Ƙarshen rahotanni
Mun kawo ƙarshen rahotannin a wannan shafi.
Mu haɗu da ku gobe Litinin - Mande tushen aiki - don samun sabbin rahotannin.
Umar Mikail ne ke fatan za ku yi sahur lafiya.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.
Awwal Ahmad Janyau and Umar Mikail
Mun kawo ƙarshen rahotannin a wannan shafi.
Mu haɗu da ku gobe Litinin - Mande tushen aiki - don samun sabbin rahotannin.
Umar Mikail ne ke fatan za ku yi sahur lafiya.
Sakamakon Kuri'un da aka kaɗa zuwa yanzu a zaɓen shugaban ƙasar Faransa ya nuna Emmanuel Macron ya samu kashi 28 cikin 100 idan aka kwatanta da Marin Le Pen da ta samu kashi 24.
Yanzu dai an cire sauran 'yan takara 10 daga wannan zaɓe.
Wakiliyar BBC ta ce Macron bai fara kamfe da wuri ba sai kamar mako uku da suka wuce, ita kuma Marin Le Pen ta daɗe da farawa, kuma ta mayar da hankali kan matsin rayuwa da ake fama da shi a kasar, abin da yake damun masu kaɗa kuri'ar kenan.
Ya zuwa ƙarfe 5:00 na yammacin Faransa, kashi 75 cikin 100 ne na masu kaɗa kuri'ar suka fito, wanda ya yi ƙasa da kashi 4 cikin 100 na wadanda suka yi zaɓe a 2017 idan aka kwatanta.
'Yan bindiga sun kashe mutum aƙalla 26 cikin wasu hare-hare da suka kai a ƙauyuka huɗu na Jihar Filato da ke tsakiyar Najeriya ranar Lahadi.
Maharan sun far wa ƙauyukan ne da ke Ƙaramar Hukumar Kanam a kan babura, inda suka dinga harbe mutane tare da ƙona gidaje masu ɗumbin yawa da kuma sace shanu.
Mazauna yankin sun ce an ga gawar mutum 20 a garin Gyambau, sannan an ga wasu shida a Kyaram.
Kazalika, an kai hare-hare a garuruwan Dungur da Kukawa. Mutane da dama ne suka ɓace kuma sakamakon harin.
Hukumomi sun ce an tura ƙarin jami'an tsaro a yankin.
Jihar Filato ta sha fama da rikicie-rikice da ke da nasaba da ƙabilanci da kuma addini, kafin daga baya 'yan fashin daji masu kashe mutane da kuma garkuwa da su don neman kuɗin fansa su ta'azzara matsalar.
Masu zaɓe a Faransa na jefa ƙuri'ar zaɓen sabon shuagaban kasar yayin da ake sa ran shugaba mai-ci Emmanuel Macron da abokiyar hamayyarsa Marin Le Pen za su sake fafatawa a zagaye na biyu na zaben.
Wakiliyar BBC ta ce Macron bai fara kamfe da wuri ba sai kamar mako uku da suka wuce, ita kuma Marin Le Pen ta dade da farawa, kuma ta mayar da hankali kan matsin rayuwa da ake fama da shi a kasar, abin da ya ke damun masu kaɗa kuri'ar kenan.
Ya zuwa karfe 5 na yammacin Faransa, kashi 75 cikin 100 ne na masu kaɗa kuri'ar suka fito, wanda ya yi kasa da wadanda suka yi zabe a 2017 idan aka kwatanta.
Wakilin BBC a Paris ya ce shugabannin jam'iyyar masu tsattsauran ra'ayi za su zama karfen kafa ga siyasar Faransa da ta Turai baki ɗaya.
Mutum sama da miliyan huɗu da rabi ne suka tsere daga Ukraine tun bayan fara yaƙi a ranar 24 ga watan Fabarairu, a cewar hukumar 'yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNHCR).
UNHCR ta ce akwai 'yan gudun hijirar Ukraine 4,503,954 - ƙarin 62,291 kenan a kan na kwana ɗaya kafin haka.
Ta ce Nahiyar Turai ba ta taɓa ganin irin wannan adadin ba tun bayan Yaƙin Duniya na II.
Kashi 90 cikin 100 na 'yan gudun hijirar mata ne da ƙananan yara, sakamakon tilasta wa maza 'yan shekarun 18 zuwa 60 zama don kare ƙasarsu.
'Yan Sandan Merseyside na bincikar dan kwallon Manchester United, Cristiano Ronaldo, wanda ake zargi ya fasa wayar dan kallo.
Wani bidiyo da yake yawo a kafar sada zumunta dauke da sako, ya nuna lokacin da ya kwada wayar da kasa, bayan da United ta yi rashin nasara da ci 1-0 a gidan Everton.
Daga baya Ronaldo mai shekara 37 ya nemi afuwa a kafar sada zumunta.
'Yan Sandan Merseside sun ce suna binciken ''rahoto kan zargin cin zarafi'' da aka yi a filin Goodison Park ranar Asabar.
Jami'in da ke magana da yawun jami'an tsaro ya ce suna tattaunawa da Manchester United da kuma Everton kan lamarin.
''A lokacin da 'yan wasan ke barin fili da misalin karfe 2.30, an yi rahoton cewar an ci zarafin wani yaro daga wajen wani dan wasa baki a lokacin da za su bar filin.''
Babbar mai shigar da ƙara a Ukraine ta ce gawar mutum 1,222 aka gano a wani yanki na birnin Kyiv tun bayan da dakarun Rasha suka fice daga yankin.
Iryna Veneditktova ta faɗa kafar talabijin ta Sky News cewa hukumomin Ukraine na bincike kan lamura 5,600 da ake zargin an aikata laifukan yaƙi, kuma tuni ta iya tantance laifukan yaƙi 500, ciki har da wanda suka ƙunshi manyan jami'an sojan Rasha da na gwamnatin ƙasar.
"Abin da muke gani a yankunan Ukraine laifukan yaƙi ne, da laifuka kan ɗan Adamtakar mutane, kuma muna yin duk abin da za mu iya don magance hakan," a cewarta.
Ta ce Ukraine na da hujjar da ke nuna Rasha ta kai harin makami mai linzami kan tashar jirgin ƙasa a Kramatorsk da ke gabashin ƙasar, wanda ya kashe mutum fiye da 50 da ke jiran ƙarasowar jirgin.
Rasha ta musanta hannu a harin na ranar Juma'a tana mai iƙirarin cewa ba makaminta ba ne. Ta kuma musanta kai wa fararen hula hari.
A ranar Lahadi 10 ga watan Afrilu Kiristoci a faɗin duniya ke bikin Palm Sunday - wadda ka iya nufin Lahadin Kwakwa da Hausa.
Bikin na nuna ranar ƙarshe ta makon Lent, inda mabiya adinin Kirista ke haƙura ko kuma su daina aikata abubuwan da suka fi so na tsawon kwana 40.
Palm Sunday rana ta musamman ga Kiristoci. Alama ce ta shiga Mako Mai Tsarki kuma kodayaushe bikin na faɗowa ne a kowace Lahadi wadda daga ita sai bikin Ista (Good Friday da Easter Sunday).
Faransawa na gudanar da zagayen farko na zaɓen shugaban kasainda za su zaɓi tsakanin 'yan takara goma 12.
Ƴan takara biyu da suka fi yawan ƙuri’a ne za su kai ga zagaye na biyu na zaɓen nan gaba a wannan watan.
Faransawa kusan miliyan ke da ƴancin kaɗa ƙuri’a a zaɓen zagaye na farko.
Al'ummar Mexico na kaɗa kuri'ar zaben raba gardama da ba a taba yin irinsa ba kan ko shugaban Andres Manuel Lopez Obrador zai ci gaba da zama a kan karagar mulki.
Mista Lopez Obrador ya ce yana da matuƙar muhimmanci a bai wa masu kaɗa ƙuri'a damar tabbatar da zaɓinsu na rabin wa'adin mulkinsa na shekaru shida.
Ƴan adawa sun cewannan wani mataki ne mai matuƙar tsada don karkatar da hankalin jama’a daga matsalolin da ƙasar ke fuskanta.
Shugaba Lopez Obrador ke mulkin Mexico tun watan Disambar 2018.Shi ne shugaba na farko da ya gudanar da irin wannan zaɓen raba gardama.
Ko da yake ana sa ran shi zai zai yi nasara, masu suka na ganin cewa nasarar da ya samu za ta iya buɗe kofar tsawaita wa'adin shugabancin kasar, wanda a halin yanzu kundin tsarin mulkiya kayyaɗe zuwa shekara shida.
Gwamnatin Najeriya ta ce an samu katsewar lantarki ne a sassan Najeriya sakamakon yadda aka lalata layin samar da lantarkin na Odukpani Ikot Ekpene.
Sanarwar da gwamnatin ta fitar ranar Lahadi ta ce an samu katsewar lantarkin kusan 400MW, wanda ya haifar da rashin wuta a sassan Najeriya.
An fuskanci katsewar lantarki a sassan Najeriya tun ranar Juma'a.
Sanarwar ta ce an yi nasarar magance matsalar ta hanyar amfani da wani layin samar da lantarkin da ke Calabar.
Mahukuntan Isra'ila sun ce Falasdinawa sun lalata wani wuri mai tsarki na Yahudawa a Nablus, a yayin da rikici ke ƙara ƙamari tsakanin Falasdinawa da sojojin Isra'ila a yankin gabar Yamma da Kogin Jordan da Isra'ila ta mamaye.
Wani shafin Twitter na gwamnatin Isra'ila ya wallafa wani bidiyo da ya ce ke nuna yadda Falasdinawa ke kai hari a wurin da Yahudawa ke ganin ya ƙunshi ƙabarin Annabi Yusuf.
Zuwa yanzu babu wani martani daga ɓangarorin Falasdinawa.
Yahudawa na girmama wurin da ƙabarin yake, amma yana cikin yankin Yamma da Kogin Jordan da Isra'ila ta mamaye.
An sha yin arangama a wurin, har ta kai aka ƙona kafin aka sake gyarawa.
Ministan tsaron Isra'ila Benny Gantz ya bayyana al'amarin a matsayin "babban laifin saɓa ƴancin ibadah."
Yankin Yamma da Kogin Jordan na fuskantar barazanar tsaro tun bayan farmakin da sojojin Isra'ila suka ƙaddamar bayan harin da aka kai a Tel Aviv da kuma cikin yankin Isra'ila.
Mutumin da ake ganin na kan gaba domin zama Firaministan Pakistan Shehbaz Sharif, ya ce sauke Imran Khan wata dama ce ta sake gina ƙasar.
A ranar Litinin majalisa za ta kada ƙuri'a don maye gurbin Mr Khan.
Alamu sun nuna Mista Sharif za a zaɓa matsayin sabon Firaminista.
Ya ce sabon kawancensa zai sake gina Pakistan.
Tuni wa'adin tsayawa takarar ya wuce.
Imran Khan ya fuskanci ɓaraka daga abokan kawancensa waɗanda suka yi watsi da shi suna masu dora masa laifin taɓarɓarewar tattalin arziki.
Mista Khan ya zargi Amurka da yi ƙulla masa maƙarƙashiyar, kuma ya yi iƙirarin cewa ba zai aminta da abin da ya kira gwamnatin da aka shigo da ita daga kasashen waje ba.
Ba za a yi zaɓe a Pakistan ba sai shekara mai zuwa. Sai dai Mista Sharif ya ce yana son a yi zaɓen da wuri da zarar an kafa dokar majalisa ta amince.
Ukraine ta ce ta sake gano wani makekenƙabari a kusa da Kyiv, bayan janyewarda sojojin Rasha suka yi.
Wani jami'i a kauyen Buzova ya ce ƙabarin na ƙunshe da gawarwakin fararen hula da dama, wadanda aka binne a wani rami kusa da gidan mai.
Kawo yanzu babu wani tabbaci daga wata kafa mai zaman kansa, amma zuwa yanzu an gano wasu manyan ƙaburbura a yankunan da ke kusa da Kyiv.
Sojojin Rasha sun mamaye yankin tsawon makonni a lokacin da suka yi wababban birnin Ukraine ƙawanya.
Ƙasashen duniya tuni suke ta Allah wadai da gwamnatin Moscow kan zargin aikata laifukan yaki. Moscow ta musanta kai hari kan fararen hula.
Rahotanni a Jamhuriyar Dimukradiyyar Congo na cewa,ƴan tawayen M23 sun karɓe iko da yawancin kauyukan gabashin kasar, bayan wata arangama da dakarun gwamnati.
Rikicin ya sake barkewa a ranar Larabar da ta gabata, bayan shafe tsawon lokaci ana zaman Lafiya.
Tun da farko, rikicin baya-bayan nan ya tilastawa dubban farar hula tserewa daga arewacin yankin Kivu.
Ƙungiyar M23 mai adawa da gwamnatin Congo, ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta a ranar 1 ga watan Afrilu tana mai cewa tana son ta tattauna da gwamnati domin aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma shekaru 10 da suka shude.
Manchester City da Liverpool za su gwabza a Etihad ranar Lahadi a babban wasan Premier da zai iya tantance wanda zai lashe kofin gasar a bana tsakanin manyan ƙungiyoyin biyu.
Man City ce saman tebur da tazarar maki ɗaya tsakaninta da Liverpool, yayin da ya rage wasa bakwai a kammala gasar.
Liverpool za ta iya karɓe jan ragamar teburin Premier idan ta yi nasara, kuma karon farko da ta hau teburin gasar tun watan Oktoba.
City na harin lashe kofin Premier karo na huɗu a kaka biyar.
Liverpool wadda tuni ta ɗauki kofin Carabao, tana harin lashe kofi huɗu, yayin da City ke harin kofi uku na Zakarun Turai da FA da kuma premier.
Faransawa na gudanar da zagayen farko na zaɓen shugaban kasainda za su zaɓi tsakanin 'yan takara goma 12.
Ƴan takara biyu da suka fi yawan ƙuri’a ne za su kai ga zagaye na biyu na zaɓen nan gaba a wannan watan.
Ƴan takarar da ke kan gaba a ƙuri’ar jin ra’ayi su ne shugaba Emmanuel Macron da shugabar masu ra’ayin riƙau Marine Le Pen, waɗanda sakamakon ya nuna za su iya lashe zaɓen.
Marine Le pen ya yi ta mayar da hankali a yaƙin neman zaɓenta kan bai wa Faransa fifiko a gidaje, da ayyukan yi da kuma tsaurara matakan tsaro.
Mista Macron da ya fi mayar da hankali kan yaƙin Ukraine, sai daga baya ne ya fara taɓo batutuwan da suka shafi cikin gida.
Idan har Macron ya lashe zaɓen zai kasance shugaba na farko bayan Jacques Chirac da ya yi wa’adi na biyu a shekaru 20.
A 2017 aka zaɓi Marcon wa'adi na farko inda ya lashe zaɓen da gagarumin rinjaye.
Gwamnan yankin Luhansk da ke gabashin Ukraine, ya yi gargadin cewa Rasha na kara zafafa kai hare harenta a yankin, a don haka ya bukaci mutane da su tsere.
Gwamnan ya ce akwai kusan kaso daya bisa uku na mazauna yankin da suka rage, kuma rayuwarsu na cikin hadari.
Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya ce yanzu dakarun Rasha sun mayar da hankali ne a gabashi da kudancin kasar wajen kai hare hare.
Mataimakiyar Firaministan kasar, Iryna Vereshchuk, ta ce sojojin Ukraine 12 da fararen hula 14 za su dawo gida a wani bangare na musayar fursunoni.
Ba ta bayyana ko Rashawa nawa aka saka ba.
Muna maku marabara da kasancewa da mu a wannan shafin da muke kawo maku labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faru a sassan duniya