Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Kotu ta hana ƴan jarida da sauran jama'a halartar shari'un Nnamdi Kanu da na BH

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Kotu ta wanke Sanata Abba Moro, ta daure wani babban sakataren ma'aikatar cikin gida kan badakkalar daukan ma'aikata

    Wata babbar kotu a Abuja ta wanke Sanata Abba Moro da wasu mutum biyu kan tuhumar da aka yi musu ta badakkalar daukan ma'aikatan hukumar shige da fice a 2014.

    Alkalin kotun Nnamdi Dimgba ya yanke hukunci a shari'ar, yana cewa hukumar da ke yaki da masu yi ma tattalin arziki zagon kasa, EFCC cewa ta gaza gamsar da kotu cewa mutanen da aka gurfanar sun aikata laifukan.

    Abba Moro tsohon ministan harkokin cikin gida ne a wancan lokacin, kuma an gurfanar da shi a gaban shari'a ne tare da babbar sakatariyar ma'aikatar shige da fice Mrs Anastasia Daniel-Nwobia, da wani tsohon darakta a ma'aikatar mai suna Felix Alayebami da kuma wani kamfani Drexel Tech Nigeria Ltd.

    An dai tuhumi mutanen ne da hada baki su aikata lafukan da suka hada da halarta kudin haram, da kuma damfara, yayin da aka gudanar da wani aikin daukar sababbin ma'aikatan hukumar ta shige da fice.

    A karshe dai rikici ya barke inda saboda wata mummunar turreniya, wasu masu neman aiki 14 suka rasa rayukansu.

  2. Babbar kotun tarayyar Najeriya ta hana ƴan jarida da sauran jama'a halartar shari'un Nnamdi Kanu da na Boko Haram

    Alkalin alkalan babbar kotun tarayya a Najeriya John Tsoho ya fitar da wata sanarwa da ke bayyana yadda kotun za ta rika gudanar da shari'un da suka jibanci ta'addanci a gaban kotun.

    Akwai shari'un da ke gaban kotun, ciki har da wanda ake wa Nnamdi Kanu shugaban kungiyar IPOB da gwamnatin Najeriya ta ayyana a matsayin kungiyar ta'addanci da ta 'yan canjin kudi da ake tuhuma da taimaka wa 'yan ta'adda, da kuma mayakan Boko Haram.

    Alkali Tsoho ya ce sababbin tsare tsaren gudanar da ayyukan kotun na karkashin dokar kasa a karkashin sashe na 254 na tsarin mulkin Najeriya 1999.

    Sanarwar ta ce a karkashin wannan sabon tsarin, za a hana kafafen yada labarai halarta da yin rahotanni kan shari'un, sai dai idan kotun ta amince da haka.

    Kotun ta kuma bayyana cewa za a rika gudanar da wasu shari'un ta hanyar amfani da fasahar zamani wato ta amfani da bidiyo da kuma ta kafar sadarwa ta intanet.

    Baya ga 'yan jarida, za a kuma hana sauran jama'a halartar shari'un, in dai ba wanda ake tuhuma da aikata laifukan ta'addanci ba, da kuma lauyoyinsu.

    Sannan sanarwar ta ce ba za a lamunci kowa ya shiga cikin kotun da wayoyin salula ko ma wasu na'urorin da ke iya nadan sauti ko bidiyo ba yayin da ake zaman shari'ar.

    A karshe sanarwar ta yi gargadi, tana cewa za a hukunta duk wanda ya karya wannan sabon tsarin karkashin sashe na 34(5) na dokar da ke hukunta laifukan ta'addanci ta 2011.

  3. An dakatar da Rasha daga hukumar kare ƴancin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya

    Babban zauren Majalisar Dinkun Duniya ya kada kuri'ar dakatar da Rasha daga hukumar da ke kare hakkin dan Adam yayin wani zama da aka yi a birnin New York.

    Matakin ya biyo bayan tuhumar da ake ma Rasha cewa sojojinta na aikata laifukan yaki a Ukraine.

    Kafin a akada kuri'a, jakadan Ukraine a Majalisar Dinkin Duniya SErgiy Kyslytsya ya tuhumi Rasha da aikata munanan laifuka - musamman bayan kashe-kashen da ake tuhumar Rashar da aikatawa a garin BUcha.

    Wakilin Rasha Gennady Kuzmin ya yi tir da kuri'ar, sannan kuma wasu kasashe, ciki har da Koriya ta Arewa da Syria sun mara ma sa baya.

  4. Buhari ya gana da sabon shugaban jam'iyyar APC a Fadar Aso Rock

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da shugaban jam'iyyar APC ta kasa, Sanata Abdullahi Adamu a Fadar Aso Rock da ke Abuja.

    Tsohon shugaban riko na APC kuma gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni ya raka sabon shugaban.

    Wannan ne karo na farko da Sanata Abdullahi Adamu ke kai ma Shugaba Buhari ziyara tun bayan da aka kammala babban taron jam'iyyar a Abuja.

    Ganawar na da nasaba da shirye-shiryen da jam'iyyar ke yi na zabukan fitar da gwani domin tunkarar babban zabe na kasar da za a yi a shekara 2023.

  5. Ukraine ta yaba wa Nato kan da matakan da take dauka don taimakonta

    Ministan harkokin wajen Ukraine ya yabawa kungiyar tsaro ta Nato kan samun hadin-kai mai karfi da matakan da suke dauka wajen marawa kasarsa baya.

    Dmytro Kuleba ya samu halartar taron ministocin ketaren kasashen Nato a Brussels.

    Ya kuma bukaci a basu ƙarin makamai domin yaƙar sojojin Rasha da ke musu mamaya.

    Kafin tattaunawar, Sakatare Janar na ƙungiyar ta Nato, Jens Stoltenberg ya ce kungiyar za ta duba bukatar Ukraine na neman ƙarin makamai da taimakon soji domin kare kanta.

    Ya ce "abubuwan da muka gani cikin kwanaki ya kazanta sosai a wannan yaki, don haka muke duba muhimmanci taimakawa Ukraine.

    "Kuma ina ganin zuwan Mista Kuleba wannan wuri a yau na da muhimmanci sosai domin mu tattauna kan yadda za a taimaka ma Ukraine na aiki da Nato amma ba ta cikin kungiyar."

  6. An ceto ƴan Nijar 25 masu tafiya Libiya da aka yasar a Sahara

    Hukumar da ke kula da ƙaurar jama'a ta Majalisar Ɗinkin Duniya IOM, ta ce ta ceto mutum 25 da aka yasar a Sahara.

    Madame Aissatou SY ita ce mai magana da yawun hukumar ta IOM a Nijar, ta kuma tabbatar wa da BBC faruwar lamarin

    Daga ciki har da mata da kananan yara yan asalin jihohin Maradi, Tawa da kuma Damagaram da ke kokarin ketara Sahara zuwa Libiya.

    Hakan na faruwa dai-dai lokacin da hukumomi ke cewa sun dauki tsauraran matakai don hana matan da yara tafiya yawon bara a wasu kasashe.

  7. Gwamnan Zamfara ya amince da naɗin Bashar Isma'il Ari sarkin Moriki

    Gwamnan Zamfara a arewacin Najeriya, Bello Matawalle, ya amince da naɗin Alhaji Bashar Isma'il Ari a matsayin Sarkin Burmin Moriki.

    Wata wasiƙa daga ofishin Sakataren Gwmanatin Zamfara Kabiru Balarabe ta ce naɗin nasa zai fara aiki daga ranar 10 ga watan Fabarairu.

    Mai taimaka wa Gwamna Matawalle kan kafofin yaɗa labarai, Jamilu Iliyasu, ya faɗa cikin wata sanarwa a yau Alhamis cewa an naɗa Bashar Isma'il ne bayan masu naɗin sarki a masarautar sun ba shi maki mafi yawa fiye da sauran abokan takararsa.

    Tsohon Sarki Burmin Moriki Alhaji Isma'ila Muhammad Ari II ya rasu ne a ranar 31 ga watan Janairun 2022.

  8. Ɗan Birtaniya ya gurfana a gaban kotu kan zargin yi wa Rasha leƙen asiri

    Wani dan Burtaniya ya gurfana gaban kotu a Landan kan zargin yi wa Rasha leken-asiri.

    David Smith, wanda tsohon jami’in tsaro ne a ofishin jakadancin Burtaniya da ke Berlin, ya musanta tuhume-tuhume tara da aka gabatar a kansa, ciki har da bai wa wani jami’in Rasha a Berlin bayanan sirrin yakar makiya.

    An mayar da shi gidan yari kafin ci gaba da sauraron ƙarar nan gaba.

  9. Dalilan da suka sa kasa ta kasance daya daga cikin abubuwa mafi ban-mamaki a duniya

    Kasa muhimmiya ce a tsarin muhallinmu.

    Ana amfani da ita wajen noma abinci da haɗa magunguna, amma ana nuna mata rashin godiya da kuma barazana.

  10. Kotu ta umarci gwamnatin Najeriya ta bai wa mata 35% na muƙamai

    Wata kotu a Abuja babban birnin Najeriya ta umarci gwamnatin ƙasar ta aiwatar da manufar daidaiton jinsi ta hanyar bai wa mata ikon rike kashi 35 cikin 100 na mukaman gwamnati.

    Da yake yanke hukunci kan karar da wani rukunin mata ya shigar, Mai Shari’a Okorowo ya amince da korafin masu karar wadanda suka ce ana nuna wa mata wariya a wajen nadin manyan mukamai na gwamnati.

    Mai shari’ar ya yi watsi da hujjojin da lauyan gwamnatin ya gabatar na cewa masu karar sun gaza gabatar da hujjar da za ta nuna cewa ana nuna musu wariya.

    Sai dai mai shari’ar ya kafa hujja da sashe na 42 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya domin kare matsayar masu karar, inda ya ce cikin ministoci 44 da ake da su shida ne kawai mata, wanda wannan wariya ce a Zahiri, kuma abin ya fi muni a ma’aikatun gwamnatin.

    Ya ƙara da cewa ba a yi adalci ba ga mata wadanda suka kai miliyan 70 na yawan ‘yan Najeriya.

    An yi ta ihu da murna da waƙe-waƙe a Babbar Kotun Tarayya bayan yanke wannan hukunci da ya yi wa matan Najeriya dadi.

  11. Estonia za ta daina sayen gas daga Rasha

    'Yan kwanaki bayan Lithuania ta sanar da daina sayen iskar gas daga Rasha, Estonia wadda maƙociyarta ce a yankin Baltic ta sanar da ɗaukar irin wannan matakin.

    Gwamnatin ƙasar ta ce tana da zimmar daina amfani da gas ɗin Rasha nan da farkon "lokacin zafi" na wannan shekara.

    Ministocin Estonia sun ce sun cimma yarjejeniya da Finland don ba ta damar shiga da gas ɗin girki.

    "A yau mun ɗauki matakin daina sayen gas ɗin Rasha. Ba zai yiwu mu ci gaba da tallafa wa Rasha ci gaba da yaƙi ba," a cewar Firaministan Estonia Kaja Kallas.

    Duk da cewa kashi 7 cikin 100 na makamashin Estonia ne kawai gas, kusan dukkansa na fitowa ne daga Rasha.

  12. Buhari ya karɓi rahoton kwamatin yi wa tsarin raba kuɗin shiga kwaskwarima

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya karɓi wani rahoto da ya ba shi shawara kan yadda za a yi wa tsarin raba kuɗaɗen shiga tsakanin gwamnatin tarayya da jihohi da kuma ƙananan hukumomi kwaskwarima.

    Buhari ya karɓi rahoton a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja a yau Alhamis.

    Ƙarƙashin tsarin raba harajin da ake amfani da shi a yanzu, gwamnatain tarayya na ɗaukar kashi 52.68 cikin 100 na kuɗaɗen da aka raba, yayin da jihohi ke samun 26.72, sai kuma ƙananan hukumomi da ke karɓar 20.60.

    Tun a Oktoban 2021 kwamatin ya fara aikin lalubo hanyoyin yi wa tsarin gyara wanda ake kira Vertical Revenue Allocation Formula a Turance.

  13. Gwamnan Zamfara ya raba wa sarakunan jihar motocin alfarma '260'

    Gwamnan Jihar Zamfara a arewacin Najeriya, Bello Matawalle, ya raba wa sarakunan gargajiya da ke jihar manyan motocin alfarma.

    Rahoton da kafar Channels TV ta ruwaito ya ce Sarkin Musulmi na Najeriya Sa’ad Abubakar III ne ya raba motocin 260 a gidan gwamnatin Zamfara.

    Gwamnan ya ce an raba motocin ne saboda muhimmancin sarakuna a cikin al'umma da ke a matsayin "turakun al'adu da addini".

    "Mun yanke shawarar ba su sabbin motocin ne saboda yadda gwamnatina ke mutunta sarakunan gargajiya," in ji shi. "Mun raba wa sarakuna 17, da manyan hakimai 13, da kuma hakimai 230 a faɗin jihar."

    Kazalika, gwamnan ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da haɗa kai da sarakunan da kuma shugabannin addini don tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai a jihar.

  14. Shugaban Yemen Mansour Hadi ya sauka daga muƙaminsa

    Shugaban Yemen ya miƙa ikon da yake da shi ga wani kwamitin shugaban kasa na musamman tare da korar mataimakinsa Ali Mohsen al-Ahmar daga mukaminsa.

    Shugaba Abd-Rabbu Mansour Hadi ya ce daga yanzu kwamitin ne zai ci gaba da tafiyar da sha'anin siyasa, da sojoji, da kuma tsaron kasar Yemen.

    Wakilin BBC ya ce a jawabin da ya yi ta talbijin, Shugaba Hadi ya ce sabuwar gwamnati za ta kawo karshen zubar da jinin da ake yi a ƙasar.

    Kwamitin mai mutum bakwai zai yi aiki ƙarƙashin jagorancin tsohon ministan cikin gida Rashad Al-Alimi.

    Tuni Saudiyya ta yi maraba da matakin, tana mai neman sabuwar gwamnati ta tattauna da 'yan tawayen Houthi saboda samun dawwamammen zaman lafiya da kawo karshen yakin basasar shekara bakwai.

  15. CBN ya ci tarar bankuna huɗu saboda sun ƙi rufe asusun cryptocurrency

    Babban Bankin Najeriya CBN ya ci tarar bankunan kasuwanci huɗu a ƙasar saboda saɓa umarnin da ya bayar na haramta gudanar da hulɗa da kuɗin intanet na cryptocurrency.

    Tun a watan Fabarairun 2021 ne CBN ya umarci bankunan da su rufe dukkan asusun da ke mu'amala da cryptocurrency.

    Cikin wani rahoto da kafar yaɗa labarai ta Bloomberg ta ruwaito ranar Laraba, bankunan da aka ci tarar sun haɗa da Stanbic IBTC Bank, da Access Bank, da United Bank for Africa (UBA), da Fidelity Bank.

    Rahoton ya ce an ci tarar Stanbic Bank naira miliyan 200 saboda ya gaza rufe asusu biyu da ake zargin an yi amfani da su wajen hulɗar kuɗin cryptocurrency.

    Kazalika, an ci tarar Access Bank naira miliyan 500 saboda ya ƙi rufe asusun crypto, yayin da aka ci tarar UBA naira miliyan 100. Sai kuma Fidelity Bank da aka ɗora wa tarar miliyan 14.

  16. Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da kai hari kan sojoji a Kaduna

    Ministan Yaɗa Labarai a Najeriya Lai Mohammed ya tabbatar da kai hari kan sansanin sojan ƙasar da 'yan bindiga suka kai a Jihar Kaduna.

    Ministan ya ce duk da cewa kafofin yaɗa labarai da dama sun ruwaito harin amma sun gaza wajen ruwaito yadda sojojin Najeriya suka fatattaki maharan.

    Sojoji aƙalla 11 rahotanni suka ruwaito an kashe a harin na ranar Lahadi lokacin da maharan suka far wa sansanin nasu da ke yankin Birnin Gwari.

    Kazalika, an ƙona motocin soja masu sulke uku.

    "Tabbas an kai hari kan sansanin soja a Kaduna amma abin da 'yan jarida ba su rawaito ba shi ne yadda aka daƙile harin da kuma ɓarnar da aka yi wa 'yan ta'addan," in ji ministan bayan kammala zaman Majalisar Zartarwa a jiya Laraba.

    Sai dai ministan bai bayyana adadin sojojin da aka kashe ba.

  17. Amurka za ta bai wa sojojin Ukraine horo na jirgi marasa matuƙa

    Amurka ta ce ta bai wa wasu daga cikin sojin Ukraine horon yadda za su sarrafa jirgi maras matuki da ke kakkaɓo tankar yaƙi mai suna Switchblade.

    Jirgin da ke tashi sama tare da sakar bam a inda aka saita shi, zai yi matukar tasiri a yakin.

    Wakilin BBC ya ce sojojin Amurka sun yi amfani da jiragen marasa matuka a Afghanistan, kuma yawancinsu na ɗauke da isassun ababen fashewa da sai a mota mai silke za a iya ɗaukarsu.

    Kakakin ma'aikatar tsaron Amurka, John Kirby, ya ce sojin Ukraine da suke Amurka gabannin mamayar Rasha aka koya wa yadda za su sarrafa jiregen.

  18. Barka

    Maraba da sake haɗewa a shafinmu na rahotanni kai-tsaye. Za mu kawo labaran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, musmaman a Najeriya da kuma halin da ake ciki a Ukraine.

    Ku biyo ni Umar Mikail a wannan hantsi na Alhamis.