Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Ko tarihi zai maimaita kansa tsakanin Ghana da Uruguay?

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Umaymah Sani Abdulmumin

  1. Rufewa

    Anan nake bakwana da ku sai kuma gobe da yardar Allah...Umaymah Sani Abdulmumin ke muku fatan alheri. A kwana lafiya.

  2. Labarai da dumi-dumi, An ga watan Azumin Ramadan a Najeriya

  3. Sarkin Musulmi ya gargaɗi Malamai da Limamai su bi dokoki shari'a a Tafsiran Azumi

    Sarkin Musulmi a Najeriya, Sultan Muhammad Sa'ad Abubakar ya yi kira ga dukkan Malamai da Limamai su mutunta dokoki da tsarin addinin Musulunci wajen gudanar da wa'azi ga dukkan darussa addini cikin watan Ramadan.

    Sanarwa da ya fitar dauke da sa hanun wazirin Sokoto, Farfesa Sambo Wali Junaidu, ta kuma umarci malamai suke lura da tsaro da dokokin Korona a lokacin gudanar da Tafsirai da wa'azi.

    Sarkin ya kuma yi kira ga al'umma Musulmi su mayar da hankali wajen yi wa kasa addu'a don samun zaman lafiya da aminci cikin kwanciyar hankali da tsaro.

  4. Nasir El-Rufai - 'Yan bindiga na iya ta da Najeriya baki ɗaya

    Gwamnan jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya, Nasir Ahmed El-Rufai ya ce 'yan Boko Haram ne suka tsara tare da aiwatar da hari kan jirgin kasa a Abuja zuwa Kaduna a jiharsa.

    Gwamna ya bayyana haka ne a wannan Juma'a lokacin da ya ke yiwa manema labarai bayani kan sakamakon ganawarsu da Shugaba Muhammadu Buhari a fadarsa.

    El-Rufai ya ce harin ya yi sanadi mutuwar aƙalla Fasinjoji takwas da raunatar wasu 40 da kuma garkuwa da wasu da ba a san adadinsu ba.

    Ya kuma shaida cewa an samu tattaunawa tsakanin iyalai da wadanda aka yi garkuwa da su, sai dai har yanzu 'yan bindigar ba su tambaye kuɗi ba, illa daga wajen mutum guda.

    Amma gwamnan ya ce yana zargin watakil daga wajen gwmanatin za su neman diyya, ba daidaikun mutane ba ko iyalansu.

  5. 'Yan bindiga sun kashe mutum 17 a Zamfara

    'Yan bindiga sun kashe aƙalla mutum 17 a wasu hare-hare da suka kai kauyuka hudu da ke karamar hukumar Anka ta jihar Zamfara.

    Mazauna yankunan sun ce 'yan bindigar sun bude wuta kan mai uwa-dawabi a kauyen Kadaddaba da tsakar rana.

    Rahotanni na cewa sun isa kauyukan ne akan babura suka buɗe wa mutane wuta lokacin da suke fitowa daga masallaci bayan sallah Azahar.

    Har yanzu dai rundunar 'yan sanda ba su yi tsokaci ba kan hare-haren.

  6. England v USA

    Wannan ne karo na uku da Ingila za ta hadu da Amurka a kofin duniya a mataki na rukuni,, sun hadu a 1950 sai kuma 2010.

    Wannan ne karo na uku da Ingila ke haduwa da wata kasa sau uku a gasar kofin duniya daban-daban.

    Ingila ta ci 8 daga cikin wasannin da ta yi 11 da USA ta yi canjaras 1 ta kuma yi rashin nasara 2, amma duka nasara 8 din da ta yi a wasannin sada zumunta ne.

  7. Labarai da dumi-dumi, Wasan farko da za a buga a gasar cin kofin duniya ta 2022 za a yi tsakanin Qatar da Ecuador...

  8. Ko tarihi zai maimaita kan sa tsakanin Ghana da Uruguay 😉?

    Za a sake haduwa tsakanin Ghana da Uruguay, masana da magoya baya ba za su kasa mantawa da kwallon da Suarez.

    Kwallon da ta hana Black Stars zuwa wasan kusa da na karshe a 2010.

    Tarihi mara dadi ga mutanen Ghana

  9. An kammala raba rukunin gasar cin kofin duniya da za a yi a Qatar

    Rukunin A: Qatar, Ecuador, Netherlands, Senegal

    Rukinin B: England, Iran, USA, Scotland/Wales/Ukraine

    Rukinin C: Argentina, Saudi Arabia, Mexico, Poland

    Rukinin D: France, UAE/Australia/Peru, Denmark, Tunisia

    Rukinin E: Spain, Costa Rica/New Zealand, Germany, Japan

    Rukinin F: Belgium, Canada, Morocco, Croatia

    Rukinin G: Brazil, Serbia, Switzerland, Cameroon

    Rukinin H: Portugal, Ghana, Uruguay, South Korea

  10. Rukunin H

    Portugal

    Uruguay

    South Korea

  11. Rukunin A ya cika

    Qatar

    Senegal

    Netherlands

    Ecuador

  12. Rukunin D ya cika

    France

    Denmark

    Tunisia

    UAE/Australia/Peru

  13. Rukunin F

    Belgium

    Morocco

    Croatia

  14. Rukunin E

    Spain

    Germany

    Japan

  15. Rukunin D

    France

    Denmark

    Tunisia

  16. Rukunin C

    Argentina

    Mexico

    Poland

  17. Rukunin B

    England

    Iran

    USA

  18. Rukunin A

    Qatar

    Senegal

    Netherlands

  19. Masu horaswa sun iso dakin taro

    Abin sha'awa manyan kociyoyi sun fara karasawa dakin taron da za a raba rukunin kasashen da za su gasar cin kofin duniya a Qatar.

    Kocin Faransa Didier Deschamps wanda ke rike da kofin duniya a isa wajen... daki ya dauki harama

  20. Watakila wannan ne World Cup na karshe da Messi da Ronaldo za su halarta

    Wannan gasdar za ta iya zama ta karshe da Messi da Ronaldo za su iya halarta.

    A gasar da za a yi mai zuwa da za a yi a North America Ronaldo zai kai shekara 41 da haihuwa a duniya.

    Si kuwa dan wasan Argentina Messi zai cika 39 a lokacin.

    Shi akwai alamar daya daga cikinsu zai iya cin gasar a karon farko a tarihi?