaministan kasar Alexander De Croo ya bayyana zabin da Ms Wilmes ta yi a matsayin wanda ya kamata "kowa ya mutunta".

    Sai dai ministar ba za ta sauka daga mukamin nata ba baki daya, amma za ta mika ayyukanta ga wasu ministocin.

    Ms Wilmes da mijinta Chris Stone dan asalin kasar Australia sun yi aure ne a 2009, kuma suna da 'ya'ya uku.

  4. Kudin aikin Hajji na bana ba zai gaza Naira miliyan biyu da rabi ba - Abdullahi Hardawa

    Al'ummar Najeriya na ci gaba da tsokaci kan matakin gwamnatin Saudiyya na ware kujeru fiye da 40,000 ga maniyatta aikin Hajji na kasar.

    Annobar korona dai ta hana gudanar da aikin Hajjin shekara uku da ta gabata.

    A yau Alhamis ne hukumar alhazai ta Najeriya NAHCON ta gudanar da wani taro da shugabannin hukumomin alhazai na jihohi.

    Alhaji Abdullahi Hardawa kwamishina ne ami kula da aikace-aikace a hukumar alhazai ta kasa, kuma ya shaida wa Ahmed Abba Abdullahi abin da aka cimma a wajen taron da aka yi a Abuja.

    Bayanan sautiAbdullahi Hardawa NAHCON
  5. China ta yi Allah-wadai da kona Qur'an da aka yi a Sweden

    Sweden riots

    Asalin hoton, Getty Images

    China ta yi Allah-wadai da matakin Sweden na koma al-Kur'ani.

    "'Yancin fadin albarkacin baki ba hujja ba ne ba cin zarafi ko nuna wariya, wanda ke raba kan al'umma," in ji Wang Wenbin, kakakin ma'aikatar harkokin wajen China.

    "Muna fatan Sweden za su mutunta musulmai marasa rinjaye da addininsu," kamar yadda ya bayyanawa jaridar Global Times.

    A watan jiya ne, Rasmus shugaban masu tsattsauran ra'ayi ya kona Kur'ani a Linkoping, da ke Sweden. Kuma ya yi barazanar zai kona wasu littatafai na daban.

  6. Aisha Buhari ta gayyaci dukkan 'yan takara zuwa shan ruwa a Aso Rock

    Uwargidan shugaban Najeriya Aisha Buhari

    Asalin hoton, Aisha Buhari / Facebook

    Bayanan hoto, Uwargidan shugaban Najeriya Aisha Muhammadu Buhari

    Uwargidan shugaban Najeriya Aisha Buhari ta gayyaci 'yan takarar mukamin shugaban kasar zuwa shan ruwa a Fadar Aso Rock Villa a ranar Asabar.

    Hajiya Aisha ta mika gayyatar ce ga dukkan 'yan takara daga dukkan jam'iyyun kasar, inda cikin wani rahoto da ta wallafa, tashar talabijin ta Channels ta ce mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo.

    Akwai kuma 'yan takara 17 daga babbar jam'iyyar PDP mai adawa - kamar gwaman Nyesom Wike na jihar Rivers, da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da sauran 'yan takara daga jam'iyya mai mulki ta APC.

    Wani abu da ya ja hankulan mutane shi ne katin gayyatar zuwa shan ruwan, domin a ciki an bukaci dukkan wadanda aka gayatar su guji zuwa da wayoyinsu na hannu zuwa shan ruwan, kuma katin ne zai ba su damar shiga Fadar Shugaban Najeriya.

  7. Za a kara kudin aikin Hajji da kashi 50 cikin 100 a bana - NAHCON

    Millions of Muslims dey gada for holy sites for Saudi Arabia evry year.

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar alhazai ta kasa a Najeriya NAHCON ya ce da dukkan alamu za a kara kudin aikin Hajji da akalla kashi 50 cikin 100 daga wanda maniyata suka biya a 2019.

    jaridar Daily Trust ta ce a 2019 maniyata sun biya naira miliyan 1.5 ne, saboda haka wadanda suka ajiye kudin guzuri tare da hukumar NAHCON na bukatar kara biyan kimanin naira miliyan 1 ke nan.

    Yayin wani taro da hukumar ta yi da jami'an da ke kula da hukumomin aikin Hajji na jihohin Najeriya, shugaban NAHCON Alhaji Zikrullah Hassan ya ce hauhawar farashi ga tattalin arzikin duniya ne ya janyo wannan matsalar.

    Ya ce a shekarar 2019, a na sauya dalar Amurka daya kan Naira 306, inda a bana ya koma Naira 410 kan kowace dala.

    Y abayyana cewa kashi 97 cikin 100 na kudaden aikin Hajji na tafiya ga biyan ayyuka da ake biya da kudaden waje ne kamar sayen tikitin jirgi da na masauki a kasa mai tsarki.

  8. An kama malaman makaranta 70 da suka shirya zanga-zangar Tehran

    Kakakin kungiyar Malaman makarantu a Tehran Mohammad Habibi, ya ce an kama malamai 70 da suka shirya taruwa a bakin ma'aikatar ilimi domin gudanar da zanga-zanga.

    Mista Habibi ya ce an kama malamai mata guda 40 sannan kuma aka kama malamai maza 30 a Gisha.

    A wasu birane na Iran, malaman sun gudanar da babbar zanga-zanga.

  9. Na bi tsarin mulki wajen yi wa Joshua Dariye da Jolly Nyame afuwa - Buhari

    BBC

    Fadar shugaban kasar Najeriya ta kare matakinta na yi wa wasu tsofaffin gwamnonin kasar wadanda ke tsare a gidan yari saboda cin hanci da rashawa afuwa.

    Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Najeriya, Garba Shehu ya fitar, ya ce Buhari ya yi wa gwamnonin - Joshua Dariye da Jolly Nyame - afuwa ne saboda matsalar rashin lafiya bayan an duba yanayin da suke ciki.

    Ya ce shawarar da majalisar magabata ta kasar ta bayar na a yi wa tsofaffin gwamnonin da wasu mutum 157, "hukunci ne da aka yanke cikin nutsuwa, kuma doka ta amince da hakan ba don cimma wata manufar siyasa ba."

    Duka gwamnonin dai na zaman gidan kaso ne bayan fuskantar shari'ar cin hanci da rasha da aka yi musu, kuma kotun koli ta yanke musu hukunci.

    'Yan Najeriya da dama dai sun yi ta Allah-wadai da wannan mataki, suna cewa, nawa ne masu fama da rashin lafiya da ke zaune gidan yarin ba a yi musu afuwa ba sai wadannan.

    Ka zalika wasu na sukar cewa akwai wadanda suka fi su shekaru a zaune a gidan, wadanda wasu ko shari'a ba a yi musu ba.

    A cikin sanarwar Malam Garba Shehu ya ce idan Buhari bai yi wa wadannan dattijai gafara ba, za a rika yi masa kallon mutum mara tausayi.

  10. An kashe wani sojin Rasha a Mali

    AFP

    Asalin hoton, AFP

    Rahotanni daga Hombori a yankin Mopti da ke Mali na cewa an an kashe wani sojin Rasha guda.

    Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ambato wata sanarwar sojoji da tace, wani mai bayar da shawara na Rasha ya taka wani bam na dasawa da safiyar ranar Talata.

    Rahotannin sun ce dan Rashan ya mutu bayan daukar shi da aka yi a jirgi aka kai shi asibitin da ke garin Sevare.

    AFP ya ce wani jami'i a Sevare ne ya tabbatar musu da mutuwar.

    Rundunar sojin Mali dai ba ta ce komai ba kan lamarin.

  11. Labarai da dumi-dumi, Shugaba Buhari na tattaunawa da manyan hafsoshin tsaro

    Bashir Ahmad

    Asalin hoton, Bashir Ahmad

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na tattaunawa yanzu haka da shugabannin hafsoshin tsaro da kuma wasu hukumomi da ke da alaka da tsaro a kasar.

    Ana yin tattaunawar ne domin ba shi bayanain kan kalubalen da ake fuskanta a bangaren tsaron a wasu sassan kasar.

    Najeriya dai na fama da matsalolin tsaro kama daga matsalar 'yan a ware zuwa masu garkuwa da mutane ga 'yan bindiga sai kuma uwa uba Boko Haram.

    Bashir Ahmad

    Asalin hoton, Bashir Ahmad

    Bashir Ahmad

    Asalin hoton, Bashir Ahmad

    Bashir Ahmad

    Asalin hoton, Bashir Ahmad

  12. Wasu tagwayen hare-hare sun jikkata yara biyu a Kabul

    Rahotanni na cewa yara sun jikkata a wata fashewa da aka samu a yammacin birnin Kabul a safiyar yau.

    Taliban ta ce yara biyu ake zaton sun jikkata a fashewar ya lardin Qambar da ke Kabul.

    Babu wani karin bayani da aka bayyana ya zuwa yanzu.

    A gefe guda kuma, an kashe wasu dalibai a jerin tagwayen hare-haren da aka kai a kofar shiga makarantar Abdul Rahim da ke yammacin Kabul a ranar Talata.

  13. Sarauniyar Elizabeth na bikin cika shekara 96 a duniya

    EB

    Asalin hoton, EB

    Sarauniya Elizabeth ta Ingila na bikin cika shekaru casa'in da shida da haihuwa, a shekarunta na 70 kan karagar mulki.

    Za ta shafe wunin yau a gidanta da ke Sandringham a Norfolk, sai dai za ayi harbin bindiga a fadarta da ke Landan da HydePark, sannan za su ayi kade-kaden gangar sojoji.

    Sarauniya a watanni baya-bayanan tana ta fama da rashin isashen lafiya, ko da yake jikanta, Yarima Harry ya ce tana samun lafiya a wata hira da aka yi da shi a farkon makon nan.

  14. Buhari ya yi jaje kan mutuwar sojojin saman Najeriya

    Sojojin da suka mutu

    Asalin hoton, Facebook/Garba Shehu

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi jajen mutuwar sojojin Najeriya biyu wadanda suka yi hatsarin jirgin saman soji a Kaduna da ke arewacin kasar.

    A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Mallam Garba Shehu, ya fitar ya ambato Shugaba Buhari yana bayyana "damuwarsa" bisa mutuwar Flight Laftanar Abubakar Alkali da Flight Laftanar Elijah Haruna Karatu.

    "Na yi matukar kaduwar da ba zan iya cewa komai ba bisa rasuwar wadannan matasa biyu wadanda suka sadaukar da rayuwar wajne bauta wa kasa," in ji Buhari.

    Ranar Talata ne jirgin rundunar sojin sama ta Najeriya ya yi hatsari inda duka jami’an biyu da ke cikinsa suka mutu.

    A cikin shekara guda da ta gabata dai, jiragen sojin saman Najeriya na yawan faduwa, lamarin da ke sanadiyar mutuwar jami’an sojin.

  15. Putin ya soke shirin kai hari a masana'antar karafa ta Azovstal a Mariupol

    A baya Shoigu ya shaida wa Putin cewa akwai fiye da mayakan Ukraine 2,000 a cikin masana'antar, wadanda suke cikin dakunan karkashin kasa.

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, A baya Shoigu ya shaida wa Putin cewa akwai fiye da mayakan Ukraine 2,000 a cikin masana'antar, wadanda suke cikin dakunan karkashin kasa.

    Shugaban Rasha Vladimir Putin ya umarci sojojinsa su fasa kai hari a masana'antar mulmula karafa ta Azovstal da ke birnin Mariupol da aka yi wa kawanya, yana mai cewa yana son a ci gaba kare ta.

    Mayakan Ukraine na karshe a birnin sun buya a masana'antar, kuma rahotanni sun akwai fararen-hula kusan 1,000 da ke cikin mawuyacin hali a can.

    Putin ya bayar da umarnin rufe masana'antar yayin tattaunawar da ya yi da Sergei Shoigu, ministan ma'aikatar tsaron kasar, wadda aka watsa a kafafen labarai.

    Ya taya kansa murna bisa nasarorin da suka samu a Mariupol bayan Shoigu ya yi ikirarin cewa dakarun Rasha sun kwace birnin.

    A baya Shoigu ya shaida wa Putin cewa akwai fiye da mayakan Ukraine 2,000 a cikin masana'antar, wadanda suke cikin dakunan karkashin kasa.

  16. Mutum uku sun mutu sakamakon rikicin shugabanci a Edo

    Shugaban 'yan sandan Najeriya

    Asalin hoton, Facebook/Nigeria Police Force

    Rahotanni daga jihar Edo da ke kudu maso kudancin Najeriya na cewa mutum uku sun mutu sakamakon rikicin da ke da alaka da neman shugabanci a karamar hukumar Uhunmwonde.

    Kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN, ya rawaito cewa lamarin ya faru ne a kauyen Uselu-Nahor ranar Laraba.

    Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Katongs Bello, ya tabbatar da aukuwar lamarin sai dai bai yi karin bayani ba.

    News Agency of Nigeria (NAN) ya rawaito cewa wasu 'yan bindiga ne suka kai hari kan mutanen, kuma daya daga cikin wadanda aka kashe jami'in tsaro ne da ke aiki a Ahor Kara.

    Mutanen suna karbar kudin fakin na motoci lokacin da 'yan bindigar suka kai mutu harin inda suka kashe mutum uku nan take.

    Bayanai sun nuna cewa rikicin yana da nasaba da rikicin shugabanci da ya ki ci ya ki cinyewa a kauyen.

  17. Barkanmu da warhaka

    Nasidi Adamu Yahaya ne yake muku barka da wannan rana ta Alhamis. Ku biyo mu domin sanin halin da duniya take ciki. Za mu fi mayar da hankali kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da makwabtansu, da ma wasu sassan duniya.