Saudiyya za ta samar da abincin buɗa baki ga Musulmi a ƙasashe 34
Saudiyya za ta ƙaddamar da shirin buɗa baki a ƙasashe 34, kamar yadda kamfanin dillancin labaran ƙasar ya ruwaito a ranar Lahadi.
Manufar shirin shi ne samar da abincin buɗa baki ga Musulmi a cikin watan Ramadan, wanda ake fatan soma wa a ranar 2 ga watan Afrilu.
Ana sa ran mutum miliyan 1.2 za su ci gajiyar shirin.
Rahotannin sun ce Ma'aikatar kula da harkokin addinin musulunci, ta yi dukkanin shirye-shiryen da suka wajaba domin ganin shirin ya shafi ɓangarorin duniya, ko da yake ya dogara daga neman bukatar.
Za a aiwatar da shirin ne tare da hadin gwiwar ofisoshin jakadancin Saudiyya da cibiyoyin addinin Musulunci na ma'aikatar.