Rasha da Ukraine sun kusa cimma yarjejeniya, in ji Turkiyya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.

Rahoto kai-tsaye

Awwal Ahmad Janyau and Umar Mikail

  1. Sai da safenku

    Nan muka zo ƙarshen rahotannin a wannan shafi.

    Mu haɗu da ku gobe Litinin don samun wasu sabbin rahotannin.

    Umar Mikail ne yake muku fatan alheri.

  2. Yaƙin Ukraine: Abubuwan da suka faru zuwa yanzu

    Ukraine

    Asalin hoton, Reuters

    Idan yanzu kuka shigo shafin namu da ke kawo rahotanni kai-tsaye, ga abubuwan da ke faruwa a yaƙin Ukraine zuwa yanzu:

    • Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya yi wa 'yan majalisar Isra'ila jawabi (Knesset) inda ya shawarce su da su rabu da matsayin ƙasarsu na 'yar ba-ruwana kan yaƙin da Rasha ta ƙaddamar a kan ƙasarsa
    • Zelensky ya ce Isra'ila na da makaman kariya ta sama fiye da kowace ƙasa a duniya, yana mai cewa "tabbas za ku iya taimaka wa mutanenmu, ku ceci rayuwar 'yan Ukraine"
    • Jami'an gwamnati a garin Mariupol da ke kudancin Ukraine sun ce Rasha ta lalata wata makaranta da mata da ƙananan yara suke 400 suke fakewa a ciki. Babu wani bayani kan mutanen da harin ya ritsa da su. BBC ba ta iya tabbatar da iƙirarin ba.
    • Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi ƙiyasin 'yan Ukraine mutum miliyan 10 sun tsere daga gidajensu. MDD ta ce ko dai sun fake a cikin ƙasar ko kuma sun koma ƙasar waje
    • Ministan harkokin wajen Turkiyya, wadda ke shiga tsakani, ya ce Rasha da Ukraine sun kusa cimma yarjejeniya
  3. Rasha ta tabbatar da kashe jami'in sojanta a Ukraine

    Andrei Paly

    Asalin hoton, Kateryna Altabayeva

    Hukumomi a Rasha sun tabbatar da mutuwar mataimakin kwamandan a rundunar sojan ƙasar ta Black Sea Fleet, Kyaftin Andrei Paly, a filin yaƙi na garin Mariupol.

    Har yanzu ana ci gaba da fafatawa a garin na Mariupol mai tashar jirgin ruwa.

    Tun farko sakataren kwaliejin soja ne mai suna Konstantin Tsarenko ya tabbatar da mutuwar sojan a dandalin sada zumunta na Vkontakte (VK).

    Gwamnan yankin Sevastopol, Mikhail Razvozhayev, ya faɗa cikijn wani saƙon Telegram cewa "Andrei Nikolaevich ya zaɓi ya kare ƙasarmu a matsayin sana'arsa kuma ya rasu saboda mu zauna lafiya nan gaba".

    Rundunar sojan Ukraine ta yi iƙirarin kashe janar-janar na Rasha biyar tun bayan fara ɓarin wuta ranar 24 ga watan Fabarairu. Sai dai janar ɗaya ne kawai Rasha ta tabbaatar da mutuwarsa - Janar Andrei Sukhovetsky.

  4. Australia ta hana shigar da duwatsu masu daraja Rasha

    Dutsen alumina

    Asalin hoton, Getty Images

    Australia ta haramta fitar da duwatsun alumina da bauxite masu daraja zuwa Rasha saboda mamayar da ta yi wa Ukraine.

    Australia ce ƙasar da ke samar wa Rasha kashi 20 cikin 100 na dutsen alumina da take amfani da shi.

    Wannan takunkumi kari ne kan wanda kasar ta dauka a karshen watan jiya a kan Rasha.

    A ranar Juma'a ma Australia ta sanya takunkumi ga wani dan kasuwar Rasha Oleg Deripaska da ya mallaki wani bangare na masana'antar sarrafa alumina a Queensland.

    A bangare guda kuma, Australia za ta bai wa Ukraine karin tallafin dala miliyan 22 na kayan agaji da karin dala miliyan 21 domin tallafa wa sojin ƙasar.

  5. Rasha da Ukraine sun kusa cimma yarjejeniya, in ji Turkiyya

    Rasha da Ukraine

    Asalin hoton, Reuters

    Ministan Harkokin Waje na Turkiyya Mevlut Cavusoglu da ke shiga tsakani a tattaunawar zaman lafiya tsakanin Rasha da Ukraine, ya ce an samu ci gaba tsakanin ɓangarorin biyu.

    Cavusoglu ya faɗa wa kamfanin labarai na AFP cewa "ba abu ne mai sauƙi ba a cimma a matsaya yayin da ake ci gaba da fafata yaƙi, yayin da ake kashe fararen hula", amma ya ƙara da cewa "mun ga alamun suna ƙoƙarin cimma yarjejeniya".

    Ministan ya ziyarci Rasha da Ukraine a makon nan sakamakon ƙawancen da Turkiyya ke yi da ƙasashen biyu.

    Ya ce Turkiyya na tuntuɓar tawagogin da ke tattaunawa da juna amma ya ƙi bayyana abin da tattaunawar ta ƙunsa saboda "Turkiyya na taka rawar mai sasanci ta gaskiya".

    Ɓangarorin biyu na yunƙurin cimma yarjejeniya a kan abu shida:

    • Ukraine ta zama 'yar ba-ruwana
    • Ukraine za ta watsar da makamanta
    • Abin da Rasha ta kira "kakkaɓe 'yan ta'adda daga Ukraine"
    • Cire duk wani tsari da zai hana amfani da harshen Rashanci a Ukraine
    • Matsayin yankuna biyu da suka ɓalle daga Ukraine na Donbass
    • Matsayin yankin Crimea da Rasha ta ƙwace a 2014

    Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya faɗa cikin wani bidiyo ranar Asabar cewa: "Wannan ne lokacin da ya kamata a haɗu, a tattauna, lokaci ne da za a fayyace iyakoki da kuma yi wa Ukraine adalci."

  6. Rasha ta sake harba makami mai gudun walƙiya a Ukraine

    Makamin Rasha

    Asalin hoton, Reuters

    Rasha ta ce ta harba makami mai linzami don kai hari kan wani wurin ma’adanin mai a Ukraine.

    Rana ta biyu ke nan a jere da Rasha ta harba makamin.

    An kai harin ranar Asabar a wurin ajiye makamai na Ukraine da ke ƙarƙashin ƙasa, wanda Rasha ta ce karon farko ke nan da ta yi amfani da makamin mai gudun walƙiya tun soma yaƙin.

    Sai dai BBC ba ta iya tabbatar da iƙirarin na Rasha ba.

  7. Majalisar Ɗinkin Duniya na son a tsagaita buɗa wuta a Yemen lokacin Azumi

    Yemen

    Asalin hoton, AFP

    Jakadan Majalisar Ɗinkin Duniya na musamman Hans Grandberg ya nuna cewa akwai yiyuwar tsagaita buɗa wuta a Yemen tsakanin ƙawancen da Saudiyya ke jagoranta da kuma mayaƙan Houthi a lokacin Azumin Ramadan da za a soma a farkon Afrilu.

    Ofishin Mr Grandberg ya ce ya gana da mai shiga tsakani na ɓangaren Houthi da kuma jami’an Oman. Manufar tattaunawar ita ce koƙarin magance matsalar jin-ƙai a Yemen da ya ƙunshi “yiyuwar tsagaita wuta” lokacin azumin Ramadan.

    Yaƙin Yemen na shekara bakwai ya kashe dubban mutane tare da jefa ƙasar cikin yunwa.

  8. Shugaban majalisar dokokin Uganda ya rasu

    Shugaban Majalisar dokokin Uganda, Jacob Oulanya, ya rasu.

    ShugabaYoweri ne ya sanar da mutuwar shugaban majalisar a shafinsa na Twitter a ranarLahadi.

    A cikin sakon nasa, shugaban ya kira marigayin mutumin kirki.

    Kawo yanzu babu wani bayani kan musabbabin mutuwar Mista Oulanyah, amma ya kwashe sama da wata guda yana kwance a asibiti a Amurka.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  9. Algeria ta yi wa jekadanta a Madrid kiranye

    Gwamnatin Algeria ta yi wa jakadanta a birnin Madrid kiranye, a wani bangare na yi wa Spain bore kan matakin marawa Morocco baya na mallakar wani yanki da kasashen biyu ke takaddama akai.

    A ranar Juma'a, ministan harkokin wajen Spain, Jose Manuel Albares, ya goyi bayan Morocco wadda kasar ta yi wa mulkin mallaka, kan bukatar da ta shigar na neman mamaye wani bangare na yammacin kasarta da suka dade suna takaddama tsakaninsu da Algeria game da wanda ya dace ya mallake shi.

  10. Ukraine ta yi iƙirarin kashe sojojin Rasha 15,000

    Jami’an sojin Ukraine sun yi ukirarin cewa kusan sojojin Rasha 15,000 aka kashe tun lokacin da shugaba Putin ya abkawa ƙasar da yaƙi sama da mako uku da suka gabata.

    Sabbin alƙalumman da aka wallafa a wani shafin Facebook na ma’aikatan Ukraine, jami’ai sun ce sojojin Rasha 14,700 aka kashe a kwanaki 25 da aka shafe ana gwabza faɗa.

    Bayanan sun yi iƙirarin cewa an lalata makaman Rasha a yaƙin, da suka haɗa da tankokin yaƙi 476 da jiragen yaƙi sama da 200 da helikwfta da jirage marar matuki da dama.

    BBC ba za ta iya tabbatar da wannan iƙirarin ba, amma majiyoyi na ƙasahen yammaci sun ce Rasha ta ji jiki a yaƙin yayin da jami’an tsaron Amurka suka yi ƙiyasin cewa sojojin Rasha 7,000 aka kashe tare da raunata 21,000.

    Ukraine

    Asalin hoton, Getty Images

  11. Xavi: Ƙofar Barcelona a buɗe take ga Messi

    Messi

    Asalin hoton, Getty Images

    Kocin Barcelona Xavi Hernandez ya ce ƙofar Barcelona a buɗe take ga Lionel Messi a duk lokacin da yake so ya dawo.

    Xavi ya faɗi haka ne a taron manema labarai a ranar Asabar kan shirin da yake na haɗuwa da Real Madrid a La Liga a wasan hamayya na Clasico.

    Messi ya koma PSG da taka leda bayan Barcelona ta ce ba ta iya sabunta kwangilar shi.

    An tambayi Xavi ko zai iya dawo da Messi, sai kocin ya ce: “idan dai ni ne koci, ƙofa a buɗe take idan har yana son ya dawo a ko wane lokaci.”

    Xavi ya kuma yi wa Messi tayin kawo ziyara domin kallon atisayen Barcelona , tare da tattaunawa da shi.

  12. Shugabannin Izala sun kai wa mataimakin shugaban ƙasar Ghana ziyara

    Shugabannin ƙungiyar Izala a Najeriya sun kai ziyara ƙasar Ghana inda suka gana da mataimakin shugaban ƙasa Mahamudu Bawumia

    Babban sakataren kungiyar Jama'atu Izalatul Bid'ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS),Sheikh Kabiru Haruna Gombe ya wallafa hotunan ziyarar a Twitter.

    Hotunan sun nuna shi tare shugaban ƙungiyar Shiekh Abdullahi Bala Lau a gidan mataimakin shugaban Ghana.

    Kauce wa X, 1
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 1

    Shiekh Gombe ya ce mataimakin shugaban Ghana ne ya gayyace su domin tattauna batutuwan da suka shafi harakokin addinin Islama.

    Ya kuma ce sun halarci wani bikin ƙaddamar da sabuwar makarantar koyar da aikin jinya ta Musulunci a Ghana.

    Hotunan da malamin ya wallafa sun nuna ginin cibiyar bene hawa uku inda hawa na biyu ke ɗauke da sunan “Sheik Haruna Kabiru Gombe”, hawa na uku kuma yana ɗauke da sunan “Sheik Abdullahi Bala Lau.”

    Hawa na farko na ɗauke ne da sunan marigayi “Sheik Abubakar Gummi”

    Kauce wa X, 2
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 2

  13. Rasha ta ce ta kashe sojojin haya na ƙasashen waje a harin makami mai linzami

    Ma’aikatar tsaron Rasha ta ce ta kashe sojojin haya da dama a harin makami mai linzami da aka kai a wata cibiyar horar da sojoji a yammacin Ukraine, kamar yadda kamfanin dillacin labarai na RIA ya ruwaito.

    Manjo Janar Igor Konashenkov, kakakin ma'aikatar, ya ce fiye da sojojin Ukraine 100 da "wasu sojojin haya" ne aka kashe a lokacin da "makami mai linzami" ya faɗa wani sansanin sojin Ukraine da ke kusa da Ovruch a Zhytomyr.

    "Makamai masu linzami da aka harba ta sama sun kai hari a cibiyar horas da dakarun soji na musamman na Ukraine, inda sojojin haya na kasashen waje da suka isa Ukraine ke zaune," in ji Konashenkov.

    BBC ba za ta iya tabbatar da wannan ikirarin ba.

  14. Ƴan sanda sun kashe ƴan bindiga da ake zargin ƴan IPOB ne a Imo

    Yan sanda

    Asalin hoton, Getty Images

    Rahotanni sun ce an kashe wasu da ake zargin ƴan kungiyar masu fafutukar kafa ƙasar Biafra IPOB ne a wani artabu da ‘yan a garin Omuma, mahaifar gwamna Hope Uzodimma da sanyin safiyar Lahadi.

    An kashe ‘yan bindigar ne bayan sun kai hari ofishin ƴan sandan Omuma da ke karamar hukumar Oru ta Gabas a jihar Imo, kamar yadda CSP Mike Abattam, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Imo ya bayyana.

    Ya ce ƴan bindigar sun buɗe wuta bayan sun abka ofishin ƴan sanda da safe, amma a cewarsa ƴan sanda sun murƙushe su a musayar wuta.

    Jami’in ya ce mutum huɗu aka kashe yayin da wasu saura suka tsere cikin daji ɗauke harsashe a jikinsu.

    Wannan na zuwa bayan wasu ƴan bindiga sun kai hari ofishin ƴan sanda a Umuguma da ke yankin Owerri ta yamma tare da kashe ƴan sanda biyu a ranar Asabar

    Haka kuma ƴan bindiga sun kai hari gidan shugaban ƴan ƙabilar Igbo ta Ohanaeze Ndigbo inda suka ƙone gidansa.

  15. Zelensky zai nemi goyon bayan Isra’ila

    Volodymyr Zelensky

    Asalin hoton, Facebook

    Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky zai yi wa ƴan majalisar Isra'ila jawabi ta kafar bidiyo, domin samun ƙarin goyon bayan kasashen duniya kan kutsen da Rasha ta yi wa kasarsa.

    Wasu rahotanni na cewa zai yi amfani da damarsa ta zama Bayahude da faɗi tashin da suka yi, sannan ya kamanta halin da Ukraine ke ciki a hannun Rasha, da neman goyon bayan yaƙarsu kwatankwacin wanda aka yi waƴan Nazi a lokacin yaƙin duniya na biyu.

    Shugaba Zelensky ya yi magana da sauran 'yan majalisu a sassa daban-daban na duniya ciki har da Birtaniya da Amirka, domin neman taimakonsu.

    An bayyana cewa saboda gyaran da ake yi wa zauren Majalisar Isra’ila, za su yi tattaunawar ne a wani wuri mai cike da tsaro.

  16. Mayaƙan Houthi sun kai hari cikin Saudiyya

    Ƙawancen da Saudiyya ke jagoranta a yaƙin da ake yi da mayaƙan Houthi a Yemen, ya ce ƴan tawayen sun kai wasu hare-hare cikin Saudiyya.

    An kai harin ne kan cibiyar wutar lantarki da matatar mai da wani wuri na daban da ke kudancin Saudiyya.

    Akwai rahotannin da suka tabbatar da faruwar lamarin, da lalacewar gidaje sai dai babu wanda ya mutu ko jikkata.

    Haɗakar kawancen, sun ce sun gano jirage marasa matuka huɗu kuma tuni suka lalata su.

    Mayaƙan Houthi na yawan kai hari Saudiyya da jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami, a matsayin martani kan harin da Saudiyya da kawayenta ke kai wa Yemen.

    A farkon wannan watan Houthi ta yi watsi da goron gayyar zama teburin Sulhu a Riyadh a wannan watan,domin kawo ƙarshen yaƙin Yemen.

  17. An murƙushe mutumin da ya kai hari Masallaci lokacin sallar Asuba a Canada

    Masallaci

    Asalin hoton, Google

    Masu ibada a wani masallaci a kasar Canada sun murƙushe tare da kama wani mutum da aka yi zargin ya yi yunƙurin kai musu hari da gatari a lokacin sallar asuba a ranar Asabar, kamar yadda ‘yan sanda suka bayyana.

    Ɗaya daga cikin masu ibadar ne ya murƙushe mutumin tare da karɓe gatarin a hannunsa kuma ya riƙe shi har sai da ‘yan sanda suka iso, kamar yadda kafafen yada labarai na kasar suka ruwaito.

    Ƴan sanda sun kama matashin mai shekaru 24 a wurin da lamarin ya faru a unguwar Mississauga, kuma tuni aka tuhume shi.

    Limamen masallacin ya ce wasu daga cikin masu ibada sun samu rauni bayan ya fesa masu wani abu.

  18. Maraba

    Muna maku maraba da kasancewa da mu a wannan shafin da muke kawo maku labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.