'Yan sandan Isra'ila sun raunata Falasɗinawa 19 a masallacin Ƙudus

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.

Rahoto kai-tsaye

Awwal Ahmad Janyau and Umar Mikail

  1. Mu kwana lafiya

    Ƙarshen rahotannin kenan a wannan shafi. Ku duba ƙasa don karanta rahotannin da muka wallafa a yau Lahadi.

    Umar Mikail ke muku fatan za a yi sahur lafiya.

  2. NDLEA ta kama masu safarar hodar ibilis a Abuja, Legas, Fatakwal

    Koken

    Asalin hoton, NDLEA

    Hukumar yaƙi da miyagun ƙwayoyi a Najeriya (NDLEA) ta ce ta kama wasu ƙunshin hodar ibilis ko kuma koken da aka yi safarar ta ta filayen jiragen sama na Abuja da Fatakwal da Legas.

    Hukumar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta fitar a yau Lahadi, inda kakakinta Femi Babafemi yake cewa sun kama mutum bakwai da ake zargi da hulɗa da wata ƙungiyar 'yan ƙwaya a Brazil.

    Ta ce an shigar da koken ɗin ne ta hanyar da ba a saba gani ba - inda aka ɓoye ta a cikin man goge baki da tufafi.

    An kama mutum biyar a filin jirgi na Fatakwal ranar Asabar, 9 ga watan Afrilu, yayin da aka kama sauran a Abuja da Legas.

  3. 'Yan sandan Isra'ila sun raunata Falasɗinawa 19 a masallacin Ƙudus

    Falasinu

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar agajin gaggawa ta Falasdinu ta ce an jikkata masu zanga-zanga 19 a hatsaniyar da ta faru tsakaninsu da 'yan sandan Isra'ila a bakin masallacin Al-aƙsa da ke birnin Kudus.

    'Yan sandan Isra'ila sun ce sun shiga harabar masallacin ne domin korar masu zanga-zanga da kuma dawo da doka da oda.

    Falasdinawan sun ce 'yan sandan sun hana su shiga masallacin bayan idar da sallar asuba saboda bai wa Yahudawa damar shiga ziyara.

    Wani wanda abin ya faru a kan idansa ya ce "sun rika harba harsashin roba kan masu bautar da ke cikin masallaci".

    A ranar Juma'a ma, sai da 'yan sanda suka jikkata sama da Falasdinawa 150 a rikicin da ya faru a masallacin.

  4. Ukraine ba ta da niyyar miƙa wa Rasha yankin Donbas - Zelensky

    Zelensky

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce ƙasarsa na ci gaba da fafatawa a yankin Donbas kuma "ba ta da niyyar saranda".

    Cikin wata hira da ya yi da kafar talabijin ta CNN, Zelensky ya yi watsi da batun sakar wa Rasha yankin Donbas da wasu yankunan gabashin ƙasar a matsayin sharaɗin kawo ƙarshen yaƙin.

    Ya ƙara da cewa: "Ukraine da mutanenta sun faɗa ƙarara. Ba mu mamaye ƙasar kowa ba kuma mu ma ba za a mamaye tamu ba."

    Duk lokacin da Shugaban Rasha Putin ya yi magana kan ƙwace yankin Donbas, yana magana ne kan tsohon garin da ake samar da ƙarafa da gawayin kwal na Ukraine.

    Abin da yake nufi takamaimai shi ne ɗaukacin yankin gabashi mai girma na Luhansk da Donetsk wanda ya fara tun daga ƙarshen Mariupol daga kudu har zuwa kan iyaka daga arewaci.

  5. An kashe mutum ɗaya yayin da 'yan sanda suka ceto mutum huɗu a Kaduna

    'Yan sandan Najeriya

    Asalin hoton, NG Police

    Mutum ɗaya ya rasu sakamakon harin da 'yan bindiga suka kai a Ƙaramar Hukumar Sabon Gari da ke Jihar Kaduna.

    An bayyana sunan wanda aka kashe da Yarima Mohammed mazaunin Kufena, wanda ya yi wa maharan turjiya lokacin da suka nemi yin garkuwa da shi.

    Wata sanarwar 'yan sanda da kafofin yaɗa labarai suka ruwaito ta ce jami'an tsaro sun bi sawun maharan tare da ceto mutum huɗu.

    Kakakin rundunar a Kaduna, Mohammed Jalige, ya ce maharan sun far wa garin Gabari da ke yankin Samaru na Sabon Gari cikin kakin soja ɗauke da manyan makamai, inda suka dinga harbi kan mai tsautsayi kuma suka yi awon gaba da mutum huɗu.

    A cewarsa, rundunar ta yi nasarar ceto mutum biyu daga cikin mutanen bayan dakarunta sun yi wa 'yan fashin kwanton-ɓauna.

    Irin wannan salon dakarun suka bi a ƙauyen Gwada inda suka yi nasarar ceto sauran mutum biyun da aka sace tare da taimakon mayaƙan sa-kai, waɗanda suka far wa 'yan bindigar.

  6. Iraƙi ta kira jekadanta na Sweden kan adawa da ƙona Al Kur’ani

    Iraƙi ta kira jekadanta a Sweden domin adawa da zargin ƙona Al Kur’ani mai tsarki a ƙasar.

    Sanarwar daga ma’aikatar harakokin waje da kafar Shafaq ta wallafa a ranar Lahadi, gwamnatin Iraƙi ta ce kona Al Kur’ani abu ne mai tsanani kan alaƙar Sweden da al’ummar Musulmi baki ɗaya, musulmi a ƙasashen larabawa da Musulmin Turai.

    An shafe kwana uku ana zanga-zanga a Sweden kan adawa da masu tsauttsauran ra’ayi da ke ƙyamar baƙi da suka kona Al Kur’ani tare da barazanar ci gaba da ƙonewa.

    Zanga-zangar ta ɓarke a Malmo a ranar Asabar bayan gangamin shugaban jam’iyyar masu kyamar Musulmi Rasmus Paludan.

    An ƙone motoci kuma masu znaga-zanga sun ta jifar ƴan sanda da duwatsu.

    Zanga-zanga a Sweden

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Zanga-zangar ta ɓarke a Malmo a ranar Asabar bayan gangamin shugaban jam’iyyar masu kyamar Musulmi Rasmus Paludan.
  7. Abin da Fafaroma ya ce kan rikicin birnin Kudus

    Fafaroma Francis ya yi kiran samar da "yanci" a wuraren ibadah a birnin Kudus, bayan artabu tsakanin sojojin Isra’ila da Falasdinawa cikin sa’o’i 48 da ya yi sanadin jikkatar mutane da dama da dama.

    "Ina fatan ƴan Isra'ila da Falasdinawa da dukkanin mazauna wurare masu tsarki za su ɗanɗana zaman lafiya, su zauna lafiya kuma su shiga wuraren ibada ba tare da wani shamaki ba cikin mutunta ƴancin kowa," kamar yadda Fafaroma ya bayyana a bikin Easter.

    Fafaroma

    Asalin hoton, Reuters

  8. An ba Saddiq Musa Kaita Sarautar Sardaunan Katsina

    Saddiq Musa Kaita

    Sarkin Katsina Dr Abdulmuninu Kabir Usman ya tabbatar wa Saddiq Musa Kaita da sarautar Sardaunan Katsina.

    Sarkin Katsina ya tabbatar masa da sarautar ne a cikin wata takarda mai ɗauke da sa hannunsa a ranar Asabar 16 ga watan Afrilu.

    "Na amince da ba ka Sarautar Sardaunan Katsina kamar yadda ka nema," kamar yadda Sarkin Katsina ya bayyana a cikin takardar.

    Sanarwar ta ce nan gaba za a sanar da ranar bikin naɗin nasa.

    Saddik jika ne ta bangaren uba ga sarkin Fadan Katsina Isma’ila Damale wanda shi kuma ɗa ne ga Wazirin Katsina na farko Haruna Kaita.

    Haka kuma ta bangaren uwa jika ne ga Makaman Katsina Marigayi Tukur Idris Nadabo hakimin Bakori.

    A kwanakin baya ne aka ba Ibrahim Ida sarautar Wazirin Katsina wanda a baya shi ne Sardaunan Katsina.

    Wannan na zuwa ne bayan ajiye sarautar waziri da Alhaji Sani Lugga ya yi saboda wasu dalilai.

    Katsina
  9. Gane Mini Hanya: Matsalolin Ilimin Firamare a Najeriya

    Batun ilimin firamare wani sha'ani ne da kusan za a iya cewa yana ci wa dukkannin jihohi a Najeriya tuwo a kwarya.

    Ma fi yawancin lokuta matsalolin na taimaka wa wajen dakile aniyar iyaye na ganin 'ya'yansu sun yi karatun zamani.

    Matsaloli kama daga rashin isassun azuzuwa kuma masu inganci zuwa matsalar karanci da rashin ingancin malamai ne manya-manyan matsalolin da suka zama tamkar sun gagari gwamnatoci.

    A cikin shiri na musamman wanda gidauniyar MacArthur ta dauki nauyi, mun yi Nazari kan yanayin makarantu da walwalar malamai, da kuma sauran bukatun fannin ilimi a jihar Adamawa.

  10. Rundunar sojan ruwan Najeriya ta ce ta kama ɗanyen mai da dama na sata

    Rundunar Sojin ruwan Najeriya

    Asalin hoton, @NigerianNavy

    Rundunar Sojin ruwan Najeriya ta ce rundunarta mai yaƙi satar ɗanyen mai ta yi nasarar kamawa da ƙwace jiragen ruwa na kwale-kwale da ke ɗauke da ɗanyen man Najeriya da aka sace.

    Rundunar sojin ruwan ta ce rundunar Dakatar da Ɓarawo mai farautar ɓarayin wadda aka ƙaddamar a farkon Afrilu ta samu nasarori da dama na kama ɓarayin mai a yankin kudu maso kudancin Najeriya mai arzikin fetir.

    Sanarwar da rundunar ta fitar ranar Lahadi ta bayyana nasarorin da rundunar ta samu.

    Rundunar ta ce jirgin ruwanta na Pathfinder ya kama wasu jiragen ruwa guda tara na Cotonou da ke ɗauke da man dizel a yankin Andoki da Bille a ranar 5 ga Afrilu. Rundunar ta kuma kama man tataccen mai wanda adadinsa ba a tantance ba a yankin Bonny.

    An kuma gano wata rijiyar mai da cibiyar da ake tace man girki a Ketoru.Rundunar ta kuma kama wani jirgi ɗauke da ɗanyen mai lita 520,000 da ake zargin sato shi aka yi a yankin Warri.

    Rundunar ta ce ta kama tataccen mai na dizel lita 6,000 a yankin Yanagoa na jihar Bayelsa da kuma wasu motocin dakon ko wacce ɗauke da lita 35,000. Ta kuma kama ɗanyen mai lita 50,000 da lita 150,000 da lita 30,000 da ake zargin na sata ne a yankin Warri a ranar 15 ga watan Afrilu.

  11. Koriya ta Arewa ta yi gwajin wani sabon makami

    Kafofin yada labarai na gwamnatin Koriya ta Arewa sun sanar da cewa, kasar ta yi nasarar gwajin wani sabon makami, wanda ta ce zai inganta karfin sojin kasar.

    Masana sun ce sun yi imanin cewa an ƙera sabon nau'in makami mai linzamin ne domin ɗaukar ƙananan makaman Nukiliya.

    Sojojin Koriya ta Kudu sun tabbatar da cewa an harba makamai masu linzami biyu daga Arewa zuwa cikin teku a daren Asabar.

    Masu aiko da rahotanni sun ce mai yiwuwa an yi gwajin ne dai-dai da zagayowar ranar da aka haifi Kim Il-sung, mutumin da ya kafa Koriya Ta Arewar.

  12. Yadda aka yi bikin Easter a sassan duniya

    Fafaroma Francis

    Asalin hoton, Getty Images

    Kiristoci a faɗin duniya na gudanar da bikin Easter, ranar da mabiya addinin uka yi imanin cewa Yesu ya tashi zuwa sama, bayan da aka gicciye shi ranar Juma'a.

    Fafaroma ya jagoranci addu’oin Easter a na ɗinbim mabiya a dandalin St. Peter a fadar Vatican

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Fafaroma ya jagoranci addu’oin Easter a na ɗinbim mabiya a dandalin St. Peter a fadar Vatican
    Mabiya ɗarikar Katolika a Los Angeles a Amurka na kwaikwayon yadda aka gicciye Yesu a ranar Juma’a

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Mabiya ɗarikar Katolika a Los Angeles a Amurka na kwaikwayon yadda aka gicciye Yesu
    An gudanar da wannan gicciyewar ne a ranar Juma’a a sassan duniya kafin ranar Lahadi ta Easter

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, An gudanar da wannan gicciyewar ne a ranar Juma’a a sassan duniya kafin ranar Lahadi ta Easter
    Yadda Kiristoci mabiya ɗarikar Katolika a Iraƙi suka yi bikin Easter a Cocin Al-Tahera da ke lardin Hamdaniyah Nineye arewacin Iraƙi

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Yadda Kiristoci mabiya ɗarikar Katolika a Iraƙi suka yi bikin Easter a Cocin Al-Tahera da ke lardin Hamdaniyah Nineye arewacin Iraƙi
    Wani Limamin Coci na bayar da sadaka mai tsarki ga mabiya addinin Kirista a ranar addu’o’in Easter a cocin St. Anthonys da ke Colombo Sri Lanka

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Wani Limamin Coci na bayar da sadaka mai tsarki ga mabiya addinin Kirista a ranar addu’o’in Easter a cocin St. Anthonys da ke Colombo Sri Lanka
    An gudanar da zanga-zanga domin tunawa da harin bom da aka kai ranar Easter a 2019 a Coci guda uku da otel uku, harin da ya kashe mutum 300 a Colombo ƙasar Sri Lanka

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, An gudanar da zanga-zanga domin tunawa da harin bom da aka kai ranar Easter a 2019 a Coci guda uku da otel uku, harin da ya kashe mutum 300 a Colombo ƙasar Sri Lanka
    Wasu mabiya Kirista sun riƙe wuta lokacin addu’o’in Easter a tsakiyar dare a birnin Nairobi na Kenya

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Wasu mabiya Kirista sun riƙe wuta lokacin addu’o’in Easter a tsakiyar dare a birnin Nairobi na Kenya
    Mabiya addinin Kirista na addu’oin Easter a Cocin Cathedral a Lahore

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Mabiya addinin Kirista na addu’oin Easter a Cocin Cathedral a Lahore
  13. Yau shekara biyu da rasuwar Malam Abba Kyari

    Abba Kyari

    Asalin hoton, Twitter

    Shekara biyu kenan cif da rasuwar shugaban ma'aikatan fadar shugaba Buhari, Malam Abba Kyari.

    Abba Kyari ya rasu ne a ranar 17 ga watan Afrilun 2020 bayan kamuwa da cutar korona.

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana marigayi Abba Kyari a matsayin babban amininsa na hakika kuma mai kishin kasa.

    Buhari ya ce Abba Kyari amininsa ne tsawon shekaru 42 suna tare kafin daga baya ya zama shugaban ma'aikata a fadarsa.

    Kuma kafin rasuwarsa, Abba Kyari ya sa suka musamman masu zargin cewa ya yi babakere a gwamnatin Buhari, sai abin da ya ce ake yi.

    Malam Abba Kyari ya rasu ne yana da shekara 67 a duniya bayan ya yi fama da cutar korona.

  14. An ba Musulmi wa’adi su cire lasifika a Masallatai a India

    Indiya

    Asalin hoton, Other

    Shugaban Jam’iyyar Maharashtra Navnirman Sena (MNS) Raj Thackeray ya ce ba ya son tashin hankali a Maharashtra. Don haka ya ce Musulmi su fahimci babu addinin da ya fi ƙarfin doka.

    Ya ce buƙatarsa ta cire lasifika daga Masallatai ba ya nuna adawarsa ba ne ga Sallar da Musulmi suke yi, kuma haka jam’iyyarsa ba ta son tashin hankali.

    An ba Musulmi wa’adi su cire lasifika a Masallatai a Maharashtra zuwa ranar 2 ga watan Mayu. “Zuwa 3 ga Mayu za a ga abin ya kamata a yi.”

    “Idan har ba a cire Lasifika a Masallatai ba zuwa 3 ga Mayu, to ma’aikatan MNS za su yi amfani da lasifika suna rera Hanuman Chalisa a Masallatan.

    Rikicin addini a Indiya tsakanin Musulmi da Hindu na ƙara ƙamari, lamarin ya munana a cikin 'yan shekarun nan, sakamakon yadda 'yan Indiya ke jifan juna da kalaman kiyayya.

  15. Gargaɗin Rasha ga dakarun Ukraine a Mariupol

    Rasha ta shaidawa sojojin Ukraine na karshe da suka rage a birnin Mariupol da take yi wa ruwan bama-bamai cewa za su tsira da rayukansu idan suka mika wuya cikin sa'o'i masu zuwa.

    Moscow ta ce dakarunta sun kawar da duk wasu sojojin turjiya daga birnin, baya ga share baraguzai daga hanya.

    Sanarwar da ma'aikatar tsaron kasar ta fitar ta ce ta yi tayin mika makaman ne a wani mataki na nuna dattaku da mutunta rayuka.

    A ranar Asabar ne shugaba Zelensky ya yi gargadin cewa za a kawo karshen tattaunawar zaman lafiya idan Rasha ta kashe sauran sojojin.

    Ya ce halin da ake ciki a Moriupol na ci gaba da kazancewa, abun da Rasha ta aikata da gan-gan, kuma take son ci gaba da yi kenan.

    Magajin garin Mariupol ya yi kiyasin cewa akalla fararen hula dubu ashirin ne suka mutu a tsawon makonni na kai hare-hare ba kakkautawa.

  16. Maraba

    Muna maku maraba da kasansewa da mu a wannan shafin da muke kawo labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a sassan duniya