Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

An yaɗa wani bidiyon ƙarya na Zelensky yana miƙa wuya ga Rasha

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.

Rahoto kai-tsaye

Sani Aliyu

  1. 'Yan Najeriya na kokawa saboda nau'ororin samar da lantarki sun sake lalacewa

    Lalacewar da tsarin samar da hasken lantarki ke yi ya ci gaba da saka 'yan Najeriya cikin duhu.

    Masu amfani da lantarki a gidajensu ko a wuraren aiki a biranen Legas da Enugu da Ibadan da Anambra da Abuja na rayuwa cikin wannan duhun saboda na'urorin samar da hasken lantarki sun sake gazawa.

    Wannan lamarin da ke faruwa ya zama ruwan dare gama duniya, kuma kamfanonin da ke samarda lantarki sun tabbatar da haka.

    Yini na biyu ke nan a jere da ake samun wannan matsalar ta lalacewar na'urorin samar da lantarki a fadin Najeriya.

    Matsalar na faruwa ne dadai lokacin da Najeriya ke fuskantar matsalar man fetur da wanda jirgin sama ke amfani da shi.

  2. Hotuna: Rasha na ci gaba da mamayar da ta ke yi a Ukraine

    Wata mata na kuka a cikin wani jirgin kasa da ke kan hanyar zuwa Poland, wani mutum na tuka kekensa a gaban wani ginin da bam ya ragargaza, sai wata tankar yaki da ke sintiri a wani layin da kusan babu koa cikinsa - wadannan ne batutuwan da muka kawo hotunansu gareku a yau.

  3. Shin me ke faruwa ne a Ukraine?

    Idan yanzu ku ka fara bibiyar BBC, ga wasu muhimma abubuwan da suke faruwa a yakin da ake gwabzawa a Ukraine.

    • Sojojin Rasha na ci gaba da jefa bama-bamai a manyan biranen Ukraine inda suke rusa gine-gine a babban birnin kasar Kyiv a wannan safiyar
    • Mutum biyu sun sami raunuka bayan da bama-bama suka fada kan wani bene mai hawa 12 a gundumar Shevchenko.
    • An kafa dokar hana fita a birnin Kyiv yayin da Magajin Garin birnin Vitali Klitschko ke gargadi cewa an shiga wani yanayi "mai hatsari da wahala."
    • Sai dai akwai alamun ana samun ci gaba a tataunawar da Ukraine ke yi da Rasha inda shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ke cewa ya fara samun karfin gwuiwa
    • A birnin Mariupol kuwa na kudancin kasar da aka yi ma kawanya, mataimakin Magajin Garin birnin ya ce Rashawa na tsare da 'yan garin 400 cikinsu akwai likitoci da marasa lafiya "a wani yanayi da ya yi kama da na garkuwa aka yi da su"
    • Ma'aikatar tsaro ta Birtaniya ta ce dakarun Rasha na fuskantar matsaloli yayin da suke kokarin kutsawa cikin yankuna da biranen Ukraine da kawo yanzu ba sa hanunsu.
  4. Barkanmu da wayewar gari yau Laraba!

    Masu bibiyar mu a wannan shafi muna muku barka da safiya da fatan an tashi lafiya.

    Sani Aliyu ke fatan kasancewa da ku a wannan yini domin kawo muku labarai da rahotanni daga sassan duniya daban daban, ciki har da yakin da ake gwabzawa tsakanin Rasha da Ukraine, da kuma wasu batutuwan da ke wakana a gida Nijar da Kamaru da Chadi da Ghana da kuma Najeriya.

    Muna fatan za ku ci gaba da kasancewa da mu!