Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Mexico ta caccaki Amurka kan tallafawa Ukraine

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.

Rahoto kai-tsaye

Sani Aliyu

  1. 'Yan a-waren da Rasha ke mara wa baya sun harba shu'uman rokokin 'thermobaric'

    Wani bidiyo da BBC ta tabbatar da sahihancinsa ya nuna yadda ake harba wasu muggan rokoki samfurin 'thermobaric' a yakin da ake yi a Ukraine.

    Bidiyon da aka samo daga rundunar 'yan aware ta jama'ar yankin Donetsk na Ukraine - wadanda Rasha ke mara wa baya - ya nuna lokacin da ake harba rokokin daga wata na'urar da Rasha ta kera mai suna TOS-1A, wadda ka iya harba rokoki masu yawa a lokaci guda.

    Amfani da rokokin na 'thermobaric' batu ne da ya raba kawunan kasashen duniya saboda mummunan sakamakon da suke da shi bayan sun fashe, idan aka kwatanta su da bama-baman da aka saba gani.

    Su kan fara sakin wani karamin bam ne da ke dauke da wani mai, wanda bayan ya warwatsu sai bam na biyu ya tashi inda ya ke zuke dukkar iskar da ke wurin kuma duk abu mai rai da ke yankin da ya fado zai kone kurmus, har ta kan kai ga ma ba a iya ganin gawarsa.

    Kalli bidiyon a Twitter:

  2. Ga wasu abubuwan da muka wayi gari da su a mamayar da Rasha ke yi a Ukraine

    Idan yanzu ku ka fara bibiyar BBC Hausa, ga wasu muhimma abubuwan da suka faru kawo wayewar gari yau Talata a yakin da Rasha ke yi da ukraine:

    • Gargadin Biden: Shugaban Amurka ya ce akwai alamu bayyanannu cewa Vladimir Putin na shirin amfani da makamai masu guba a Ukraine. Biden ya kuma ce shugaban na Rasha "ba shi da wurin gudu" saboda turjiyar da Ukraine ke nunawa kan wannan yakin, kuma akwai hadarin zai iya fara amfani dawasu muggan makamai
    • Turjiyar Zelensky: Shugaban Ukraine ya ce kasarsa ba za ta taba mika wuya ga bukatun Rasha ba - wannan na zuwa ne bayan da Rashar ta ce za ta kyale mazauna birnin Mariupol su fice daga birnin idan Ukraine ta amince za ta mika ma ta birnin. Ya kuma sake yin kira da a tattauna kai tsaye tsakaninsa da Shugaba Putin "ta kowane hali" domin kawo karshen yakin
    • Rasha ta kara kai hare-hare ta sama: Dakarun Ukraine na cewa Rasha ta kara bude wuta ta hanyar amfani da jiragenta na yaki cikin sa'a 24 da ta gabata
  3. Budewa

    Masu bibiyarmu barka da tashi da fatan an wayi gari lafiya.

    Sani Aliyu ne a yau ke fatan kasancewa da ku a wannan yini, domin kawo muku labarai da rahotanni daga sassan duniya.

    Sai ku kasance da Sashen Hausa na BBC cikin wannan yini.