Mayaƙan ISWAP sun sace 'yan mata shida a garin Chibok

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Sallama

    Mun kawo karshen wannan yini na Laraba na rahotanni da bayanai daga Sashen Hausa na BBC.

    Sai ku biyo mu a gobe Alhamis domin samun wasu labarai da rahotanni.

    Bari mu bar ku da wannan hoton na kabilar Xingu ta kasar Brazil wanda rawa ne da kokawa mai suna Kuarap da 'yan kabilar ke yi dmin girmama wadanda suka mutu.

    A madadin abokan aikina, ni Sani Aliyu ke muku fatan alheri daga BBC Hausa.

    The Kuarup is a ritual of the Xingu Indigenous Brazilian to honour the illustrious dead - it is the farewell and closing of a mourning period.

    Asalin hoton, RICARDO TELES

  2. Cutar kyanda ta barke a yawancin yankunan kasar Laberiya

    Measles can be prevented by vaccination

    Asalin hoton, AFP

    Ma'aikatar lafiya ta Laberiya ta tabatar cewa an sami arkewar cutar kyanda a yankuna 14 cikin 15 na kasar.

    Babban jami'in kiwon lafiya Francis Kateh ya ce akwai rahotannin mace-mace a sanadin barkewar cutar, sai dai bai tabbatar da alakarsu da cutar kyanda ba.

    Yana jawabi ne a wani shirin gidan rediyo inda ya ce rashin isassun alluran riga-kafi ne ya haddasa matsalar.

    Ya kuma ce iyaye masu dama ne suka daina kai 'ya'yansu asibitoci domi a yi musu alluran riga-kafi tun bayan da annobar korona ta bayyana.

  3. Hotunan yadda ake kwashe mazauna birnin Mariupol

    Kamar yadda muka shafe makonni muna kawo muku rahotanni kan yakin Ukraine, a yau mazauna birnin Mariupol sun sami damar ficewa daga birnin ta wasu hanyoyin jin-kai da aka samar zuwa Zaporizhzhia da ke kudu maso gabashin Ukraine.

    Ga wasu hotunan yadda ake kwashe mutanen daga rahotann da Reuters suka wallafa.

    Mariupol evac

    Asalin hoton, Reuters

    Mariupol evac

    Asalin hoton, Reuters

    Mariupol evac

    Asalin hoton, Reuters

    Mariupol evac

    Asalin hoton, Reuters

    Mariupol evac

    Asalin hoton, Reuters

    Mariupol evac

    Asalin hoton, reu

  4. 'Yan bindiga sun sace mutum hudu 'yan gida daya a Abuja

    Gunman

    Asalin hoton, Getty Images

    Wasu mahara da ake kyautata zaton masu satar mutane domin kudin fansa ne sun afkawa al'ummar Shadadi skuma sun sace mutum hudu da sanyin safiyar Laraba a karamar hukumar Kuje ta Abuja babban birnin Najeriya.

    Wasu mazauna yank sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, cewa lamarin ya auku ne da misalin karfe 1 na dare bayan da suka rika harbin mai uwa da wabi domin tsorata mazauna yankin.

    Jaridar vanguard ta ruwaito cewa wani dan uwan wandanda aka sace na cewa maharan su goma sun kutsa cikin gidan bayan balla babbar kofar shiga ciki.

    Ya nemi jami'an tsaro da su taimaka wajen kwato 'yan uwan nasa, inda ya ce dukkansu 'yan uwan juna ne.

  5. Wimbledon 2022: An haramta wa ƴan wasan Rasha da Belarus shiga gasar

    Tennis

    Asalin hoton, Getty Images

    An haramta wa ƴan wasan Rasha da Belarus wasannin Tennis na gasar Wimbledon a bana saboda mamayar Ukraine

    Ɗan wasan na biyu a duniya Daniil Medvedev na Rasha da ta ɗaya a duniya ɓangaren mata Aryna Sabalenka su ne manyan ƴan wasan da matakin ya shafa

    Ƴan wasan an amince su shiga gasar ta Tennis amma ba tare da sun wakilci ƙasashensu ba.

    Za a gudanar da Wimbledon ne daga 27 ga watan Yuni zuwa 10 ga Yuli.

  6. Mayaƙan ISWAP sun sace 'yan mata shida a garin Chibok

    Rahotanni daga Jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya na cewa, mayaƙa masu iƙirarin jihadi na ƙungiyar ISWAP sun kai hari kauyen Yimir Mugza da ke yankin Chibok tare da kwashe wasu ‘yan mata shida.

    Lamarin na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan kammala addu’o’in cika shekara takwas da sace ‘yan matan Chibok da ƙungiyar Boko Haram ta yi a Jihar ta Borno.

    Latsa hoton ƙasa ku saurari rahoton Buhari Fagge:

    Bayanan sautiMayaƙn ISWAP sun sace 'yan mata shida a garin Chibok
  7. Ɗan takarar shugaban ƙasa a APC ya kaɗu da jin farashin fom ɗin takarar

    Adamu Garba

    Asalin hoton, @adamugarba

    Mai neman jam'iyyar APC ta tsayar da shi takarar shugaban ƙasa a Najeriya, Adamu Garba, ya kaɗu da jin farashin fom ɗin takararar da jam'iyyarsu ta saka na naira miliyan 100.

    A yau Laraba ne APC ta ce duk mai son ya tsaya takarar shugaban ƙasa sai ya biya kuɗin na-gani-ina-so naira miliyan 30 da kuma kuɗin fom naira miliyan 70.

    Adamu Garba ya bayyana kaɗuwarsa ne a shafinsa na Twitter jim kaɗan bayan sanar da farashin.

    "Miliyan 100 kuɗin fom. Lallai!," kamar yadda ya wallafa.

    Matashin da ke yawan amfani da shafukan zumunta ya kuma nemi 'yan uwansa matasa su fito su "yaƙi jakunkunan kuɗi".

    "Ba zai yiwu mu ci gaba da sayen ofisoshin gwamnati a Najeriya ba, muna buƙatar ƙwararrun shugabanni a (zaɓen) 2023," in ji shi.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  8. Rundunar sojan sama ta Najeriya ta bayyana sunayen sojojin da suka rasu a hatsarin jirgi

    Rundunar sojan sama ta Najeriya ta tabbatar cewa matuƙa jirginta biyu ne suka rasu a hatsarin da jirgin su ya yi a Jihar Kaduna da ke arewacin ƙasar.

    Jirgin ya faɗo ne a yammacin jiya Talata a wani sansanin sojan saman kuma duka mutum biyun da ke ciki ne suka rasu.

    Rundunar ta bayyana sunan dakarun nata da suna Laftanal Abubakar Muhammed Alkali da Laftanal Elijah Haruna Karatu.

    A yau Laraba Hafsan Sojan Sama na Najeriya Air Marshal Oladayo Amao ya kai ziyara wurin da hatsarin ya faru don jajanta wa dangin mutanen.

    Kakakin rundunar, Edward Gabkwet, ya ce za su yi "nutsattsen bincike don gano abin da ya haddasa hatsarin".

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  9. Babu masalaha wajen fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa a APC

    Buhari da Osinbajo

    Asalin hoton, State House

    Har yanzu dai game da zaɓukan fitar da gwani a jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, Majalisar Zartarwa ta ce za ta zaɓi ɗan takarar shugaban ƙasa ne ta hanyar jefa ƙuri'a.

    Sun cimma matsayar ce yayin taron majalisar karo na 11 a yau Laraba.

    Daga cikin waɗanda za su fafata a zaɓen sun haɗa da Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo, da jagoran APC Bola Tinubu, da Ministan Sufuri Rotimi Amaechi, da Gwamnan Ebonyi Dave Umahi, da Gwamnan Kogi Yahaya Bello.

  10. Labarai da dumi-dumi, APC za ta sayar da fom ɗin takarar shugaban ƙasa kan naira miliyan 100

    Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta sanar da sayar da fom ɗin takarar shugaban ƙasa kan naira miliyan 100 a babban zaɓe na 2023 mai zuwa.

    Wani jadawalin gudanar da zaɓukan fid da gwani da jam'iyyar ta fitar bayan taron Majalisar Zartarwarta a yau Laraba ya nuna cewa masu son yin takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin tutar APC za su biya kuɗin na-gani-ina-so naira miliyan 30, sai kuma kuɗin fom naira miliyan 70.

    Kazalika, masu son yin takarar gwamna za su lale naira miliyan 50, yayin da sanatoci za su biya miliyan 20.

    Masu fatan zama 'yan majalisar wakilai za su biya naira miliyan 10. Su kuma 'yan majalisar jiha miliyan biyu.

  11. 'Yan Ukraine fiye da miliyan biyar ne suka tsere daga ƙasar

    Ukraine

    Asalin hoton, Reuters

    Adadin 'yan Ukraine da suka tsere daga ƙasar sakamakon mamayar Rasha ya zarta miliyan biyar, a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD).

    Rasha ta afka wa Ukraine ranar 24 ga watan Fabarairun 2022.

  12. Rasha ta yi iƙirarin tarwatsa cibiyoyin sojan Ukraine 1,053 da tsakar dare

    Sojan Rasha

    Asalin hoton, Getty Images

    Ma'aikatar Tsaro ta Rasha ta yi iƙirarin cewa dakarun sojanta sun yi luguden wuta kan cibiyoyin soja na Ukraine 1,053 da tsakar daren da ya gabata.

    Cikin wata sanarwa a dandalin sadarwa na Telegram da safiyar yau, ma'aikatar ta ce ta lalata wuraren harba makaman atilare 106 sannan suka harbe jiragen Ukraine marasa matuƙa shida.

    Daga cikinsu, ta ƙara da cewa ta tarwatsa kadarorin soja 73 na Ukraine ɗin.

  13. An sako wasu 'yan Najeriya 13 da aka kama a Poland

    'Yan Najeriya

    Asalin hoton, NidCom

    Hukumomin ƙasar Poland sun sako 'yan Najeriya 13 cikin 19 da suke tsare da su a sansanonin tsare 'yan gudun hijira na ƙasar bayan yaƙi tsakanin Rasha da Ukraine ya kore su daga Ukraine ɗin.

    Hukumar 'Yan Najeriya Mazauna Ƙasashen Waje (NidCom) ta ce an sako mutanen ne bayan saka hannun da jekadan Najeriya a Poland, Manjo Janar Christian Ugwu, ya yi.

    An kama su ne bayan sun ƙi yarda su koma Najeriya lokacin da gwamnati ta ɗauki nauyin kwashe 'yan ƙasar daga ƙasashe maƙwabtan Ukraine, kamar Poland da Romania da Hungary, a cewar NidCom.

    A cewar jekadan, ɗaya daga cikin shidan da suka rage a hannun hukuma ya ce shi ɗan Kamaru ne saboda mahaifiyarsa 'yar can ce.

    "Abin baƙin ciki, sauran biyar ɗin sun nemi mafaka daga gwamnati...kuma ba za a sake su ba har sai gwamnatin Poland ta yanke shawara kan buƙatarsu ta amincewa ko kuma watsi da ita," in ji Janar Ugwu.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  14. Musulman Rohingya 160 sun gudu daga cibiyar tsare mutane a Malaysia

    Hukumomi a Malaysia na neman 'yan Rohingya sama da 160 da suka tsere daga wata cibiyar tsare mutane da ke arewacin ƙasar da sanyin safiya.

    Shugaban hukumar shige da fice ta Malaysia, Khairul Zaimee Daud, ya ce sama da mutum 500 ‘yan asalin kasar Myanmar ne suka yi nasarar tserewa amma daga baya aka sake kama yawancinsu.

    An ce an kashe mutum shida a lokacin da suke kokarin guduwa.

    Da yawansu sun isa Malaysia ne da kwale-kwale bayan doguwar tafiya ta ruwa kuma ana tura su wuraren da ake tsare da su wadanda kungiyoyin kare hakkin dan Adam ke cewa a cunkushe suke.

  15. Labarai da dumi-dumi, Buhari na halartar taron APC kan jadawalin zaɓen fid da gwani

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na halartar taron Majalisar Zartarwa na jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar da ke gudana yanzu haka.

    Ana gudanar da taron ne a otel ɗin Transcop Hilton da ke Abuja karon farko tun bayan da APC ta zaɓi sabbin shugabanninta a watan Maris.

    Ana sa ran 'yan majalisar wanda Buhari na ɗaya daga cikinsu, za su daddale jadawalin zaɓukan fid da gwani na jam'iyyar a matakin shugaban ƙasa da kuma na jihohi.

    Za mu kawo ƙarin bayani da zarar mun samu...

    • Zaɓen 2023: Ƴaƴan jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya na ficewa saboda zargin ɗauki-ɗora
    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  16. Ya kamata 'yan takara daga yankin Yarabawa su bar wa Igbo shugabancin Najeriya - Afenifere

    Tinubu da Osinbajo

    Asalin hoton, State House

    Shugaban majalisar tuntuɓa ta ƙabilar Yarabawa, Afenifere, Cif Ayo Adebanjo ya nemi masu neman takarar shugabancin Najeriya daga yankin kudu maso yamma da su haƙura.

    Shugaban ƙungiyar al'ummar Yarabawa ya ce ya kamata 'yan takarar yankin nasu kamar Bola Ahmed Tinubu da Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo su bar wa 'yan ƙabilar Igbo don samar da shugaban ƙasa na gaba a 2023.

    Jagoran ya bayyana hakan ne cikin wata hira da jaridar Punch ranar Talata, yana mai cewa "rashin adalci ne ɗan kudu maso yamma ya zama shugaban ƙasa bayan Olusegun Obasanjo ya mulki Najeriya shekara takwas, sannan kuma Yemi Osinbajo zai shekara takwas a muƙamin mataimakin shugaban ƙasa".

    Sai dai kuma dattijon mai shekara 94 ya ce "dole ne a kyautata ƙasar kafin Najeriya ta samu sabon shugaba".

    "A yanzu akwai ƙasar ma da suke so su shugabanta? Wajibi ne a samar da dunƙulalliyar ƙasa kafin ka yi maganar zaɓe," in ji shi.

  17. Ba zan bari wani ya karya doka a Najeriya ba - Buhari

    Buhari

    Asalin hoton, State House

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi kira ga 'yan kasar da su guji mutanen da ke hankoron ganin sun karya doka a kasar.

    Wata sanarwa da kakakin shugaban kasar Malam Garba Shehu ya aike wa manema labarai ta ambato Shugaba Buhari yana mai tabbatar wa 'yan kasar cewa ba zai kyale wani ya karya dokokin kasar ba.

    ''Muna da kasa, muna da albarkatun kasa da kuma mutane. Sai dai ban san dalilin da ya sa wasu ke da niyyar ba da kansu ba wajen lalata ƙasarsu ba," a cewar Buhari yayin buɗe baki da ya yi da gwamnoni da ministoci a Abuja ranar Talata.

    Shugaban ya sake jaddada cewa ƙaddamar da amfani da fasahar na'urar tantance masu kaɗa ƙuri'a "ba za ta bari wani ya yi iƙirarin samun miliyoyin ƙuri'u" yayin babban zaɓe na 2023 mai zuwa.

    Buhari

    Asalin hoton, State House

  18. Ukraine da Rasha sun cimma yarjejeniyar kwashe fararen hula daga Mariupol

    Ukraine

    Asalin hoton, Getty Images

    Ukraine ta ƙulla yarjejeniyar farko-farko da Rasha da zimmar samar wa fararen hula hanyoyin ficewa daga garin Mariupol da dakarun Rashar suka yi wa ƙawanya.

    Akasarin waɗanda za a kwashe ɗin mata ne da ƙananan yara a yau Laraba, a cewar mataimakiyar firaministan Ukraine.

    "Ganin halin tashin hankali da ake ciki a Mariupol, za mu mayar da hankalinmu a wannan fannin a yau," in ji Iryna Vereshchuk cikin wani saƙon Facebook.

    Kamar yadda muka sha ruwaitowa, mutane sun maƙale a garin mai tashar jirgin ruwa tsawon makonni ba tare da abinci ba ko ruwa ko magunguna.

    An sha zargin Rasha da kwashe mazauna birnin zuwa cikin ƙasarta ta hanyar tilasta musu.

  19. Bam ya kashe mutum biyar a Jihar Taraba

    Wani harin bam da aka kai a wata mashaya da ke Jihar Taraba a gabashin Najeriya ya kashe aƙalla mutum biyar.

    Wasu 19 sun samu munanan raunuka sakamakon fashewar wani abu a garin Iware.

    Shaidu sun ce an ɓoye bam ɗin ne a cikin wata jaka.

    Lamarin ya faru ne da tsakar ranar Talata yayin da mutane suka taru a majalisar da ake shan barasa.

    Rundunar 'yan sandan jihar sun shaida wa BBC cewa ɗaya daga cikin wadanda ake zargi da kai harin ya mutu, amma ba a sani ba ko ɗan ƙunar-bakin-wake ne.

  20. Assalamu Alaikum

    Kun shigo shafin rahotanni kai-tsaye na BBC Hausa tare da Umar Mikail a wannan hantsi na Laraba.

    Za mu kawo labarai game da abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, musamman a Najeriya da Nijar da maƙotansu.

    Kazalika, za mu sa ido kan halin da ake ciki a rikicin Ukraine.