Ƙarshen rahotannin kenan
Mun kawo ƙarshen rahotanni a wannan shafi na kai-tsaye, amma za mu kawo muku sakamakon abin da aka samu a wajen taron na APC da ke gudana yanzu haka a wani shafin daban.
Umar Mikail ne ke muku fatan alheri.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.
Awwal Ahmad Janyau and Umar Mikail
Mun kawo ƙarshen rahotanni a wannan shafi na kai-tsaye, amma za mu kawo muku sakamakon abin da aka samu a wajen taron na APC da ke gudana yanzu haka a wani shafin daban.
Umar Mikail ne ke muku fatan alheri.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya isa filin taron jam'iyyar APC mai mulki.
Bayan kammala taken Najeriya ne kuma shugaban ya kama wuri ya zauna.
Tuni Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo ya isa wurin.
'Yan takarar shugabancin jam'iyyar APC mai muilkin Najeriya na ƙasa sun amince su bar wa mutum ɗaya muƙamin, a cewar Gwamnan Nasarawa Abdullahi Sule.
Gwamnan wanda shi ne shugaban ƙaramin kwamatin yaɗa labarai na taron APC, ya faɗa wa BBC Hausa cewa tuni suka karɓi jerin sunayen waɗanda suka amince ɗin da gwamnonin yankunansu, wanda suka yi wa laƙabi da Unity List a Turance.
"Ai da ma amfanin Unity List shi ne kowane ɓangare ya je ya zauna da gwamnansa da 'yan takarar su amince da ɗan takara ɗaya," in ji shi.
"Yanzu haka maganar da nake maka muna da jerin sunayen duk waɗanda suka amince, kowa ya zmince."
Sai dai bai ambaci sunan ɗan takarar da suka janye wa ba. Amma tun farko 'yan takara shida sun janye wa Sanata Abdullahi Adamu, tsohon Gwamnan Nasarawa, wanda ke samun goyon bayan Shugaba Buhari.
Sai dai har yanzu filin taron cike yake maƙil da jama'a daga kowace jiha a Najeriya, yayin da wakilai fiye da 7,000 ke shirin kaɗa ƙuri'unsu idan ta kai ga yin zaɓe.
Jagororin taron sun faɗa wa BBC Hausa cewa za su fifita masalaha kan jefa ƙuri'a.
Daga yau zuwa gobe Lahadi ake sa ran APC za ta zaɓi dukkan shugabanninta da kuma 'yan majalisar ƙoli wato National Working Committe (NWC).
Shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana Shugaban Rasha Vladimir Putin a matsayin 'Mahauci' yayin wata tattaunawarsa da 'yan gudun hijrar Ukraine a Poland.
Biden ya yi wannan kalami ne yayin wani shirin talabijin da ya gudana a birnin Warsaw a wata ziyarar nuna goyon baya ga Poland kan taimakon da take yi wa Ukraine.
Wakilin BBC ya ce wani dan jarida ya tambayi Biden game da yadda yake kallon abin da Putin ke yi wa mutanen Ukraine, sai ya ce Putin ya zama 'mahauci'.
Tun da fari sai da Biden ya tattauna da takwaransa na Poland Andrzej Duda.
Shugaban Amurka Joe Biden ya ce yana ganin shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi mamakin ganin ya kasa raba hankalin Nato kan mamayar da ya yi wa Ukraine.
Biden na magana ne a ziyarar da ya kai a Warsaw babban birnin Poland inda ya gana da ministocin gwamnatin Ukraine da kuma shugaban Poland Andrzej Duda.
“Na tabbata cewa Vladimir Putin yana lissafin zai iya raba hankalin Nato, ta hanyar raba gabashi da yammaci, da koƙarin raba ƙasashe ta amfani da tasiri.”
“Amma ya kasa – muna nan a haɗe wuri ɗaya,” in ji Biden
Muna kawo muku yadda take kasancewa a filin babban taro na jam'iyyar APC mai mulki na ƙasa a shafinmu na Facebook kai-tsaye.
Ya zuwa yanzu ba a kai ga fara kaɗa ƙuri'a ba.
Amma rahotanni na cewa 'yan takara shida sun janye wa Sanata Abdullahi Adamu, wanda shi ne Shugaba Muhammadu Buhari yake mara wa baya a takarar.
Muna samun rahotannin da ke cewa an ji fashe-fashen abubuwa a yammacin birnin Lviv na Ukraine.
Wannan hoton da ke ƙasa na nuna hayaƙi na tashi daga nesa
Za mu kawo ƙarin bayani da zarar mun samu.
Jami’an tsaro sun cafke wasu mutum uku da ake zargi da yankan aljihu a wajen babban taron jam’iyar APC da ke gudana a Abuja, bayan kama su suna satar wayar salula a kofar shiga filin taron.
Wani jami’in tsaro ya faɗa wa kamfanin labara na Najeriya NAN cewa waɗanda aka Kama ɗin sun faki idon dandazon mutane da ke kofar shiga filin taron na Eagle Square wajen sace wayoyinsu.
Jami’in tsaron ya kuma ce waɗanda ake zargi da sace wayoyin sun haɗa baki wajen aiki tare, inda suke sace wayoyi da kuma kuɗin mutane da ke filin taron.
Har wa yau, jami’in tsaron ya ce an samu damar kama mutanen ne da taimakon sauran abokan aikinsu 'yan sanda da ke sanya ido a kofar shiga Eagle Square yayin da wakilai ke shiga domin kaɗa kuri’arsu.
Ya ce za a kai waɗanda ake zargin zuwa shelikwatar ‘yan sanda domin ci gaba da bincike.
Rundunar sojan Najeriya ta ce dakarunta sun gano ɓaraguzan jirgin samanta na Alpha Jet (NAF475) da ya ɓace ranar 31 ga watan Maris na 2021.
Wata sanarwa da rundunar ta fitar a yau Asabar ta ce dakarunta na Operation Desert Sanity ne suka gano jirgin a Dajin Sambisa da ke Jihar Borno.
Jirgin na ɗauke da mutum biyu a lokacin da ya ɓace, a cewar rundunar.
Ta ƙara da cewa tana ci gaba da bincike.
Gwamnatin Kaduna ta tabbatar da afkuwar wata fashewa, inda bam ɗin da ya tashi a Ƙaramar Hukumar Igabi ya raunata mutum biyu ranar Asabar.
Wata sanarwa daga ma'aikatar tsaron cikin gida ta ce lamarin ya faru ne a Hayin Danmani lokacin da bam ɗin ya tarwatse a jikin wani babur mallakar wani mai suna Mohammed Hassan da ke sana'ar cire kuɗi a na'urar POS.
Rahoton ma'aikatar tsaron ya ce bayan mutumin ya tashi daga aiki ne kuma ya nufi babur ɗinsa don ya tafi gida, yana buga babur ɗin sai bam ɗin ya tashi da shi.
Ta ƙara da cewa fashewar ta ji wa Mohammed mummunan rauni da kuma wani mai wucewa da har yanzu ba a kai ga tantance ko wane ne ba. Kazalika, ta lalata rufin wani gini da ke kusa.
Tuni 'yan sandan kwance bam suka isa wurin kuma sun yi nasarar kwance wani abin fashewar a jikin babur ɗin na Mohammed, a cewarta.
Yanzu haka waɗanda lamarin ya ritsa da su suna jinya a asibiti.
Sojojin Rasha sun shiga Slavutych -- da ke yankin arewa inda gidajen ma'aikatan tsohuwar tashar nukiliya ta Chernobyl suke.
A cewar gwamnan yankin, sun ƙwace asibitin kuma sun yi garkuwa da magajin garin.
Sun fuskanci fushin mazauna yankin da suka taru a babban dandalin birnin suna rera taken kishin kasa tare da ɗaga tutar Ukraine.
Bayan da aka sake shi, magajin garin ya shaida wa taron jama'ar kasar Rasha cewa sun amince su fice yau Asabar.
Ƴan takara shida masu neman kujerar shugabancin jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya sun janye kafin babban taron zaɓen shugabanni a Abuja.
Ƴan takarar da suka janye sun haɗa da tsohon gwamnan Nasarawa Tanko Al-Makura da George Akume, tsohon gwamnan Benue da tsohon gwamnan Zamfara Abdulaziz Yari, da kuma Saliu Mustapha da Muhammed Etsu da kuma Sani Musa.
Cikin wata sanarwa mai ɗauke da sunayensu da kuma sa hannun tsohon gwamnan Benue ƴan takarar sun ce sun janye wa zaɓin shugaba Muhammadu Buhari tsohon gwamnan Nasarawa Sanata Abdullahi Adamu.
Jam`iyyar APC mai mulki a Najeriya na gudanar da babban taronta na kasa, inda wakilai daga sassan kasar za su zabi sabbin shugabannin da za su gudanar da harkokin jam`iyyar nan da shekara huɗu masu zuwa.
Jam'iyyar APC ta ce wakilanta sama da 7,000 ne za su zaɓi sabbin shugabanni
Ɗan jihar Borno ya lashe gasar izu 60 ta karatun Al Kur'ani mai tsarki ta ƙasa Najeriya da aka kammala a jihar Bauchi.
Baba Sanyinna Goni Mukatar ya karɓi kyautar naira miliyan uku.
Ƴar jihar Zamfara Haulatu Aminu Ishaq ce ta lashe gasar izu 60 ɓangaren mata.
Ita ma ta lashe kyautar naira miliyan uku.
Wannan ne karo na 36 da ake gudanar da gasar da Jami’ar Usman Danfodio da ke Sokoto ke jagoranta.
Rahotanni sun ce ƴan bindiga na ɗaukar mayaƙa a arewacin Jamhuriyyar Benin.
Jaridar La Nouvelle Tribune ta ambato wata ƙungiyar sa-kai ta Fondation Malehossou na cewa mayaƙa sun tare a yankin arewa kusa da kan iyaka da Burkina Faso, suna ɗaukar mayaƙa.
Jaridar ta ce matasa da dama sun bar gidajensu kuma ba a san inda suke ba tsawon watanni.
Bayan gudanar da bincike, aka fahimci cewa sun rugumi makamai, kamar yadda jaridar ta ambato Yacoubou Malehossou, shugaban ƙungiyar yana cewa.
Ya ce ana ba matasan aiki da kuma albashin kuɗi kwatankwashin dala tsakanin 167 zuwa 334.
Mata da dama sun fito zanga-zanga domin adawa da matakin gwamnatin Taliban na rufe makarantun sakandare na mata.
Matan sun fito rike da kwalaye da ke dauke da bayanin cewa “Ilimi ƴancinmu ne, ba tsarin siyasa ba.”
Sai dai rahotanni sun matan sun watse lokacin da sojojin Taliban suka tunkari wurin da suke zanga-zangar.
Wannan ne karon farko da mata suka fito zanga-zanga a Kabul, makwanni bayan Taliban ta kama mata da dama masu fafutikar kare haƙƙin mata.
Jami'an China sun tabbatar da cewa babu wanda ya tsira da ransa sakamakon hatsarin jirgin saman fasinja a lardin Guangxi a ranar Litinin da ta gabata.
Jirgin Boeing 737 ya taso ne daga Kunming zuwa Guangzhou, tare da mutane 132 a lokacin da ya yi hatsari ya fada cikin daji mai tsaunika.
Jami'ai sun ce babu alamun abubuwan fashewa a wurin da hadarin ya auku.
Ba a gano na'urar nadar bayanan jirgin daga jirgin saman China Eastern Airlines ba.
Amurka ta yi kira da a saka zafafan takunkmai ga Koriya Ta Arewa bayan gwajin da ta yi a baya-bayan nan na wani makami mai linzami.
Wakiliyar Amurka a Majalisar Ɗinkin Duniya Linda Thomas Greenfield ce ta bayyana haka inda ta zargi Pyongyang da tsokanar faɗa.
Sai dai China da Rasha sun ce ba za su lamunci saka wasu ƙarin takunkumai ga Koriya Ta Arewa ba.
A ranar Alhamis ne shugaban Koriya Ta Arewa Kim Jong-un ya ziyarci wurin gwajin makamin domin sa ido a yayin gwajin.
Makamin dai yana da nisan zango kuma za a iya harba shi daga wata nahiya zuwa wata kuma rabon da ƙasar ta yi gwajin irinsa tun a 2017.
Ga alama batun zaɓen shugaban APC ta hanyar maslaha zai yi wuya, inda wasu ƴan takara har zuwa ranar babban taron jam’iyyar ba su janye ba.
Jam’iyyar APC dai ta nuna cewa tsarin daidaitawa ko maslaha ne tsarin da ta fi so wajen zaɓar shugabanninta.
Shugaba Buhari ma ya nuna tsarin maslaha ko daidaitawa tsakanin ƴan takara ne yake goyon baya.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, kuma jami`i a kwamitin yada labarai na babban taron APC ya ce maslaha za a bai wa fifiko, kuma abin da jiga-jigan APC suka kashe dare suna yi ke nan, suna lallashin sauran `yan takara domin su mara wa mutum guda. Har ma an ba da umurnin jam`iyya ta mayar musu da kudin da suka kashe wajen sayen fam.
Mutum tara ne suka nuna sha`awar takarar shugabancin jam`iyyar, kuma har zuwa safiyar Asabar ranar babban taron APC babu labarin janyewar wasu ƴan takarar da ke neman shugabancin jam’iyyar.
Tun tuni rahotanni ke cewa tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Senata Abdullahi Adamu ne shugban kasa da jiga-jigan APC ke goyon baya don zama shugaban jam`iyya, kuma har yanzu fadar shugaban kasa ba ta musanta ba.
Hukumar Lafiya Ta Duniya ta bayyana cewa ta damu matuƙa kan hare-haren da ake kai wa asibitoci da sauran wuraren kiwon lafiya a Ukraine.
Sama da marasa lafiya da kuma jami'an lafiya 70 ne aka kashe tun bayan da aka soma yaƙin Ukraine.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta fito fili ta haramta kai hare-hare kan wuraren kiwon lafiya sai dai idan wuraren suna taka wata muhimmiyar rawa a yaƙin kamar bayar da mafaka ga mayaƙa masu lafiya.
Rasha ta sha nanata cewa ba dagan-gan take kai hari a wuraren farar hula ba