Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Tarayyar Turai ta ce za ta rage dogaro da arzikin gas na Rasha

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.

Rahoto kai-tsaye

Sani Aliyu

  1. Hotunan macin da mata ke yi a Abuja domin zagayowar Ranar Mata ta Duniya

    Wasu mata a Najeriya sun hallara a dandalin Eagle Square da ke Abuja babban birnin kasar, a ranar da ake bikin zagayowar Ranar Mata ta Duniya.

  2. 'Yan bindiga sun sace Rabaran na cocin Katolika da wasu mutum uku a Kaduna

    Wasu 'yan bindiga sun harbe mutum biyu har lahira kuma sun sace wani Fada na cocin Katolika a yankin Kudenda da ke wajen birnin Kaduna.

    Jaridar Daily Trust ta wallafa rahoton da ke cewa maharan sun sace Rabaran Fada Joseph Akeke bayan sun kai wani hari kan al'ummar ta Kudenda.

    Samson, wani mazaunin yankin, ya ce maharan sun isa wurin ne da misali karfe 1 na tsakar dare, kuma suka fice da misalin karfe 2.30 kafin Asubar yau Talata.

    Wadanda suka kashe sun hada da wani mai gadin gidan Rabaran Akeke da wani mai zama a gidan, sannan maharan su sace wata mata da 'ya'yanta biyu tare da Mista Akeke.

    Jaridar ta Daily Trust ta tuntubi kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Kaduna, ASP Jalige Mohammed wanda ya shaida ma ta cewa zai binciki lamarin kafin ya ce wani abu.

  3. Rasha ta bude wasu hanyoyin jin kai domin fararen hular Ukraine su fice daga garuruwan da ake yaki

    Ma'aikatar tsaron Rasha ta sanar cewa ta bude wasu hanyoyin jin kai domin fararen hular Ukraine su fice daga garuruwan Cherhihiv da Sumy da Kharkiv da Mariupol da kuma Kyiv babban birnin kasar.

    Yunkurin da a ke yi a kwanakin baya sun gamu da cikas, inda aka rika bude wa fararen hular wuta.

    Kamfanin dillancin labarai na Interfax na kasar Rasha ya ruwaito cewa sojojin Rasha sun daina bude wuta tun karfe 7 agogon GMT, wato karfe bakwai ke nan agogon Najeriya, Kamaru, Nijar da Chadi.

  4. Ukraine ta ce ta kashe wani babban hafsan sojojin Rasha a wajen birnin Kharkiv

    Ma'aikatar tsaro ta Ukraine ta sanar cewa dakarun kasar sun kashe wani babban janar na sojojin Rasha yayinwani fada da sojojin kasashen biyu suka yi a wajen birnin Kharkiv.

    Sai dai BBC ba za ta iya tabbatar da sahihancin wannan labarin ba domin jami'an gwamnatin Rasha ba su ce komai ba kan batun.

    Sanarwar ta ma'aikatar tsaron Ukraine ta ce mutumin da aka kashe shi ne Vitaly Gerasimov, wanda manjo-janar ne kuma mataimakin kwamnadan rundunar sojojin Rasha ta 41.

    Sanarwar ta kuma ce baya ga Janar Gerasimov, an kashe wasu hafsoshin sojin na Rasha, wasunsu kuma an raunata su.

    Jami'an Ukraine sun wallafa hoton wani soja wanda suka ce hoton Janar Gerasimov ne, kuma sun rubuta wani sako a jiki da ke cewa "Halakakke" wanda suka rubuta da jan launi a kasan hoton.

  5. Mamayar da Rasha ke wa Ukraine ta shiga kwana na 13

    Barkanmu da wannan safiya ta Talata, ranar da za mu ci gaba da bayyana muku abubuwan da ke faruwa a rana ta 13 ta mamayar da Rasha ke yi wa Ukraine. Ga wasu cikin abubuwan da muka sani:

    • Shugaban hukumar da ke kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya Martin Griffiths, ya bukaci Ukraine da Rasha su samar da wasu hanyoyin da fararen hula za su rika bi domin ficewa daga yankunan da ake gwabza fada
    • Rokokin da Rasha ke harbawa na hana fararen hula a biranen Kyiv da Mariupol da Sumy da kuma Kharkiv ficewa, inji Ukraine
    • Kafofin yada labarai na Rasha sun ruwaito gwamnatin kasar na cewa za ta sake bude wasu hanyoyin domin fararen hular Ukraine su fice daga wuraren da yaki ya rutsa da su
    • Wata ganawa da bangarorin biyu suka yi a karo na uku ba ta samar da wata yarjejeniya ba - sai dai jami'an Rasha da na Ukraine za su sake ganawa a karo na hudu a yau Talata
    • Ana kuma sa ran ministocin harkokin waje na Rasha da Ukraine za su gana kai tsaye ranar Alhamis a Turkiyya
  6. Barkanmu da safiyar Talata

    BBC za ta rika kawo muku yadda take kasancewa a fagen dagar da Rasha ta buɗe yayin da ta ke ci gaba da kai hare-hare a Ukraine tun daga ranar Alhamis, 24 ga watan Fabrairu.

    Za mu kuma kawo muku muhimman labarai daga wasu sassa na Najeriya da wasu kasashen duniya.

    Ku biyo ni Sani Aliyu a wannan shafin domin samun rahotannin kai-tsaye.