Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An yaɗa wani bidiyon ƙarya na Zelensky yana miƙa wuya ga Rasha
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.
Rahoto kai-tsaye
Sani Aliyu
Biden ya kira Putin "mai aikata laifin yaƙi"
Shugaban Amurka Joe Biden ya kira Vladimir Putin a matsayin “mai laifin yaƙi” a karon farko.
Kafin yanzu, gwamnatin Amurka ta daɗe tana kaucewa amfani da kalaman, ko da kuwa an nemi ta faɗa.
Da yake zantawa da manema labarai a Fadar White House a ranar Laraba, Biden ya ce “ina ganin mai laifin yaki ne."
Tun da farko Biden ya ce Amurka zata bayar da karin dala miliyan takwas domin tallafawa sojojin Ukraine, yana mai gargadin cewa shugaban Rasha Putin zai yi nadama a kan irin abubuwan da ya aikata a Ukraine.
Mr Biden ya yabawa irin kokarin da shugaban Ukraine Zelensky ya yi musamman wajen samun karfin giwa har ya nemi karin tallafi a wani bayani da ya yiwa majalisar dokokin Amurka ta Bidiyo.
An yaɗa wani bidiyon ƙarya na Zelensky yana miƙa wuya ga Rasha
Ana ta yawo da wani bidiyo na bogi na shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky a kafofin sada zumunta yana yin kira ga sojojin ƙasar su ajiye makamansu.
Ko da yake leɓɓansa na motsawa daidai da sautin, amma kan Zelensky yana kallon wani wuri kuma muryar ba ta yi kama da tasa ba.
Wani ɓangare na bidiyon na bogi ya fito a shafin intanet na tashar talabijin ta Ukrayina 24 kuma an watsa saƙon a taƙaice a talabijin.
Ukrayina 24 a cikin wata sanarwa ta ce an yi wa shafinta ne kutse.
Zelensky ya yi watsi da saƙon wanda ya kira na bogi da aka wallafa a shafinsa na Instagram, yana mai cewa “shi sai dai ya yi kira ga sojojin Rasha su ajiye makamansu su koma gida.
Ƴan Sudan na ci gaba da zanga-zangar adawa da tsadar burodi
Ɗalibai a biranen Sudan da dama sun ci gaba da zanga-zanga tsawon kwana uku kan tsadar kayan abinci musamman burudi.
Rahotanni daga Nyala, babban birnin jihar Darfur ta Kudu, sun an raunata dalibai da dama bayan da jami'an tsaro suka tarwatsa su.
Malamai ma sun fito suna zanga-zanga domin nuna fushinsu bayan ƴan sanda sun yi wa ɗaya daga cikunsu duka a cikin makaranta a ranar Lahadi.
Masu aiko da rahotanni sun ce matsin tattalin arziki da hauhawan farashi ya fusata ƴan ƙasar da kuma matsi daga shugabannin soji.
Za mu goyi bayan Ukraine ta kare ƙasarta - Nato
Sakatare Janar na ƙungiyar tsaro ta Nato ya ce za su ci gaba da ba Ukraine goyon baya kan abin da ya kira babban goyon bayan soji a yaƙin da take da mamayar Rasha.
Amma Jens Stoltenberg ya nanata cewa Nato ba za ta tura dakaru ba a Ukraine duk da rokon da Shugaba Zelensky yake ci gaba da yi na neman hana shawagin jiragen Rasha.
Jens Stoltenberg ya yi magana ne bayan taron ministocin tsaro na Nato a Brussels - na farko tun bayan da Rasha ta abkawa Ukraine makonni uku da suka gabata.
Buhari ya gana da Mai Mala kuma ya yarda ya ci gaba da shugabancin APC
Gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Buni ya gana da shugaba Muhammadu Buhari a Landan.
Buhari ya kuma amince Mai Mala Buni ya ci gaba da jagorancin APC a matsayinsa na shugaban kwamatin riƙo na jam'iyyar, kamar yadda Hon Faruk Adamu Aliyu jigo a jam’iyyar APC ya shaida wa BBC.
Ya ce Buhari ya amince Mai Mala Buni ya ci gaba da aikin jagorancin babban taron jam’iyyar da ake shirin gudanarwa a ranar 26 ga watan Janairu, duk da wani umarnin kotu da ya ce a dakatar da taron.
Shugabancin APC ya shiga ruɗani ne a ƙarshen watan Fabarairu tun bayan da aka ga Gwamnan Neja Abubaukar Sani Bello ya fara jagorancin kwamatin. Daga baya kuma wata wasiƙa ta ɓulla cewa Mai Mala ne ya ba shi riƙo saboda ya yi tafiya ƙasar waje don a duba lafiyarsa.
Rikicin shugabanci a APC ya ƙara ƙamari ne tun bayan da wasu gwamnoni, ciki har da Nasir El-Rufai na Kaduna, suka ce Shugaba Muhammadu Buhari ne ya ba da umarnin a sauke Mai Mala Buni, wanda ya fara jagoranci tun watan Yuni na 2020.
Ba mu buƙatar buga sabbin kuɗi saboda takunkumi - Putin
Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ce ƙasashen yammaci ba za su yi nasara ba kan abin da ya kira yunƙuri na mamaye duniya da kuma mayar da Rasha saniyar ware, kamar yadda Reuters ta ruwaito.
Putin wanda ya ke jawabi a wani taron gwamnati da aka yaɗa ta kafar talabijin da safe, ya ce idan har ƙasashen yammaci na tunanin Rasha za ta kariya, to ba su fahimci Rasha ba.
Ya kuma taɓo batun takunkumi da aka kakaba da nufin gurgunta tattalin arzikin Rasha - amma ya ce Babban Bankin ƙasar ba ya buƙatar buga sabbin kuɗi domin ƙasar tana cikin wadata.
Nato ba za ta tura sojoji a Ukraine ba ko hana shawagin jirage - Stoltenberg
Shugaban Nato Jens Stoltenberg, ya tattauna da manema labarai a Brussels bayan taron ministocin tsaro na ƙungiyar.
Da BBC ta tambaye shi ko akwai wasu ƙasashe da suke son a hana shawagin jirage, idan har Nato ta yanke shawarar ba za ta yi ba.
Stoltenberg ya bayar da amsa cewa mambobin ƙungiyar kansu a haɗe yake na mataki guda na kaucewa tura sojoji a ƙasa ko na sama "saboda muna da haƙƙin tabbatar da cewa yaƙin Ukraine bai fantsama ba."
BBC ta kuma tambaye shi ko yana tunanin Ukraine ta sassuta kan burinta na shiga Nato a matsayin babban mataki na tattaunawa da Rasha.
Stoltenberg wanda yake bikin zagoyowar ranar haihuwarsa - ya ce "Ukraine ƙasa ce mai ƴanci kuma tana da damar ta zaɓi makomarta. " Ya rage nasu su yi yanke shawarar burin shiga Nato ko kuma aa," in ji shi.
Yakin Ukraine: Abubuwan da suka faru a yau
Ga abubuwan da suka faru yau - makonni uku tun bayan da Rasha ta kaddamar da hare-hare three weeks a Ukraine.
- Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya yi waiwaye kan harin 9/11 inda ya jaddada kiran da ya yi ga Amurka ta dauki matakin haramta zirga-zirga sararin samaniya a wani jawabi da ya yi wa 'yan majalisar dokokin kasar - inda aka rika yi masa tafi.
- Ana sa ran Joe Biden zai sanar da taimakon $800m (£612m) na ayyukan soji bayan jawabin Zelensky
- An ci gaba da fada yayin da aka jikkata mutum biyua Kyiv bayan an yi luguden wuta a wasu manyan gidaje da safiyar yau
- A Kharkiv, birni na biyu mafi girma a Ukraine, mutum biyu sun mutu bayan an yi luguden wuta a wani rukunin gidaje, a cewar hukumar bayar da agajin gaggawa
- Dakarun Ukraine sun yi ikirarin kashe janar din soji na hudu na rundunar sojin Rasha tun bayan soma kai hare-haren Rasha, ko da yake ba a tabbatar da hakan ba
Abinci da magunguna sun kusa karewa a Mariupol
Kimanin ma’aikata da marasa lafiya 400 ne suka maƙale a cikin asibitin da sojojin Rasha suka kwace iko da shi a kudancin birnin Mariupol.
Iryna Vereshchuk, mataimakin firaiministan Ukraine, ya ce sojojin Rasha na ci gaba da harbin dakarun Ukraine daga cikin harabar asibitin.
Wakilin Yanayi a Mariupol na dada kamari yayin da mazauna garin kusan 400,000 ke fama da rashin ruwa da wutar lantarki da iskar gas, kuma ba su da halin barin garin. Samun mutanen da ke zaune a garin na da matukar wahala.
Dmytro Horshakov ya ce mahaifiyarsa mai shekaru 57 ta na asibitin kuma ya kasa samunta a waya, amma yana samun labarinta daga wani abokin shi da ke zaune a garin.
An sallamo Sarki Salman na Saudiyya daga asibitin kwararru na Riyadh
Masarautar Saudiyya ta ce an sallamo Sarki Salman bin Abdulaziz daga asibiti.
Wata sanarwa da Masarautar ta fitar ta ce: "Mai yi wa Masallatai Biyu Masu Tsarki hidima, Sarki Salman bin Abdulaziz (Allah ya cigaba da kare shi) ya bar asibitin kwararru na Sarki Faisal a Riyadh bayan da likitoci suka yi nasarar binciken lafiyarsa da safiyar yau, godiya ta tabbata ga Allah."
A watan Yulin 2020 an kwantar da Sarki Salman a asibiti na tsawon kwana 10 domin cire ma sa wasu duwatsu a jikinsa.
Shafin sada zumunta na Haramain Sharifain ya wallafa wasu hotunan sarkin mai shekara 86 yayin da yake fitowa daga asibitin, kuma ana iya ganin dansa Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman cikin masu yi ma Sarkin hidima suna raka shi.
Shugaban hukumar leken asiri ya ce makomar Rasha a duniya na dab da tabbatuwa
Shugaban hukumar leken asiri ta Rasha ya ce cikin kwanaki masu zuwa za a yanke hukunci kan makomar kasar.
Sergei Naryshkin, wanda shi ne ke shugabantar hukumar ta SVR ya shaida wa wasu jami'ai a Moscow cewa "Rasha na fuskantar wani yanayi mai cike da tarihi."
Naryshkin ya ce "ana daf da sanin matsayar Rasha da makomarta tsakanin kasashen duniya."
Ya kuma ce "cikin wadannan al'amuran, Rasha ba ta taba ja da baya ba kuma ba za ta ja da baya ba, domin a maimakon haka za ta bace a doron kasa ne."
Gabanin mamayar da Rasha ke yi a Ukraine, Shugaba Putin ya muzanta Naryshkin yayin wani taro da aka haska a tashar talabijin mallakin gwamantin kasar.
Manchester United na binciken yadda wasu magoya bayanta suka jefi kocin Atletico Madrid
Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta ce tana duba bidiyon da aka nada a filin wasan Old Trafford wanda ya nuna yadda wasu magoya bayan kungiyar suka rika jifa da wasu abubuwa yayin da kungiyar ta sha kaye a hannun Atletico Madrid ta ci daya mai ban haushi.
Wasunsu sun jefi kocin kungiyar ta Atletico Madrid da abubuan da suka hada da kwalabe bayan da aka kammala wasan.
Hukumar da ke shirya gasar kwallon kafa ta nahiyar Turai, UEFA na jiran rahoton da 'yan kallon da ta tura za su mika ma ta kafin ta dauki mataki.
Duk wanda aka samu da laifin yin jifa a filin wasan kwallo ya taka dokar wasa kuma ana iya hana shi halartar wasanni a filayen wasa na tsawon shekara uku.
Majalisar wakilai na binciken bashin tiriliyan 2.6 da gwamnatin Najeriya ke bin kamfanonin mai
Majalisar Wakilan Najeriya ta ƙaddamar da bincike ranar Talata kan kuɗi fiye da naira tiriliyan biyu da rabi da gwamnatin ƙasar ke bin kamfanonin man fetur 77 bashi.
Rahoton jaridar Punch ya ce 'yan majalisar na aiki ne da wani rahoton shekarar 2019 da kwamatin Nigeria Extractive Industry Transparency Initiative ya gabatar.
Kakakin Majalisa Femi Gbajabiamila ya yi barazanar cewa majalisar za ta yi amfani da tanadin kundin tsarin mulki a kan duk kamfanin da ya ƙi bai wa binciken haɗin kai.
"Don nuna muhimmancin wannan aikin, bari na tabbaatar muku cewa idan aka samu wani mutum ko kamfani da ya ƙi bai wa binciken haɗin kai, zai zama lokaci na farko da majalisa ko kuma ni zan yi amfani da ikon kundin tsarin mulki don a kama shi," in ji Mitsa Gbajabiamila.
Ya ƙara da cewa naira tiriliyan 2.6 kuɗi mai yawa da bai kamata a ƙyale su tafi a banza ba.
An tabbatar da mutuwar sojojin Kenya 10 a Somalia
Sama da sojojin Kenya 10 ne aka tabbatar da mutuwarsu yayin da wani bam ya fashe a gefen titi a Kudancin Somalia ranar Litinin.
Mutum biyar ne a halin yanzu aka tabbatar da sun ji rauni.
Lamarin ya faru ne a lokacin da motar sojin ta taka wani abin fashewa a yankin Gedo da ke kusa da iyakar Kenya da Somalia.
Ba a bayyana sunayen sojojin da suka rasu ba amma wani tsohon ɗan takarar shugabancin Kenya ya wallafa saƙo a shafinsa na Twitter, yana cewa ƙaninsa na daga cikin waɗanda suka rasu.
An ɗora alhakin harin kan ƙungiyar al-Shabaab mai alaƙa da Al-Qaeda wadda ta sha kai hare-hare irin wannan kan farar hula da jami'an tsaro.
Korona: Kasar Namibiya ta daina tilasta wa 'yan kasar amfani da takunkumi
Shugaban kasar Namibiya Hage Geingob ya sanar cewa gwamnatinsa ba za ta ci gaba da tilasta wa 'yan kasar su sanya takunkumi a ofisoshi da wuraren da jama'a ke taruwa ba.
Mista Geingob ya kuma ce 'yan kasar waje da ke ziyara a kasar ba sa bukatar yin gwajin korona idan sun shiga kasar.
Cire wannan bukatar na zuwa ne yayi da ake samun raguwar masu kamuwa da annobar korona.
Shugaban ya ce an kara yawan masu iya halartar bukukuwa da tarurruka daga mutum 500 zuwa mutum 1,000.
Alkaluman masu kamuwa da cutar korona a kasar 222 ne, inda ake samun kimanin mutum 14 da ke kamuwa a kowace rana cikin kwanaki bakwai da suka gabata.
Ukraine: Mun amince 'har abada ba za mu shiga NATO ba'
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya amince cewa kasarsa ba za ta taba iya shiga kungiyar tsaro ta NATO ba.
Wannan muhimmin sauyi ne a matsayar kasar wanda ka iya taimakawa a kawo karshen mamayar da Rasha ke yi wa kasar.
Gabanin Rasha ta kutsa cikin kasar, daya daga cikn manyan bukatun Rasha shi ne kar Ukraine ta kuskura ta shiga NATO.
Kawo yanzu, Amurka ta yi watsi da batun hana shigar da Ukraine cikin kungiyar tsaron, tare da gwamnatin kasar da ma kungiyar ta NATO; suna cewa Ukraine kasa ce mai 'yanci kuma tana iya gudanar da harkokinta yadda ta so.
Rasha ta dade tana cewa babbar bukatarta ita ce Ukraine ta zama 'yar ba ruwanmu a siyasar gabashin Turai da na yammacin Turai.
Ukraine: 'Mun kashe janar din sojojin Rasha na hudu'
Jami'an gwamnatin Ukraine sun ce sun kashe wani janar din sojojin Rasha, wanda suka ce alama ce ta yadda ake tilasta wa janar-janar din Rasha su jagoranci yakin da Rasha ke yi a Ukraine.
Wani mai ba da shawara a ma'aikatar harkkin wajen Ukraine, Anton Gerashchenko ya sanar a manhajar sadarwa ta Telegram cewa sojojin Ukraine sun kashe Manjo-Janar Oleg Mityaev yayin wani yakin da aka gwabza a wajen birnin mariupol.
Sai dai BBC ba za ta iya tabbatar da sahihancin rahoton ba, kuma Rasha ba ta ce komai kan labarin kashe janar din ba.
Shugaba Zelensky na Ukraine ya sanar da cewa dakarunsa sun kashe wani janar na sojojin Rasha sai dai bai ambaci sunansa ba.
'Yan Najeriya a Ukraine na tsaka-mai-wuya
Wasu dalibai 'yan Najeriya da suka makale a birni Kherson na Ukraine wanda sojojin Rasha suka yi wa kofar rago na bayyana mwuyacin halin da suka fada bayan mako biyu suna buya a wani dakin karkashin kasa.
Daliban na bukatar kasarsu ta dauki matakin ceto su da gaggawa.
Jerry Kenny ya shaida wa BBC cewa shi da wasu abokansa shida ba su da lafiya saboda mummunan halin da suke rayuwa cikinsa a dakin karkashin kasa kuma ya ce ba su da abinci da sauran abubuwan more rayuwa.
"Wasu cikinmu ma ba sa iya magana saboda fargaba," inji shi, kuma ya ce gwamnatin Najeriya "ba ta tuntube mu ba da zummar samar mana da ruwa da abinci".
"Na yi magana da wakilan kasarmu da jakadu da kuma jami'an ma'aikatar harkokin waje kan yadda za a iya kwashe mu daga nan. Amma har yanzu babu labari."
Ministan harkokin wajen Najeriya Geoffrey Onyeama ya ce ya tuntubi jakadun Najeriya da ke Ukraine da Rasha, kuma sun tuntubi takwarorinsu na Rasha da na Indiya domin samar da hanyoyin kwaso daliban daga Ukraine zuwa Najeriya.
Rahotanni na cewa har yanzu akwai daliban nahiyar Afirka fiye da 100, yawancinsu daga Najeriya da ke Kherson.
Dubban kororon roba da magungunan kanjamau sun yi batan dabo a Kenya
Hukumar da ke kula da samar da magunguna da kayayyakin kiwon lafiya ta ce an sace wasu dubban kayayyaki ciki har da dubban kororon roba da magungunan da ake raba wa masu tarin fika da ragar kare jama'a daga cizon sauro wadanda darajarsu ta kai dalar Amurka 100,000.
Hukumar ta ce an sace kayan ne daga wani dakin adana kaya a birnin Nairobi.
Wata gidauniya mai suna Global Fund da ke samar wa kasashe tallafin magungunan cutar Sida da tarin fika da zazzabin cizon sauro ne ta bayyana haka.
Gidauniyar ta tuhumi Kemsa da zuzuta kudin magungunan da miliyoyin daloli, inda suka kara farashin wasu magungunan sau 100.
Global Fund ta kuma ce mutane na sace magungunan kuma suna sayar da su a kasuwar bayan fage da kuma ga masu shagunan da ke tallan magunguna masu zaman kansu.