Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Putin ya ce Rasha za ta ci gaba da mamaye Ukraine

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya, Badariyya Tijjani Kalarawi and Sani Aliyu

  1. An kama jami'an tsaron Najeriya dauke da kudin fansa Naira miliyan 60

    Wasu jami'an tsaro da ke dauke da Naira miliyan 60 sun shiga hannun hukumomi.

    Jaridar PRNigeria ta ruwaito cewa an kama jami'an tsaron ne bayan da wasu suka fallasa cewa suna dauke da kudin fansa kuma suna kan hanyar kai kudin ne ga barayi daji.

    Sojojin kasa na Najeriya tare da taimakon wasu dakarun sojin sama ne suka kai wani samame a yankin wada ya sa aka halaka wasu 'yan fashin daji da kuma ceto wadanda aka yi garkuwa da su.

    Wani jami'in tsaro na cikin gida ya shaida wa jaridar PRNigeria cewa "An kwace tsabar Naira miliyan 60 tare da man fetur da wasu bindigogi samfurin AK-47 da wayoyin hannu da kuma harsasai masu yawa."

  2. ICPC za ta binciki gine-ginen da aka yi don ɓatar da haramtattun kuɗi

    Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC, ta ce za ta ci gaba da gudanar da bincike kan wasu gine-gine da aka kammalasu amma ba kowa a cikinsu a wani mataki na magance matsalar hada-hadar haramtattun kudade.

    Hukumar ta ce gwamnati na asarar bilyoyin daloli na haraji da ya kamata a karba na irin wadanan gine-ginen da aka yi watsi da su.

    Ku saurari rahoton Zahraddeen Lawan

  3. Le Pen na adawa da kakaba wa Rasha takunkumin gas

    'Yar takarar shugabancin Faransa Marine Le Pen ta ce tana goyon bayan kakabawa Rasha takunkumi, amma ba wai kan batun samar da mai da iskar gas ba.

    A wata hira da ta yi da wata kafar yaɗa labaran Faransa Inter, ta ce ba ta son al'ummar Faransa su shiga matsi sakamakon takunkumin da aka kakaba na man fetur da iskar gas.

    Kasar Faransa kamar sauran kasashen Turai, tana shigo da gas ta hanyar bututun mai daga kasar Rasha, inda take amfani da shi wajen samar da makamashi.

    Le Pen, da za ta fafata da shugaba Emmanuel Macron a zaben shugaban kasa a zagaye na biyu na ranar 24 ga Afrilu, ta sha suka daga abokan hamayya saboda goyon bayan da ta yi a baya ga Rasha da Shugaba Vladimir Putin.

    Ta bayyana goyon bayan mamaye yankin Crimea da Rasha ta yi a shekarar 2014 amma ta bayyana mamayar da ake yi a halin yanzu a matsayin wani yanayi na daban.

  4. Putin ya ce Rasha za ta ci gaba da mamaye Ukraine

    Shugaba Vladimir Putin ya jaddada cewa Rasha za ci gaba da mamaye kasar Ukraine har sai an cimma dukkanin manufofi, kuma ya zargi Ukraine da jan kafa a tattaunawar sulhu.

    A wata ziyara da ya kai wata cibiyar zuwa sararin samaniya a yankin gabas mai nisa na Rasha, Mr Putin ya bayyana sojojin Rasha a matsayin jarumai.

    Ya ce dalilin gudanar da farmakin shi ne a taimaka wa mutanen yankin Donbas na kasar Ukraine.

    Kusan makonni bakwai da aka kwashe ana gwabza kazamin fada ya janyo hasarar rayukan fararen hula da dama tare da zargin aikata laifukan yaki na sojojin Rasha inda yakin ya raba miliyoyin mutane da gidajensu.

    Mista Putin ya samu rakiyar babban amininsa, shugaban kasar Belarus, Alexander Lukashenko.

  5. Za a ci tarar Firaministan Birtaniya kan saɓa doka

    Firaministan Biritaniya, Boris Johnson da Ministan Kudi Rishi Sunak na shirin biyan tara saboda keta ka'idojin kullen korona.

    'Yan sanda sun gudanar da bincike kan wasu tarukan holewa 12 da ake zargin sun halarta, kuma an gano cewa Mista Johnson ya halarci akalla uku daga cikinsu.

    A wani taron da aka yi a ofishin majalisar ministoci an gabatar masa da kek na murnar zagayowar ranar haihuwarsa.

    Zuwa yanzu ofishin 'yan sandan kwaryar birnin Landan ya ci tarar sama da mutane 50 saboda halartar tarukan a gine-ginen da aka sanya dokar korona, kuma fadar mulki ta Downing ta ce za ta tabbatar ko Mista Johnson na cikinsu.

    Shugaban jam’iyyar Labour, Keir Starmer, ya ce dole ne Firaministan da ministansa su yi murabus saboda yadda mai dokar bacci ya bide da gyangyadi.

  6. An gurfanar da kamfanin shirya fim kan kin biyan kudin hayar kaya a Masar

    Wani lauya a kasar Masar, ya kai karar masu shirya shirin talbijin mai dogon zango da aka fassara da harshen larabci mai suna Suits, wato Badlat da harshen larabci, inda ya yi ikirarin kamfanin da ya shirya wasan bai biya kudin hayar Kwat din da tauraron shirin ya sanya ba.

    Sai dai kamfanin ya musanta wannan zargi, inda ya sha alwashin daukar matakin shari'a kan bata ma sa suna.

    Ikirarin da ake magana akai da aka shigar da karar, ya kai dala miliyan 1 da dubu dari biyar, na kayan wani kamfanin kayan kawa da ya kware wajen bai wa fitattun mutane da masu shirya fina-finai hayar kayan kece raini.

    Shirin Badlat na daya daga cikin masu farin jini a watan Ramadan, inda manyan kamfanonin shirya fina-finai masu dogon zango ke baje kolinsu.

  7. Jami'ar Lagos na neman karin bayani kan gawar da aka gano a tekun da ke bayanta

    Jami'ar Lagos da ke Najeriya ta yi kiran ayi ma ta karin bayani bayan tsintar gawar gawar wani da a ba san ko waye ba, a bakin ruwan da ke bayan jami'ar.

    A wata sanarwa da hukumomin jami'ar suka fitar,da wallafawa a shafinsu na Tiwita, sun ce an gano gawar ne a ranakun karshen mako, bayan an tafka ruwa, kuma nan da nan suka sanar da jami'an tsaro.

    Kawo yanzu ba bu cikakken bayani, kan yadda gawar ta kare a cikin ruwan da kuma musabbabin mutuwar mutumin.

    Bakin tekun da ke kusa da jami'ar ta Lagos, wuri ne da jama'a ke zuwa domin shakatawa, don haka jami'ar ta bukaci wdanda ke da wani bayani game da hakan su tuntubi jami'an 'yan sanda.

    A karshe sanarwar ta tabbatarwa da dalibai da ma'aikatan jami'ar su kwantar da hankalinsu, za ayi duk mai yi domin tabbatar da tsaron lafiyarsu.

    Fitacciyar jami'ar ta Lagos ta kyankyashe manyan mutane a Najeriya, kamar Wole Soyinka da mataimakin shugaban Najeriya na yanzu farfesa Yemi Osinbajo.

  8. Yan bindiga sun yi garkuwa da motocin fasinja guda biyu kirar Bus

    Rahotanni daga jihar Rivers da ke kudancin Najeriya na cewa, wasu mahara sun yi garkuwa da motocin fasinja guda biyu kirar Bus.

    Motocin dai na kan hanyarsu ta zuwa yankin Kalabari ne da ke Degema a karamar hukumar Akukutoru, daga birnin Ftakwal a lokacin da maharan suka tare da motocin.

    Jaridar The Nation ta rawaito cewa, rundunar 'yan sandan jihar Rivers ta tabbatar da faruwar kai wanna hari, tare da fara binciken inda aka kai fasinjojin da kawo yanzu ba a tantance yawansu ba.

  9. Sojin Najeriya sun gano naira miliyan 60 da za a kai wa 'yan fashin daji kudin fansa

    Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun gano naira miliyan 60 da aka yi nufin kai wa 'yan ta'adda kudin fansar karbo wasu daga cikin wadanda 'yan bindiga suka yi garkuwa da su.

    Jaridar PRNigeria da ke da alaka da jami'an tsaron Najeriya ta rawaito cewa sojin sun ce ana zargi a cikin wadanda aka samu da kai kudin fansar har da jami'an tsaron farin-kaya wato DSS.

    Har wa yau, dakarun sun yi nasarar kubutar da wasu mutane da aka yi garkuwa da su da suka hada da mata da kananan yara.

    Dakarun, wadanda suka hada da sojin sama da na kasa, sun kai ga cin karfin 'yan bindigar. An gano muggan makamai da bindiga kirar AK47, da albarusai da sauransu.

    Sojojin sun ce za su mika batun jami'an tsaron da suka hada da na DSS da ake zargi da kai kudin fansar ga ma'aikatar tsaron Najeriya, domin gudanar da bincike

  10. An kashe sojojin Benin biyar

    An kashe sojojin Benin biyar a cikin wani harin da 'yan bindiga suka kai a gandun dajin Pendjari da ke arewacin kasar.

    Yankin arewacin Benin na fuskantar karuwar hare-haren masu ikirarin jihadi.

    Kazalika yankin ya zama wurin daukar sabbin 'yan tayar da kayar baya, saboda kusancin yankin da yankunan da ake fama da rikici a makwabtan kasashen Burkina Faso, da Nijar da Najeriya.

    A shekarar 2019, an kashe wani dan-jagorar masu yawon bude-ido sannan aka sace 'yan kasar Faransa biyu.

  11. Buhari ya taka rawar gani a fannin tsaro - Ban Ki-moon

    Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya nuna jin dadi kan kalaman da tsohon Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya yi kan rawar da gwamnatinsa ta taka wajen inganta tsaro da bunkasa tattalin arzikin kasar.

    A jiya ne dai Shugaba Buhari da Ban Ki-moon suka tattauna ta wayar tarho, Buhrin ya jaddada girman da Mista Moon ke da shi a wurinsa, tare da gode masa kan wayar tarhon da ya yi, a cewar wata sanarwa da fadar gwamnatin Najeriya ta fitar.

    Sanarwar da mai bai wa shugaban shawara kan yada labarai Malam Garba Shehu ya sanya wa hannu, ta ce Moon ya jinjina wa Shugaba Buhari game da shawo kan matsalar tsaro da kasar ke fama da ita.

    Garba Shehu ya ce shugaban ya gode wa tsohon Magatakardar Majalisar Dinkin Duniyar kan gudunmawar da ya bai wa Najeriya a lokacin da yake kan aiki.

    Mista Moon ya kuma gode wa shugaban ma'aikatan fadar shugaban Najeriya Farfesa Ibrahim Gambari da ya taba aiki karkashin sa, da kuma Mataimakiyar Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Hajiya Amina Muhammad, wadanda ya ce shekarun da suka yi aiki tare masu muhimmanci ne da kokarin kawo ci gaba a Najeriyar.

    Wannan na zuwa ne adaidai lokacin da ake ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro a sassa daban-daban na Najeriya, musamman arewacin kasar da ke fama da matsalar barayin daji, da masu satar mutane don neman kudin fansa.

  12. Ana zargin Rasha da kai hari da makamai masu guba a Mariupol

    An fara yada jita-jitar cewa Rasha ta kai hari da makamai masu guba a birnin Mariupol da sojinta suka yi wa kawanya.

    A jiya ne dai mayakan sa-kai na Ukraine da ke fafatawa a birnin suka fara yada wannan ikirari.

    A wani bidiyo da shugaban mayakan kuma tsohon kwamandanta, Andriy Biletskyy, ya ce an harba makamai masu guba guda biyu a birnin Azovstal wanda kungiyar ta Azov Battalion ke gadi.

    Ya ce an ji wa mutane uku rauni, ba tare da ya ba da karin shaida kan hakan ba.

    Mataimakin ministan tsaron Ukraine, Hanna Malya, ya ce idan aka yi la'akari da bayanan da ke fitowa da yankin, akwai alamun an yi amfani da sinadarin phosphorus munition, amma dai ana gudanar da bincike kan hakan.

    A jiya ne mai magana da yawun 'yan a-waren Rasha a Donetsk, Eduard Basurin, ya bayyana karara tare da kira ga Rasha ta yi amfani da makamai masu gubarta domin kare kasar.

    A hira da kamfanin dillancin labarai na Interfax, Basurin ya yi ta cewa ba a yi amfani da makamai masu guba a Mariupol ba.

    Amurka ta ce tana sane da duk rahotannin da ake yadawa, amma har yanzu ba ta tantance gaskiyarsu ba.

    Idan har ta tabbata gaskiya ne, wannan zai zamo babban tashin hankali da damuwa kamar yadda mai magana da ma'aikatar tsaro ta Pentagon ya bayyana.

  13. Zalensky zai yi wa Tarayyar Afirka jawabi kan mamayar Rasha

    Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya bukaci taimakon kungiyar Tarayyar Afirka, domin mara masa baya kan mamayar da Rasha ta yi kasarsa, inda ya bukaci yi wa kungiyar jawabi.

    Mr Zelensky ya wallafa a shafinsa na Tuwita cewa ya kira shugaban Senegal Macky Sall a ranar Litinin, kuma a tattaunawarsu sun tabo batun matsayar Afirka a sanarwar da ta fitar a watan Fabrairu tare da bukatar Rasha ta dakatar da bude wuta tare da hawa teburin sulhu.

    A tattaunawar ta wayar tarho, Mr Zalensky ya shaida wa Macky Sall yadda Ukraine ke fadi-tashi da kokarin kare kasar daga hare-haren Rasha.

    Tarayyar Afirka dai ta nuna rashin jin dadi da amincewa matakin da Rasha ta dauka a Ukraine.

    Kuma Senegal na daga cikin kasashe 17 na Afirka da suka rattaba hannu a Majalisar Dinkin Duniya kan bukatar Rasha ta kawo karshen yakin sojin da take yi a kasar.

  14. Yakin Ukraine: Tarayyar Turai na so Najeriya ta rika sayar mata da karin iskar gas

    Tarayyar Turai na kokarin yaukaka dangantaka da Najeriya domin samun karin wuraren da za ta sayi iskar gas da nufin rage dogaro ga Rasha.

    Najeriya ce kasa ta hudu da ke safarar iskar gas zuwa Turai, inda aka yi kiyasin cewa kusan kashi 40 cikin 100 na gas din da kasar ke fitarwa ana kai shi kasashen Turai ne.

    Tarayyar Turai na son dakatar da sayen gas daga Rasha a matsayin martani kan yakin da ta kaddamar a Ukraine.

    Jami'an diflomasiyyar Turai sun kai ziyara Najeriya a ranar Litinin, inda suka gana da shugabannin kamfanin mai na kasar.

    “Matsayinmu ba wai ya tsaya na babbar abokiyar huldar Najeriya ba, muna son kulla alaka da kasar ta fannin mai da iskar gas, saboda yawancin kamfanonin da ke aiki tare da ku na kasashen Turai ne. Mu ma muna son zama daya daga cikin abokan huldarku,'' in ji jakadan Tarayyar Turai a Najeriya Samuela Isopi.

    Shugaban kamfanin mai na Najeriya NNPC sun tabbatar wa wakilan Turai cewa a shirye kamfanin yake ya kara yawan gas din da yake fitarwa a kasuwannin duniya.

    Hukumomin Najeriya sun ce kasar ta tabbatar tana da iskar gas da ta kai yawan cubic tiriliyan 209.5 a watan Junairun shekarar 2022.

    Yayin da kasar ke samun kashi biyu na kudaden shigar da ake tarawa gwamnatin Najeriya.

  15. UNICEF: Miliyoyin yara sun tagayyara sakamakon yaki a Ukraine

    Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya ce kusan kashi biyu cikin uku na yaran Ukraine sun tsere daga gidajensu cikin makwanni shida da mamayar da Rasha ta yi wa kasar.

    Majalisar Dinkin Duniya ta kuma tabbatar da mutuwar yara 142, duk da cewa ta yi gargadin adadin ka iya fin haka.

    Daraktan shirin gaggawa na UNICEF Manuel Fontaine, wanda ya dawo daga ziyarar aiki Ukraine, ya ce farar-hula kusan miliyan biyar ne suka rasa muhallansu, yayin da yara sama da miliyan bakwai suka shiga gararamba cikin kankanen lokaci, lamari ne da bai taba ganin ya faru cikin sauri ba a shekaru 31 da ya kwashe yana aikin jinkai.

    Fonteine ya shaida wa Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya cewa " cikin yara kanana miliyan uku da dubu 200 da suka rage a gidajensu, kusan rabinsu na cikin hadarin rasa isasshen abinci."

    Ya yi gargadin lamarin zai munanan a birane kamar Matiupol da Kherson, inda babu ruwa mai tsafta, babu abinci, sannan babu magani.

    A bangare guda kuma, jakadan Ukraine a Majalisar Dinkin Duniya, Sergiy Kyslytsya, ya yi ikirarin Rasha ta dauke yaran kasar sama da 121,000, sun kuma fara shirin ba da rikonsu ga iyalai Rashawa.

    Sai dai Fontaine ya ce kawo yanzu babu shaidar da za ta tabbatar da wannan ikirari, amma UNICEF za ta gudanar da bincike domin gano gaskiyar ikirarin nasa.

  16. 'Yan sanda sun hana yin tashe a Kano

    Rundunar 'yan sandan jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta sanar da soke tashe da ake farawa a ranar 10 ga watan azumin Ramadan.

    Wannan na cikin wata sanarwar da mai magana da yawun 'yan sandan jihar ta Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya aikewa manema labarai ranar Litinin da maraice.

    Sanarwar ta ce an soke yin tashen ne saboda yadda bata-gari ke amfani da wannan dama wajen aikata miyagun laifuka da suka hada da kwacen wayar salula, da daba, da shaye-shayen miyagun kwayoyi da sauransu.

    Don haka jami'an 'yan sandan sun dauki matakai domin magance matsalar tsaro da ayyukan bata-gari a jihar, in ji sanarwar.

    CP Sama'ila ya yi kira ga al'ummar jihar Kano, musamman iyaye da shugabannin al'umma su gargadi 'ya'yansu domin kauce wa duk wani yunkuri na taka doka.

    Rundunar 'yan sandan ta ce duk wanda aka samu da karya doka zai fuskanci fushin hukuma ta hanyar ladabtarwa.

  17. Barkanmu da warhaka

    Nasidi Adamu Yahaya da Badriyya Tijjani ne suke tare da ku a wannan hantsi. Da fatan za ku biyo mu domin sanin halin da duniya take ciki a wannan rana ta Talata.

    Za mu kawo maku labarai da rahotanni kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.

    Za mu mayar da hankali kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtanta da Rasha da Ukraine, da ma wasu sassan duniya.