Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Ƴan bindiga sun kashe DPO a Neja

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.

Rahoto kai-tsaye

Sani Aliyu and Awwal Ahmad Janyau

  1. Yau ce rana ta 20 ta mamayar da Rasha ke yi a Ukraine

    Ga wasu cikin abubuwan da suka faru kawo yanzu safiyar Talata a yakin da Rasha ke yi da Ukraine:

    • Rasha ta ci gaba da jefa bama-bamai a birnn Kyiv da safiyar nan, har wani bene mai gidajen zama ya kama da wuta baya ga fashewar abubuwa da aka rika ji cikin babban birnin na Ukraine. Ma'aikatar da ke kula da ayyukan agaji ta ce an kashe gobarar
    • A shirya bude wasu hanyoyi na jin kai daga karfe 9 na safe zuwa karfe 9 na dare a yankin Sumy da ke arewa maso gabashin kasar, kamar yada gwamnatin yankin ta sanar
    • Za a ci gaba da tattaunawa tsakanin Rasha da Ukraine a yau, kamar yadda wata sanarwa da ofishin shugaban kasar Ukraine ta sanar
    • Wani mai ba gwamnatin Ukraine shawara ya ce a ganinsa za a kawo karshen wannan yakin a farkon watan Mayu
  2. Barkanmu da wayewar gari yau Talata!

    Masu bibiyar mu a wannan shafi muna muku barka da safiya da fatan an tashi lafiya.

    Sani Aliyu ke fatan kasancewa da ku a wannan yini domin kawo muku labarai da rahotanni daga sassan duniya daban daban, ciki har da yakin da ake gwabzawa tsakanin Rasha da Ukraine, da kuma wasu batutuwan da ke wakana a gida Nijar da Kamaru da Chadi da Ghana da kuma Najeriya.

    Muna fatan za ku ci gaba da kasancewa da mu!