Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

China ta ce za ta bunƙasa dangantakarta da Rasha

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya

  1. An ji karar makaman atilari ta karade gefen birnin Kyiv

    An ji karar fashewar abubuwa kusa da birnin Kyiv a safiyar nan.

    Wakiliyarmu kan kasashen duniya Lyse Doucet ta ce lamarin ya soma ne da jin karar amsa-kuwwa, da kuma manyan kararraki daga wajen birnin wadanda ta ji daga tsakiyar birnin.

    Kazalika Jeremy Bowen, wanda shi ma yana birnin Kyiv, ya wallafa sakon Tuwita da ke cewa "an ji karar makaman atilari ta mamaye gefe zuwa tsakiyar birnin".

    Babu tabbas kan ko dakarun Rasha ko na Ukraine ne suka yi harbe-harbe, a cewarsa.

    A jiya bayan tattaunawar sulhu, Rasha ta ce za ta rage ayyukanta a kusa da babban birnin - alwashin da shugabannin kasashen Yamma suka yi kira a yi kaffa-kaffa da shi.

  2. Ikirarin Rasha na tsagaita wuta a yakin Ukraine yaudara ce - Babban jami'in soji

    Wani babban jami'in rundunar sojin Ukraine ya ce alwashin da Rasha ta yi na janyewa daga kasar yaudara ce kawai.

    A wani jawabi da yake wallafawa a shafinsa na Facebook a kullum game da yakin na Rasha da Ukraine , babban jami'in sojan ya ce dakarun Rasha suna ci gaba da janyewa daga Kyiv da Chernihiv. Tuni Rasha ta ce za ta mayar da hankali zuwa lardin Donbas da ke gabashin kasar.

    Rundunar sojin Ukraine ta yi amannar cewa Rasha tana janyewa ne "domin bai wa wasu jami'anta sauya wurin yaki" kuma ta ce za ta tsagaita wutar ne da zummar yaudarar shugabannin sojin Ukraine da kuma kirkiro wani "salon yaudara" .

    Bayanin nasa ya yi daidai da wanda kakakin Pentagon John Kirby, ya yi inda ya ce har yanzu akwai barazanar kai hari a Kyiv duk da janyewar da dakarun Rasha suke yi daga birnin.

  3. Barkanmu da warhaka

    Nasidi Adamu Yahaya ne yake tare da ku a wannan hantsi. Da fatan za ku biyo mu domin sanin halin da duniya take ciki a wannan rana ta Laraba wadda Hausawa ke yi wa kate Tabawa ranar samu.

    Za mu kawo maku labarai da rahotanni kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.

    Za mu mayar da hankali kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtanta da Rasha da Ukraine, da ma wasu sassan duniya.