Ronaldo ya sanar da ɗansa ya mutu

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya and Awwal Ahmad Janyau

  1. Nan za mu rufe wannan shafin sai kuma gobe

  2. Rasha ta ƙara matsa ƙaimi a gabashin Ukraine

    Ukraine ta ce Rasha ta kara matsa kaimi a gabacin kasar, wani abu da ke alamta fara kaddamar da sabbin ayyukan soji da Rashar ta sha alwashin yi.

    Sakataren majalisar tsaro ta Ukraine Oleksiy Danilov ya ce dakarun Rasha sun yi kokarin karya duk wani shingen tsaro da ke fagen daga a yankuna Donetsk da Luhansk da kuma Kharkiv.

    Tun farko d a yau Litinin mutane tara ne aka ruwaito sun hallaka sanadiyyar luguden wuta da Rasha ta yi kan birane da dama na Ukraine, wani abu da masana ke kallo a matsayin lanba na sabbin hare-haren da Rashar ke shirin kaddamarwa.

    Mutane bakwai aka tabbatar sun mutu a Lviv.

    Jami'an agajin gaggawa na ci gaba da bincike, kuma za su iya gano wasu da lamarin ya rutsa da su.

  3. Ronaldo ya sanar da mutuwar ɗansa

    Cristiano Ronaldo ya sanar da mutuwar ɗansa a cikin sanarwar da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta.

    "A cike da baƙin ciki muke sanar da mutuwar ɗanmu, Wannan babban baƙin ciki ne da iyaye za su ji."

    "Ƴar da aka haifa ce kawai ta ƙarfafa muna guiwa a wannan lokaci da muke cike da fata da farin ciki," in ji Ronaldo.

    A watan Oktoba Ronaldo da budurwarsa Rodriguez suka sanar da cewa za su haifi tagwaye.

    Dama Ronaldo yana da ƴaƴa huɗu, tagwaye Eva Maria da Mateo da ƙaramarsu Alana Martina da kuma babban ɗansa Cristiano Jr.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  4. ‘Yaƙin Ukraine zai dagula tattalin arzikin duniya’

    Ukraine

    Asalin hoton, Reuters

    Bankin duniya ya ce yakin da ake yi a Ukraine ya sanya hasashen da aka yi na ci gaban da tattalin arzikin daukacin duniya zai samu a wannan shekara, ya yi kasa.

    David Malpass ya ce kiyasin da bankin ya yi ya fadi daga ci gaba na kashi 4.1 cikin dari, zuwa kashi 3.2 cikin dari.

    Ya ce inda yakin zai fi yi wa illa sun hada da nahiyar Turaida tsakiyar Asia wanda ya hada da Ukraine da Rasha da kuma kasashe makwabtaka.

    Bankin ya yi hasashen tattalin arzikin zai iya tsukewa da kashi 4.1 cikin dari.

    Malpass ya ce bayanin ya fito ne bayan wani agaji da aka yi kiyasi, wanda ya kai na kudi dala biliyan 170 ga kasashen da lamarin ya shafa a cikin watanni 15.

  5. Rikicin addini ya barke a birnin Delhi tsakanin Musulmai da Hindu

    Mazauna yankin da akai rikicin sun kadu matuka

    Asalin hoton, Getty Images

    BBC ta kai ziyara yankin Jihangirpuri da ke birnin Delhi, bayan wani rikicin addini da ya faru, inda suka tayar da mazauna yankin cikin kaduwa da bacin rai.

    A kalla mutane tara ciki har da dan sanda suka mutu, a yamutsin da ya barke tsakanin masu amfani da harshen Bengali da Musulmai a ranar Asabar din karshen mako. Kuma har yanzu hankula ba su kwanta kamar yadda ake bukata ba.

    Ana ci gaba da zaman dardar a yankin, inda ganau suka shaidawa BBC cewa lamarin ya faru ne bayan daruruwan mabiya addinin Hindu sun shirya tattaki a wani bangare na bikin ranar haihuwar abin bautarsu Hanuman.

    Sun ratsa wuraren zaman Musulmai cikin kade-kade da raye-raye da wakokin batanci da tsokanar fada ga Musulmai.

    A daidai lokacin da suka isa kusa da wani masallaci ne, fusatattun musulmai suka taso inda akai ta ruwan duwatsu akansu.

    Kawo yanzu kura ta lafa sai zaman dardar, yayin da jami'an tsaro da hukumomin yankin ke cewa sun shawo kan matsalar.

  6. Putin ya zanta da shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas

    Putin da Abbas

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya zanta da shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas ta wayar tarho.

    Shugabannin sun tattauna batutuwa da suka shafi matsugunin Yahudawa da ke ƙara rurua rikici a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da kuma gabashin Kudus.

    Sun bayyana fatan wannan ba zai kai ga fito na fito ba tsakanin Falasdinawa da Isra’ila ba. Sun jaddada buƙatar sake farfaɗo da hawa teburin sulhu tsakanin Falasdinawa da Isra’ila.

    Shugaban sun tattauna yadda za su inganta hulɗar kasuwanci da tattalin arziki. Sannan Putin ya taya Mahmoud Abbas da Falasdinawa murnar azumin watan Ramadan.

  7. An jefa bama-bamai a majalisar dokokin Somalia

    Kungiyar Al-Shabab ta dade ta na kai munanan hare-hare a Somalia

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, Mayakan Al-Shabab

    An jefa wasu ma manyan bama-bamai a kan ginin majalisar dokokin Somalia, lamarin da ya raunata akalla mutane bakwai, ciki har da masu tsaron lafiyar 'yan majalisar.

    Kungiyar 'yan bindiga ta Al-Shabab ta ce ita ce ta kai harin, a daidai lokacin da 'yan majalisar ke tattaunawa kan ranar da za a sanya ta zaben shugabannin zaurukan majalisar biyu, wanda ake sa ran yi a cikin watan nan.

    Hakan dai zai iya kara jinkirta lokacin zaben sabon shugaban kasa. Akwai dai adawa mai zafi tsakanin 'yan siyasa na kasar, ciki har da na bangaren shugaban kasar mai ci Mohammed Abdullahi Farmajo.

    A wata sanarwa da Majlisar Dinkin Duniya ta fitr, ta jaddada goyon baya ga gwamnatin Somalia a kokarin da suke yi na tabbatar da an gudanar da zabe yadda ya dace.

  8. Wuta da lantarki sun katse a KwaZulu-Natal a Afirka ta Kudu

    Gwamnati na fuskantar matsain lambar sake gina hanyoyin da ambaliyar ta lalata.

    Asalin hoton, Reuters

    A wata sanarwa da ma'aikatar tsaron Afirka ta Kudu ta fitar, ta ce za su tura dakarunsu domin fadada aikin ceto, da kuma kwashe wadanda suka jikkata domin kai su tudun mun tsira.

    Haka kuma sojoji da ake aikin fanfo da na wutar lantarki, za su isa KwaZulu-Natal domin gyara wutar lantarki da hanyoyin ruwan sha da suka lalace, za kuma su kasance a can har na mako guda.

    Yawancin al'umma a yankunan KwaZulu-Natal na rayuwa babu wutar lantarki tun bayan afkuwar mummunar ambaliyar ruwan, babu hanyoyi da gadoji wadanda suka katse.

    Kusan makarantu da cibiyoyin lafiya 300 ambaliyar ta lalata. A lokacin ziyarar da ya kai yankin da ambaliyar ta shafa, shugaba Cyril Ramaphosa, ya ce gwamnati za ta tabbatar ta sake gina ayyukan ababen more rayuwar da ambaliyar ta lalata, da taimakawa iyalan da suka rasa komai na su a wannan ibtila'i.

  9. An dakatar da sarautar sabon Sardaunan Katsina

    Saddiq Musa Kaita

    Asalin hoton, Iyalan Kaita

    Masarautar Katsina da ke Arewacin Najeriya ta dakatar da sarautar Sardaunan Katsina da aka bai wa Saddiq Musa Kaita.

    Wata sanarwa da Alhaji Sule Mamman Dee, Sarkin Tsaftan Katsina ya sanya wa hannu ta ce nan gaba za a tuntube shi domin yi masa karin bayani.

    "Bisa ga takardar da aka ba ka ta ranar 16/4/2022 wadda aka ba ka Sarautar Sardaunan Katsina, Majalisar Mai martaba Sarkin Katsina ta umarce ni da na rubuto na sanar da kai cewa ta dakatar da Sarautar.

    Komi ke nan za a tuntube ka nan gaba," in ji sanarwar.

    Tun da farko farko Sarkin Katsina ya tabbatar masa da sarautar ne a cikin wata takarda mai ɗauke da sa hannunsa a ranar Asabar 16 ga watan Afrilu.

    "Na amince da ba ka Sarautar Sardaunan Katsina kamar yadda ka nema," kamar yadda Sarkin Katsina ya bayyana a cikin takardar.

    Sanarwar ta ce nan gaba za a sanar da ranar bikin naɗin nasa.

    Saddik jika ne ta bangaren uba ga sarkin Fadan Katsina Isma’ila Damale wanda shi kuma ɗa ne ga Wazirin Katsina na farko Haruna Kaita.

    Haka kuma ta bangaren uwa jika ne ga Makaman Katsina Marigayi Tukur Idris Nadabo hakimin Bakori.

    A kwanakin baya ne aka ba Ibrahim Ida sarautar Wazirin Katsina wanda a baya shi ne Sardaunan Katsina.

    Wannan na zuwa ne bayan ajiye sarautar waziri da Alhaji Sani Lugga ya yi saboda wasu dalilai.

    Takarda

    Asalin hoton, Katsina Emirate Council

  10. Putin ya ce Kasashen Yamma sun cuci kansu da suka sanya wa kasarsa takunkumai

    Putin

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ce Kasashen Yamma sun cuci kansu da suka sanya takunkumai a kan kasarsa.

    Ya ce sanya takunkuman ya sa "tattalin arzikin Kasashen Yamma ya tabarbare".

    Da yake bayani kan halin da tattalin arzikin kasar yake ciki, Putin ya ce hauhawar farashin kayayyaki tana dawowa daidai kuma masu son sayen kayayyaki suna karuwa, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Reuters ya rawaito.

    Kasashen Yamma sun sanya jerin takunkumai a kan Rasha bayan da ta mamaye Ukraine.

    Tun da fari, Putin ya shaida wa jami'an gwamnati ta na'urar bidiyo cewa Rasha za ta yi amfani da kasafin kudinta wajen tallafa wa tattalin arzikinta.

  11. Gwamnatin Lagos ta rufe makarantun Chrisland bisa zargin lalata tsakanin dalibai

    Makarantar Chrisland

    Asalin hoton, OTHER

    Gwamnatin Lagos da ke Kudancin Najeriya ta sanar da rufe dukkan makarantun Chrisland da ke Jihar bisa zargin da ake yi wa wani dalibi na yi wa wata daliba fyade.

    Lamarin ya faru ne a birnin Dubai da ke Hadaddiyar Daular Larabawa yayin da suka je ziyarar bude-ido.

    A wata sanarwa da Hukumar Yaki da Lalata ta Jihar ta fitar dazun nan, gwamnatin ta ce tana gudanar da bincike game da zargin lalata da dalibar.

    "Hankalin gwamnatin Jihar Lagos ya kai kan labarin zargin lalata da ya hada da wasu daliban makarantar Chrisland da ya faru Dubai da ke Hadaddiyar Daular Larabawa. Yana da muhimmaci a sani cewa hukumomin da lamarin ya shafa, kamar su Ma'aikatar Ilimi, Ofishin Kula da Ingancin Ilimi, Ma'aikatar Matasa, Ma'aikatar Shari'a, da Kwamishinan 'yan sanda suna bincike kan lamarin," in ji sanarwar.

    Lamarin dai ya ya hankalin 'yan Najeriya bayan da aka ga bidiyon daliban suna lalata a dakin otal din da suka sauka a Dubai.

  12. Hotunan barnar da makamai masu-linzamin Rasha suka yi a harin Lviv

    Kamar yadda muka ba ku labari, mutum bakwai sun mutu sannan da dama suka jikkata bayan wasu makamai masu-linzami da Rasha ta harba a birikokin sojin Ukraineda ke Lviv.

    Yanzu mun samu hotunan abubuwan da suka faru:

    Ma'aikatan kashe gobara suna aiki a ginin da makamai masu-linzamin Rasha  suka lalata a Lviv

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Ma'aikatan kashe gobara suna aiki a gine-ginen da makamai masu-linzamin Rasha suka lalata a Lviv
    Hayaki ya turnike sararin samaniyar Lviv bayan Rasha ta harba makamai masu-linzami a birnin da sanyin safiya

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Hayaki ya turnike sararin samaniyar Lviv bayan Rasha ta harba makamai masu-linzami a birnin da sanyin safiya
    Harin ya lalata gidaje da dama a wajen birnin Lviv

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Harin ya lalata gidaje da dama a wajen birnin Lviv
    Ma'aikatan kashe gobara suna ta fafutikar kashe wutar da ta tashi a wani gida da fararen-hula suke zama wanda makamai masu-linzamin Rasha suka lalata

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Ma'aikatan kashe gobara suna ta fafutikar kashe wutar da ta tashi a wani gida da fararen-hula suke zama wanda makamai masu-linzamin Rasha suka lalata
  13. Bayanan baya-bayan nan kan rikicin Ukraine

    Wani sojan Ukraine

    Asalin hoton, Reuters

    Ga bayanan baya-bayan nan game da yakin da ake yi a Ukraine:

    • Mutum bakwai sun mutu bayan rokoki hudu sun fada kan wasu wuraren da soji suke a Lviv da ke yammacin Ukraine, a cewar jami'ai
    • Hakan na faruwa ne yayin da dakarun Rasha suka yi ruwan bam-bamai a birane dama na Ukraine sannan an yi karar abubuwan fashewa a babban birnin kasar Kyiv
    • Kafofin watsa labaran Rasha sun bayar da rahoton cewa dakarun tsaron kasar sun kai hari kan wurare 315 a Ukraine jiya da daddare.
    • An harbe fararen-hula hudu sanna aka jikkata guda daya a yayin da suke kokarin tserewa daga garin Kreminna na gabashin kasar, a cewar jami'an kasar Ukraine
    • Ba za a samu damar kwashe fararen-hula daga Ukraine ba, kwana na biyu a jere bayan jami'an kasar da na Rasha sun gaza amincewa kan batun
  14. Yadda zafi ya sa Kanawa rububin kankara da neman inuwa a Ramadan

    Bayanan bidiyo, Ramadan: Yadda zafi ya sa Kanawa rububin kankara da neman inuwa

    Danna hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

    Wasu mutane a birnin Kano da ke arewacin Najeriya sun shiga rububin neman kankara domin shan ruwan sanyi a wannan yanayi na zafi.

    Mutanen, wadanda suke azumin watan Ramadana cikin tsananin zafi, sun shaida wa BBC cewa kankara ta yi matukar tsada kuma duk da haka ba a samunta a kwanciyar hankali.

  15. Mutane fiye da 60 sun bata bayan ambaliyar ruwa a Afirka ta Kudu

    Wani ma'aikacin agaji

    Asalin hoton, Getty Images

    Ana ci gaba da neman mutane 63 da suka bata bayan ambaliyar ruwan da aka yi a yankin KwaZulu-Natal na kasar Afirka ta Kudu a makon jiya.

    Mutane fiye da 440 ne suka mutu sanadin ambaliyar ruwan, ciki har da ma'aikatan agajin gaggawa biyu.

    Mamakon ruwan sama da ya cika koguna yankin da zaftarewar kasa ne suka yi awon-gaba da mutanen.

    Gwamnati ta ayyana KwaZulu-Natal a matsayin yankin da ke fama da bala'i bayan jami'a sun bayyana cewa ambaliyar ruwan na cikin mafi muni da ta faru a yankin a tsawon tarihi.

    Firimiyan KwaZulu-Natal Sihle Zikalala ya ce ambaliyar ruwan ta rusa kusan gidaje 4,000 sannan ta lalata gidaje fiye da 8,000, galibi a birnin Durban da ke kusa da tashar jiragen ruwa da ma garuruwan da ke kusa da shi.

  16. Labarai da dumi-dumi, 'Rasha ta harba makamai masu-linzami hudu a Lviv'

    Gwamnan lardin Lviv, Makysm Kozytskyi, ya yi ikirarin cewa Rasha ta harba makamai masu-linzami hudu a lardin.

    A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Telegram, ya ce "bayanan farko" da suka samu ne suka tabbatar da hakan.

    Kozytskyi ya ce lamarin ya yi sanadin mutuwar mutum shida da jikkata mutum 11.

    Ya zargi Rasha da kisan kare-dangi.

    Ya bukaci mazauna lardin su "zauna a gidajenku".

    Wakilin BBC, Toby Luckhurst, ya ce sun ji karar manyan fashewa akalla biyar a yammacin Lviv, birnin da ke kan iyakar Ukraine da Poland.

  17. Yadda 'yan Najeriya suka yi bikin Easter cikin tsadar rayuwa

    Bayanan sautiYadda 'yan Najeriya suka yi bikin Easter cikin tsadar rayuwa

    Danna hoton da ke sama domin sauraren rahoton:

    Wasu 'yan Najeriya sun bayyana suka yi bikin Easter cikin mawuyacin hali na tsadar rayuwa.

    A tattaunawarsu da BBC, wasu Kiristoci sun bayyana cewa a wannan lokaci, tsananin tsadar rayuwa da rashin kudi sun tilasta musu yin bikin a yanayi maras dadi.

    Sai dai sun ce sun gode wa Allah da ya bar su da rai da lafiya.

  18. Saudiyya ta yi tir da masu kona AlKur'ani

    An yi arangama tsakanin 'yan sanda da masu zanga-zangar kyamar kona AlKur'ani

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, An yi arangama tsakanin 'yan sanda da masu zanga-zangar kyamar kona AlKur'ani

    Gwamnatin Saudiyya ta yi tir da masu tsattsauran ra'ayi na kasar Sweden da suka kona Alkur'ani mai tsarki da "gangan" tana mai cewa sun yi hakan ne domin su takali fada da kuma hasala Musulmai.

    A wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, Ma'aikatar Harkokin Wajen kasar, ta bayyana muhimmancin tattaunawa da amincewa da juna da kuma zaman tare.

    Sanarwar ta kuma jaddada bukatar kyamar tsattsauran ra'ayi da kiyayya. Saudiyya ta kuma bayyana bukatar kawar da dukkan arangama tsakanin mabiya mabambantan addinai a wurare masu tsarki.

    Mutane uku sun jikkata babban birnin Norrkoping na kasar Sweden bayan 'yan sanda sun harba musu alburusai lokacin wata taho-mu-gama tsakaninsu bayan kona Alkur'ani, lamarin da ya haifar da zanga-zanga a garuruwa da dama na kasar a karshen mako lokacin bikin Easter.

  19. Barkanmu da hantsi

    Nasidi Adamu Yahaya ne tare da ku a wannan rana ta Litinin.

    Ku biyo mu domin sanin halin da duniya take ciki.

    Za mu fi mayar da hankali kan abubuwan da ke wakana a Najeriya da Nijar da makwabtansu, da ma wasu sassan duniya.