Twitter zai toshe wasu shafukan gwamnatin Rasha
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.
Rahoto kai-tsaye
Sani Aliyu
Sharuɗɗan da Inec ta gindaya jam’iyyun siyasa a Najeriya

Asalin hoton, KOLA SULAIMON
Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Nijeriya (INEC) ta ce jazaman ne jam'iyyun siyasar ƙasar su yi aiki sau da ƙafa da tsarin dimokraɗiyya a cikin gida, wajen gudanar da zaɓukansu na fid da gwani gabanin babban zaɓen ƙasar da ke tafe.
An kashe wani malami a harin Masallaci a Iran

Wani hari da aka kai da wuka a wani Masallaci a Iran ya yi sanadin mutuwar wani malami tare da jikkata wasu biyu.
'Yan sandan Iran sun ce sun kama maharin ne a harabar hubbaren Imam Reza da ke birnin Mashhad.
Sun ce ana binciken asalinsa, amma sun nuna cewa ɗan ƙasar waje ne.
Twitter zai toshe wasu shafukan gwamnatin Rasha

Asalin hoton, Reuters
Twitter ya ce zai toshe shafuka sama da 300 na gwamnatin Rasha, ciki har da na shugaba Vladimir Putin.
An zargi shafukan da yaɗa labaran ƙarya kan yakin Ukraine, kuma tun abka wa Ukraine da Rasha aka taƙaita Twitter a Rasha.
Kamfanin ya ce zai ɗauki mataki kan duk wata ƙasa da ta taƙaita amfani da intanet yayin da take fagen yaƙi.
Twitter zai naɗa Elon Musk cikin manyan daraktocinsa
Kamfanin Twitter ya ce zai nada hamshakin attajirin na dan Amurka, Elon Musk cikin manyan daraktocinsa.
Mista Musk ya kasance wanda ya fi yawan hannnu jari a kamfanin na sada zumunta a yanzu, bayan ya sayi kashi 9.2 cikin 100 na hanayen jarin kamfanin.
Twitter ya ce manufofi da burin Mista Musk sun zo daidai da muradan kamfanin – sai dai ya kara da cewa hannayen jarin Mista Musk ba zai zarta kashi 14.9 ba cikin 100 muddin ya cigaba da kasancewa cikin daraktocinsa.
Daraja da Hanayen jarin Twitter nata karuwa bayan Mista Musk ya fitar da wannan sanarwa.
Iran ta ce Saudiyya ba ta gayyace ta shirye-shiryen aikin Hajjin bana ba

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar kula da aikin Hajji ta Iran ta ce Saudiyya ta gayyaci wasu ƙasashen Musulmi game da shirin aikin Hajjin bana amma ba tare da ta gayyace ta ba.
Hukumar ta ce watanni uku da suka rage a soma akin Hajji, ta tura wa hukumomin Saudiyya wasiƙa game da halin da ake ciki kan aikin Hajjin bana.
Har yanzu Saudiyya ba ta bayyana sharuɗɗan aikin Hajjin bana ba, amma ƙasashe da dama sun fara shiri.
Shugaban hukumar kula da aikin Hajji ta Iran ta ce tun 2016 da kuma kafin ɓarkewar annobar korona, Saudiyya ba ta gayyaci Iran ba. Harin da aka kai wa ofishin jekadancin Saudiyya a Tehran da kuma kone shi a 2015 ya ƙara lalata dangantaka tsakanin Saudiyya da Iran.
An samar da ruwan Zamzam lita rabin miliyan na buɗa baki a Masallacin Makkah

Asalin hoton, @theholymosques
Hukumomin da ke kula da Masallatai biyu mafi daraja sun ce an samar da ruwan Zamzam lita rabin miliyan domin masu azumi a Masallacin Harami.
Kamfanin dillacin labaran Saudiyya SPA ya ambato, shugaban ɓangaren da ke kula da ruwan Zamzam Abdul Rahman Al-Zahrani ya ce akwai guda 100,000 na Zamzam da aka samar na roba da kuma 13,000 babbar gora da ya kai lita 40 da aka samar domin masu buɗa baki a Masallacin Makkah.
Sannan an samar da ruwan Zamzam na roba 160, 000 a Masallacin Madina da kuma 14,000 na gora a sassan Masallacin.
Ƴan sanda sun ce an sako ɗaliban Jami’ar jihar Abia

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta tabbatar da cewa an sako daliban jami’ar jihar Abia da aka yi garkuwa da su.
Tun farko hukumar gudanarwar jami’ar jihar Abia, da ke Uturu, ta tabbatar da sace dalibanta da ba a tantance adadinsu ba da wasu ‘yan bindiga suka yi a hanyar Okigwe zuwa Uturu kwanaki biyu da suka gabata.
Nato na nazarin sake aika wa Ukraine ƙarin makamai
Sakatare Janar na kungiyar tsaro ta Nato, ya ce kungiyar na duba yiwuwar sake aika Karin makamai domin taimakawa Ukraine a yakin da take da mamayar Rasha a kasarta.
Ya ce aikin Nato ne ta taimakawa Ukraine kuma suna yin haka da taimakon makamai na zamani, da kudade da taimakon soji da kuma agaji.
Jens Stoltenberg ya yi gargadin cewa Moscow ba ta da niyyar tsagaitawa, sannan babban burinta a yanzu shi ne ta karbe ikon ilahirin yakin Donbass da ke gabashi nan da makonni masu zuwa.
Rundunar sojin Ukraine ta ce dakarun Rasha na sake gina kansu a kokarin kai sabbin farmaki, sannan rahotanni da ake samu na baya-bayanan na cewa suna ta ruwan wuta a birane irinsu Kharkiv da Luhansk da Donetsk.
Kokarin kwashe fararan-hula daga yankunan da ake yaki na fuskantar cikas.
Burin Rasha shi ne kwace 'daukacin yankin Donbas' na Ukraine - shugaban Nato

Asalin hoton, EPA/STEPHANIE LECOCQ
Sakatare Janar na kungiyar Nato Jens Stoltenberg ya ce Rasha ba ta yi sanyin-gwiwa ba game da mamayar da take yi wa Ukraine amma za ta yi kokarin mayar da hankali kacokan wajen kwace lardin Donbas baki daya nan da makonni masu zuwa.
"Mun ga karin kazar-kazar din dakarun Rasha wajen barin Kyiv domin sake haduwa, su kara makamai da kuma mayar da hankali gabashin kasar," a cewarsa Stoltenberg a wajen taron manema labarai a Brussels.
"Nan da makonni masu zuwa, muna sa ran Rasha za ta zakuda zuwa gabashi da kudanci Ukraine domin kokarin kwace baki dayan Donbas da kuma samar da wata gada ta kasa zuwa yankin Crimea da aka mamaye," in ji shi a taron da ya yi da ministocin wajen kasashen Nato.
Dakarun Rasha sun kwace yankin Crimea da ke kudancin Ukraine shekara takwas da suka gabata.
Mubarak Bala ya amsa laifin aikata saɓo a gaban kotu

Bayanan hoto, Mubarak Bala Wata babbar kotu a Kano da ke arewacin Najeriya ta sake aike wa da Mubakar Bala zuwa gidan gyaran hali, saboda ci gaba da tsare rayuwarsa da kuma gazawar lauyoyinsa na gabatar wa kotun da cikakaken takardun da za su tabbatar mata cewar yana fama da rashin lafiya.
An karanto wa Mubarak Bala caji 14 da ake tuhumarsa a kai na yin sabo.
Yayin zaman kotun, an karanto masa sakonnin da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na Facebook, wadanda ya yi kalaman batanci ga addinin Musulunci.
Ya amsa dukkan caji 14 da aka karanto masa da cewar ya aikata dukkan laifukan da ake tuhumarsa da aikatawa.
Ganin haka sai lauyansa ya roki kotun ta ba shi damar ganawa da wanda yake wakiltar, wato Mubarak Bala, kuma bayan ta amince, ya yi kokarin nuna ma sa tasirin cewa ya amsa dukkan laifukan da ake tuhumarsa.

Bayanan hoto, Mubarak Bala Amma bayan da lauyan ya sanar da kotun cewa Mubarak Bala na son sauya amsar da ya bayar a gaban kotun, sai alkalin ya sake tambayar wanda ake tuhumar ko haka lamarin yake.
Mubarak Bala ya sanar da kotun cewa ba zai sauya amsa laifinsa da ya yi a gaban kotun ba.
Alkali kotun ya tambaye shi ko ya fahimci nauyin abubuwan da yake cewa, kuma wanda ake tuhumar ya amsa cewa ya fahimci komai.
Ya kara da cewa babu wanda ya tursasa masa don ya amsa dukkan laifukan da ake tuhumarsa da aikatawa. Sannan ya ce babu wanda yayi masa wani alkawari, ko ya sanya masa wani ra’ayi, sai dai ya bukaci kotun ta yi masa sassauci da kuma adalci.
Wakilin BBC da ke kotun ya ce kotun na ci gaba da sauraron shari'ar.
Wani dan kwallon Tennis ya mari abokin karawarsa saboda zafin kayen da ya sha
Masu kallon wasan Tennis a Ghana sun ga abin mamaki yayin da wani dan wasan da ya sha kaye ya mari abokin wasansa a kunchi a jim kadan bayan karashe wasan nasu a birnin Accra na Ghana.
Dan wasan mai suna Michael Kouamé dan kasar Faransa wanda ke da shekara 15 da haihuwa ya mari Raphael Nii Ankrah dan kasar Ghana, mai shekara 16 da haihuwa yayin da suke gaisawa da juna a tsakiyar filin wasan, matakin da ya ba 'yan kallo mamaki:
Kauce wa XYa kamata a bar bayanan X?Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Kawo yanzu dai babu wata sanarwa da masu shirya gasar suka fitar kan halayyar dan Faransar.
Sai dai Ankrah zai kara da Ishmael Nii Nortey wanda shi ma dan kasar Ghana ne a zagaye na gaba.
'Yan bindiga sun kashe sojojin Najeriya 11 a wani sansaninsu a Kaduna

Asalin hoton, Reuters
Kimanin sojoji 11 sun rasa rayukansu yayin wani hari da wasu 'yan bindiga suka kai kan wani sansanin sojojin Najeriya a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna, kamar yadda jaridar TheCable ta wallafa.
Daruruwan 'yan bindigan sun isa sansanin ne a kusa da kauyen Polwire a jiya Litinin kuma sun dauki wani lokaci suna musayar wuta da sojojin da ke cikin barikin.
Wata majiya daga rundunar soji Najeriya na cewa 'yan bindigan sun isa sansanin ne bisa babura dauke da manyan makamai, ciki har da bindiga mai harba gurnati.
Majiyar ta ce an shafe sa'a biyu ana gwabzawa kafin 'yan bindigan suka iya kore sojojin daga cikin sansanin.
"Mun rasa sojoji 11 kuma an raunata 19 yayin harin. Maharan sun kuma kona wasu motoci masu sulke uku bayan da suka mamaye sansanin", inji wani jami'in sojojin Najeriya.
Majiyar ta kuma ce maharan sun kwashe makamai masu dama daga sansanin.
An kai sojojin da aka raunata zuwa babban asibitin Birnin Gwari da asibitin sojojin sama, yayin da aka kai gawarwakin wadanda suka mutu zuwa asibitin 44 da ke birnin Kaduna.
Sai dai ba a sami jin ta bakin kakakin rundunar sojin Najeriya Onyema Nwachukwu ba kan halin da ake ciki a yankin na Birnin Gwari bayan wannan mummunan harin.
An nada Sheikh Nuru Khalid limamin wani masallaci a Abuja

Asalin hoton, Sheik Nuru Khalid
Bayanan hoto, Sheik Nuru Khalid Malamin addinin Musuluncin nan da aka kora daga limancin masallacin unguwar Apo saboda ya soki gwamnatin Najeriya ya sami wani sabon aikin na limanci a Abuja.
Kwamitin wani sabon masallacin Juma'a a Abuja ya nada shi a matsayin sabon limamin masallacin.
Sanata Sa'idu Dansadau, wanda shi ne shugaban kwamitin masallacin 'yan majalisu da ke unguwar Apo ne ya kori Sheikh Nuru Khalid saboda bai yi nadamar kalaman da ya fada a hudubarsa ta ranar Juma'a ba.
A ranar ce Sheikh Nuru ya caccaki gwamnati kan yadda ta bari wasu 'yan bindiga suka kai wani mummunan hari kan wani jirgin kasa da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna a arewacin Najeriya.
Cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafukan sada zumunta, limamin ya sanar cewa, "Ina son sanar muku cewa mun sami wani sabon masallaci, kuma daga ranar Juma'a mai zuwa za mu bude shi. Ga wadanda ke ganin an hana mu wurin yin wa'azi, to su sani cewa mun sami wata sabuwar cibiya."
Sheikh Khalid ya kara da cewa: "Ko a jiya wani malami addinin Kirista ya kira ni kuma ya sanar da ni cewa ya saka bidiyon hudubar da nayi ta ranar Juma'a ga mambobin cocinsa domin su saurari abin da na ce. Hudubata a masallaci ta fusata wasu mutane, amma wasu mutanen sun yaba min a cocinsu kan hudubar."
Ya kuma ce maimakon ya ji haushin wadanda suka kore shi kan hudubar, yana tausaya musu ne.
Gwamna Soludo: Ku ba mu bindigoginku, mun yi alkawarin taimaka muku

Asalin hoton, Charles Soludo
Bayanan hoto, Gwamnan jihar Anambra, Charles Soludo Gwamnan jihar Anambra a yankin kudu maso gabanshin Najeriya ya sanar cewa daga Litinin din wannan makon, an kawo karshen hana jama'ar jihar fita wuraren aiki da sana'o'insu a fadin jihar.
Gwamnan ya kuma sanar da cewa gwamnatinsa ta yi ma mutanen da ke dauke da makamai afuwa, musamman wadanda ke yin kira da a raba Najeriya gida biyu kuma a kafa kasa ta 'yan yankin zalla.
Farfesa Charles Soludo ya sanar da haka cikin wata sanarwa, inda ya jaddada cewa zai dawo da zaman lumana a jihar.
Wasu mayaka, wadanda mambobin kungiyar IPOB ne - kungiyar da gwamnatin Najeriya ta haramta ma aiki a Najeriya - sun rika kai hare-hare a jihar ta Anambra da yankin kudu maso gabashin Najeriya.
Mambobin kungiyar na son a sako shugabansu Mazi Nnamdi Kanu.
"Mun yi ma 'yan uwanmu wadanda ke cikin dazukan jiharmu afuwa. Ku mika mana bindigoginku, kuma ku amince mana mu taimaka muku gina rayuwa mai afani", inji gwamna Soludo.
Hotunan yadda aka wayi gari a Ukraine a yau Talata

Asalin hoton, reu
Bayanan hoto, Wasu tankoki yaki na Rasha da aka lalata a garin Bucha bayan da dakarun Rasha suka janye 
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, An gano wani wagegen rami dauke da gawarwakin 'yan Ukraine kusa da wani coci a garin Bucha 
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Ga wata motar da aka lalata baki daya a Bucha 
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, A nan ana raba wa mazauna Bucha tallafin abinci ne 
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Yadda aka binne wani dan jarida dan Ukraine a birnin Kyiv 
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Wani dan Ukraine na shuka furanni a wajen wani gidan da aka lalata a birin Mariupol An sanya wa wasu jarirai da aka haifa a Ukraine sunan wani makamin Birtaniya

Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Dakarun Ukraine yayin da suke fareti inda suke rike da rokokin Javelin na Birtaniya An sanya ma wasu jarirai biyu da aka haifa a cikin Ukraine sunayen wasu rokokin yaki na Birtaniya, kamar yadda wasu kafofin yada labarai na Ukraine ke cewa.
Jariran biyu namiji da mace ne, kuma an sanya ma namijin Yan Javelin, ita macen kuma an sanya ma ta Javelina.
An yi rajistar wadannan sunayen ne a Vinnytsia Oblast kamar yadda matar tsohon shugaban Ukraine Kateryna Yushchenko ta sanar, wadda ta ce alama ce ta yabon da 'yan Ukraine ke ma kasashen yammacin Turai saboda makaman da suke tura ma kasar.
Budewa
Barka da shigowa shafinmu na rahotanni kai-tsaye daga BBC Hausa.
Sani Aliyu ne zai kawo muku abubuwan da ke faruwa a sassan duniya tun daga wannan hantsi na Talata har zuwa yammacin yinin. Sai ku kasance tare da BBC Hausa.
