Sai da safenku
Nan muka zo ƙarshen rahotannin a wannan shafin. Mu haɗu da ku gobe Asabar don samun sabbi kai-tsaye.
Umar Mikail ke cewa a yi sahur lafiya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.
Nasidi Adamu Yahaya and Umar Mikail
Nan muka zo ƙarshen rahotannin a wannan shafin. Mu haɗu da ku gobe Asabar don samun sabbi kai-tsaye.
Umar Mikail ke cewa a yi sahur lafiya.

Asalin hoton, Reuters
Hukumomin Ukraine sun ce suna ci gaba da zaƙulo gawarwakin mutane a garuruwan da ke kusa da birnin Kyiv fiye da mako ɗaya bayan sojojin Rasha sun fice daga yankunan.
"Abin takaici, ina sanar muku cewa mun samu gawar fararen hula 900 kuma mun miƙa wa ƙwararru," a cewar shugaban 'yan sanda na yankin Kiyv Andriy Nebytov.
Nebytov ya ce fiye da mutum 350 daga cikinsu an gano su ne a garin Bucha - inda ake zargin Rasha da aikata laifukan yaƙi. Sai dai Rashar ta musanta zargin.
Ana ci gaba da tona ɓaraguzai a Borodyanka da Makarov "kuma za a sake samun gawarwakin mutane a ƙarƙashinsu," in ji shi.

Asalin hoton, APC
Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta sanar da cewa Kwamatin Gudanarwa na Ƙasa na jam'iyyar zai gudanar da taron bayan zaɓen shugabanni irinsa na farko ranar Laraba mai zuwa.
Sakataren Yaɗa Labarai na APC Felix Morka ne ya sanar da matakin cikin wata sanarwa ranar Juma'a, yana mai cewa na gaggawa ne.
Sanarwar ta ce taron zai gudana a oteli ɗin Transcorp Hilton da ke Abuja babban birnin ƙasar da misalin ƙarfe 10:00 na safe.
"Dukkan 'yan Kwamatin Gudanarwa na Ƙasa (NEC) su sani cewa an gayyace su ne bisa tanadin sashe na 12.3 na Kundin Tsarin Mulkin APC," a cewar sanarwar.
A ƙarshen watan Maris ne APC ta gudanar da babban taronta na ƙasa, inda ta zaɓi Sanata Abdullahi Adamu a matsayin shugaba.

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Rasha kori jakadun ƙasashen Turai 18 daga ƙasar, inda ta tuɓe musu rigar kariya (persona non grata).
"Ma'aikatan za su fice daga Tarayyar Rasha nan da ɗan lokaci," a cewar ma'aikatar harkokin waje cikin wata sanarwa.
Da take mayar da martani, ƙungiyar Tarayyar Turai ta EU ta yi wadai da "matakin maras dalili", tana mai cewa "ba wani abu ne ya sa aka ɗauki umarnin ba illa ramuwar gayya".
Ƙasashen EU sun kori gomman jakadun Rasha cikin watan da ya wuce.
A ƙarshen watan Maris, ƙasashen Ireland, da Belgium, da Netherlands sun fitar da sanarwar haɗin gwiwa ta korar ma'aikatan jakadancin Rasha 43 saboda zarginsu da aikata leƙen asiri.
A ranar 5 ga watan Afrilu kuma, EU ta umarci Rashawa 19 su fice daga Belgium sakamakon "shiga wasu ayyuka da suka saɓa wa ayyukansu a hukumance".

Asalin hoton, Thinkstock
Wani tsohon mamba a majalisar manyan malaman Saudiyya, Dr. Qais Bin Muhammad Al-Sheikh Mubarak, ya ce babu wani laifi idan Musulmi ya shirya bukukuwa kamar murnar zagayowar ranar haihuwarsa ko kuma 'yan uwansa.
Cikin rahoton da jaridar Saudi Gazette ta ruwaito, shehin malamin ya ƙara da cewa haka abin yake idan mutum ya yi bikin tunawa da wani abu kamar wata nasararsa, ko ta 'ya'yansa, ko samun shaidar karatu ko kammala jami'a.
A cewarsa, abin da kawai ya kamata a lura shi ne halal ne kawai amma babu haramci a kan hakan a cikin Musulunci, yana mai cewa bukukuwan na al'ada ne waɗanda ba su da alaƙa da abin da addinin ya hana.
Al-Mubarak ya ce waɗannan lamura ba sa cikin ayyukan addini da aka hana Musulmi ƙarawa ko rage wani abu daga ciki. Ba kamar faɗin Annabi SAW ba cewa: "Duk wanda ya ƙirƙiri wani abu a cikin wannan lamarin namu (Musulunci) da babu shi a cikinsa, ba za a karɓa ba," a cewrsa.
Malamin ya jaddada cewa babu laifi idan mutum ya yi amfani da lokutan hijirar Annabi a matsayin matashiya ko alƙiblar gudanar da ayyuka a rayuwarsu ta yau da kullum.

Hauhawar farashin kayayyakin da mutane ke saya a Najeriya wato Cosumer Price Index (CPI) ta ƙaru zuwa kashi 15.92 cikin 100 a watan Maris na 2022, yayin da ake fama da tashin farashin kayan abinci a ƙasar.
Alƙaluman sun nuna wannan ne adadi mafi girma da aka samu tun Oktoban 2021, wanda kuma ya ƙaru da kashi 0.22 a kan 15.7 cikin 100 da aka samu a Fabarairun 2022.
Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ce ta bayyana hakan cikin rahoton da ta fitar ranar Juma'a.
Sai dai rahoton ya nuna cewa ɗaukacin hauhawar farashi a ƙasar ya ragu daga kashi 14.01 cikin 100 a watan Fabarairu zuwa 13.91 a watan Maris.
NBS ta ɗora alhakin tashin farashin kayayyakin kan tashin farashinn kayayyaki kamar gas da tufafi da kayan tsafta.

Asalin hoton, EPA
Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ce ƙasashen nahiyar Turai ba su da wani zaɓi illa su ci gaba da amfani da fetur da gas ɗin ƙasarsa, yana mai gargaɗin "halin ƙunci na tattalin arziki" idan suka yi yunƙurin maye gurbin makamashin nasa da wani.
"Turai ba su da wani zaɓi cikin sauƙi," a cewar Putin cikin wata hira da manema labarai ta bidiyo daga gidansa da ke kusa da birnin Moscow ranar Alhamis.
"Babu tarin man a kasuwar duniya, kuma na ƙasashen duniya, kamar Amurka, da ake tunanin kaiwa Turai, zai yi wa masu amfani da shi tsada matuƙa."
Tuni ƙasashen Turai suka fara tunanin rage dogaro da makamashin Rasha.
Shuagaban Ukraine Zelensky ya sha sukar ƙasashe kamar Jamus da suka hana a saka takunkumi kan makamashin na Rasha, suna masu cewa zai shafi rayuwar al'ummar ƙasashen nasu.

Asalin hoton, Getty Images
Akalla mutane 35 suka mutu sannan 71 suka jikkata a Zimbabwe yayin da wata motar bas dauke da Kiristoci da ke kan hanyarsu ta zuwa coci domin yin bikin Easter ta kauce kan hanyarta inda ta fada wani rami, a cewar 'yan sanda.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito cewa motar tana dauke da mambobin cocin Christian Church wadanda ke kan hanyarsu ta zuwa wani taron Easter a kudancin kasar.
"Zan iya tabbatar muku cewa hatsarin ya faru ne jiya da daddare. Kawo yanzu mutane 35 sun mutu sannan 71 sun jikkata," a cewar mataimakin Kwamishin 'yan sanda Paul Nyathi a hirarsa da AFP.
"Alamu sun nuna cewa an yi wa motar lodin da ya wuce kima," in ji shi.
Galibin motocin bas a Zimbabwe suna daukar mutane 60 zuwa 75.
"A matsayinsu na mabiya addinin Kirista, ya kamata su zama abin misali amma sai suka yi tafiya da daddare abin da ba a so," a cewar Nyathi.
Yau ake cika kwana 50 da soma yakin Ukraine. Ga wasu hotunan abubuwan da suka faru a kasar a awanni 24 da suka gabata.

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar da ke kula da kan iyalar Poland ta ce 'yan gudun hijira fiye da miliyan biyu da dubu dari bakwai ne suka shiga kasar daga Ukraine tun da aka soma yakin da Rasha.
Ta bayyana haka ne ranar Juma'a.
A makonnin baya bayan nan, 'yan gudun hijirar da suke tsallakawa zuwa Poland sun ragu sannan masu komawa Ukraine sun karu.
Ranar Alhamis, mutane 26,800 suka tsallaka zuwa Poland, karuwar kashi 8 idan aka kwatanta da ranar Laraba,a cewar hukumar a sakon da ta wallafa a Tuwita. Sai dai hakan ya ragu idan aka kwatanta da mutane 142,300 da suka shiga kasar ranar 6 ga watan Maris.
Mutane 16,800. suke shiga Poland daga Ukraine a kullum kafin a soma yaki.
Sai dai tuni wasu daga cikin 'yan gudun hijirar suka bar Poland. Amma wani Farfesa a Jami'ar Warsaw da ke bincike kan 'yan gudun hijira Maciej Duszczyk ya yi kiyasin cewa mutane miliyan 1.2 zuwa miliyan 1.4 suna ci gaba da zama a kasar.

Asalin hoton, NAF
Amurka ta amince ta sayar wa Najeriya makamai da kudinsu ya kai na dala biliyan daya da zummar karfafa yaki da kungiyoyi masu rike da makamai.
A wata sanarwa da hukumar hadin kai game da tsaro ta Amurka ta fitar, ta ce Najeriya ta bukaci sayen jiragen helikwafta 12 masu kai hare-hare da makami mai kai hari inda aka nufa ba tare da matsala ba.
Amurka ta ce daga yanzu Najeriya ba za ta fuskanci wata matsala ba wajen sayen makamai daga wurin ta.
Sai dai ana sa rai wannan batun zai dauki akalla shekaru biyar kafin a kammala shi - domin kuwa zai hada da horas da dakarun tsaron Najeriya kan yadda za su yi aiki da makaman da kuma kauce wa kai hari kan fararen-hula.
Wannan ne karo na biyu da Amurka ke sayar wa Najeriya makamai cikin shekaru biyar.
A baya gwamnatin Barack Obama ta ki sayar wa Najeriya makamai bisa zargin take hakkin dan adam.
Sai dai a shekarar 2017, gwamnatin Donald Trump ta amince ta sayar wa Najeriya jiragen yaki samfurin Super Tucano guda 12.
A shekarar da ta gabata ne aka kai jiragen Najeriya.
Mai gabatar da shirin podcast a BBC mai taken Ukrainecast, Vitaly Shevchenko, ya yi karin haske game da mahaifiyarsa da kanwarta mai fama da laurara, wadanda suka tsallaka iyaka zuwa Poland, wata daya bayan barin mahaifarsu Zaporizhzhia da ke kudu maso gabashin Ukraine.
Wani mai sauraron podcast ya tuntubi Vitaly bayan jin labarin abin da ya faru da iyalansa kuma ya yi alkawarin tuka su a mota zuwa Birtaniya.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Asalin hoton, AP
Jami'an tsaron Isra'ila sun shiga Masallacin Kudus kafin ketowar alfijir a yayin da dubban Falasdinawa suka taru domin yin sallah a wannan wata na Ramadana mai albarka, lamarin da ya haddasa arangama tsakanin su.
Hakan ya yi sanadin raunata Falasdinawa akalla 152, a cewar Jaridar Arab News.
Isra'ila ta ce dakarunta sun shiga Masallacin ne domin cire duwatsu da aka tara a cikinsa da nufin tayar da rikici.
Masallacin na Kudus, wanda Musulmai da Yahudawa suke matukar girmamawa, ya kasance wani wuri da ake yawan samun tashin-tashina tsakanin Yahudawa da Musulmai.
A wannan karon lamarin ya ta'azzara saboda watan Ramadan ya zo daidai da lokacin bikin Yahudawa na Passover, da kuma bikin Easter Sunday da Kiristoci suke gudanarwa.

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban lardin Kharkiv da ke gabashin Ukraine ya ce an kashe akalla fararen-hula 503 tun lokacin da Rasha ta kaddamar da yaki a yankin ranar 24 ga watan Fabrairu.
A wani sako da ya wallafa a Telegram, Oleg Synegubov ya ce kananan yara 24 na cikin wadanda aka kashe sakamakon hare-haren dakarun Rasha.
"Wadannan fararen-hula ba su ji ba ba su gani ba, ba za mu taba yafe kisan da aka yi musu ba," a cewarsa.
BBC ba ta tabbatar da wannan ikirari ba.
Kharkiv - wanda ke da nisan kilomita 40 daga kan iyaka da Rasha - yana da mutane da suka kai miliyan daya da rabi kafin a soma yaki.
Ba kamar sauran yankunan Ukraine ba, wadanda aka sarara da yaki bayan da dakarun Rasha suka mayar da hankali wasu yankunan, Kharkiv bai samu kakkautawa daga hare-haren Rasha ba.

Asalin hoton, Nigeria Presidency
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jaddada cewa bangaren zartarwa zai ci gaba da mutunta iyakokin da ke tsakaninsa da na shari'a kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.
Ya bayyana haka ne a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu, ya aike wa manema labarai ranar Alhamis, a daidai lokacin da gwamnatinsa ta yi afuwa ga wasu tsoffin gwamnoni da aka kama da sace makudan kudaden jihohinsu.
Shugaban kasar ya yi wannan ikirari ne a yayin da ya karbi bakuncin shugabannin bangaren shari'a na kasar domin yin buda-baki a fadarsa da ke Abuja.
"Ina mai tabbatar muku cewa ina matukar mutunta bangaren shari'a," in ji Buhari yana mai karawa da cewa za a tabbatar da doka da oda a kasa ne kawai idan doka ta hau kan kowa ba tare da nuna bambanci ba.
"Ina yin kokarin nisanta kaina da ku saboda gudun zargin yin katsalandan," a cewar Buhari inda ya ce ya gamsu da tsarin da kotuna suke bi wajen gudanar da shari'a.
Nasidi Adamu Yahaya ne yake tare da ku a wannan rana ta Juma'a, Haji babbar rana.
Ku biyo mu domin sanin halin da duniya take ciki.
Za mu fi mayar da hankali kan abubuwan da ke wakana a Najeriya da Nijar da makwabtansu, da ma wasu sassan duniya.