Kotu ta wanke Sanata Abba Moro, ta daure wani babban sakataren ma'aikatar cikin gida kan badakkalar daukan ma'aikata

Asalin hoton, facebook / Abba Moro
Wata babbar kotu a Abuja ta wanke Sanata Abba Moro da wasu mutum biyu kan tuhumar da aka yi musu ta badakkalar daukan ma'aikatan hukumar shige da fice a 2014.
Alkalin kotun Nnamdi Dimgba ya yanke hukunci a shari'ar, yana cewa hukumar da ke yaki da masu yi ma tattalin arziki zagon kasa, EFCC cewa ta gaza gamsar da kotu cewa mutanen da aka gurfanar sun aikata laifukan.
Abba Moro tsohon ministan harkokin cikin gida ne a wancan lokacin, kuma an gurfanar da shi a gaban shari'a ne tare da babbar sakatariyar ma'aikatar shige da fice Mrs Anastasia Daniel-Nwobia, da wani tsohon darakta a ma'aikatar mai suna Felix Alayebami da kuma wani kamfani Drexel Tech Nigeria Ltd.
An dai tuhumi mutanen ne da hada baki su aikata lafukan da suka hada da halarta kudin haram, da kuma damfara, yayin da aka gudanar da wani aikin daukar sababbin ma'aikatan hukumar ta shige da fice.
A karshe dai rikici ya barke inda saboda wata mummunar turreniya, wasu masu neman aiki 14 suka rasa rayukansu.
















