Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Taron APC: Dukkan 'yan takara sun janye wa mutum ɗaya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.

Rahoto kai-tsaye

Awwal Ahmad Janyau and Umar Mikail

  1. Ƙungiyar Izala ta roƙi Buhari ya buɗe rumbunan abinci albarkacin Ramadan

    Ƙungiyar Izala a Najeriya ta yi kira ga shugaban ƙasar Muhammadu Buhari da ya buɗe rumbunan abinci da kuma rage farashi domin al’umma su ji saukin lamura a watan Ramadan.

    Shugaban kungiyar Sheikh Abdullahi Bala Laune ya yi wannan kira a jiya lokacin buɗe Masallacin Juma’a na ƙungiyar a Abuja.

    Ƙungiyar ta ce an gina Masallacin ne da kuɗin fatar da jama’a suka bayar a lokacin layya.

    Sheikh Bala Lau ya ce ya shaida wa shugaba Buhari wanda ya halarci bikin buɗe Masallacin cewa ya kamata gwamnatinsa ta sa ido ta tabbatar da ba a tsawwala farashin kayayyaki ba, kamar yadda ya shaida wa BBC.

  2. Ukraine ta ce yara 136 aka kashe zuwa yanzu

    Ofishin babban mai shigar da ƙara a Ukraine ya ce yara 136 aka kashe kawo yanzu a yaƙin da ƙasar ke yi da Rasha.

    Ya ƙara da cewa adadin yaran da aka raunata sun kai 199.

    BBC ba za ta iya tantance gaskiyar wannan iƙirarin ba.

  3. Maraba

    Muna maku maraba da kasancewa da mu a wannan shafin da muke kawo maku labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.

    Sai ku kasance da mu