A nan za mu rufe wannan shafin da muke kawo labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a sassan duniya
Sai gobe
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya musamman Ukraine da Rasha.
Sani Aliyu
Sai gobe
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya gode wa shugaban Amurka kan matakinsa na dakatar da sayen albarkatun man Rasha.
Ya yi kira ga sauran kasashen duniya su bi sahun Amurka, yana mai cewa matakin “zai karya zuciyar Putin ta yaki.”
Tun da farko shugaban na Ukraine ya gabatar da jawabi ga majalisar dokokin Birtaniya, inda ya nemi a kara tsawwala takunkumai kan Rasha.
Ma’ikatar tsaron Amurka ta ce ta yi amannar cewa an kashe sojojin Rasha tsakanin dubu biyu zuwa dubu hudu ya zuwa yanzu tun bayan fara fada da Ukraine.
Shugaban hukumar leken asirin kasar ya fada a wani taro na Majalisar kasar cewa an yi wannan kiyasi ne bisa la’akari da bayanan da hukumar ta samu.
Dangane da batun sanyin da Rasha ta yi a mamayar da ta ke ya ce, ‘ta kare wa Rasha ne’
BBC ta dawo da aikin watsa labarai a harshen Ingilishi a kasar Rasha bayan ta dakatar da ayyukan yan jarida masu watsa labarai da kuma ma'aikatanta na wucin gadi a kasar.
BBC ta ce ta yi la'akari ne da tasirin sabbin dokokin majalisar dokokin Rasha da ta zartar a makon da ya gabata wanda zai zama laifi ne yada labaran karya game da yakin Rasha a Ukraine.
Saba dokar ya shafi hukuncin ɗaurin shekara 15 a gidan yari.
BBC ta ce bayan nazari sosai, ta yanke shawarar cewa batun Rasha wani muhimmin bangare ne na labarin Ukraine wanda ya kamata a ba da labarin kai tsaye ba tare da nuna son kai ba.
Kungiyar tarayyar Turai ta ce tana shirin rage dogaro kacokan akan gas din Rasha da kaso biyu bisa uku kafin nan da karshen shekarar da muke ciki.
Kwamishinonin kungiyar sun ce zasu cimma hakan ne ta hanyar raba kafa da kuma maye gurbin amfani da gas da makamashi marar gurbata muhalli.
Sun kuma ce gidajen dake amfani da iskar gas zasu rage amfani da shi.
Kasashen Turai dai a yanzu na shigar da kusan kaso 40 cikin 100 na gas kasashensu daga Rasha.
Fararen hula sun fara ficewa dagakofar ragon da Rasha ta yi wa birnin Sumy na Ukraine bayan da Rasha ta amince ta daina yi wa birnin lugudan wuta.
Wasu jerin gwanon bas bas da kananan motoci sun bar birnin Poltava wanda ba shi da nisa da iyakar Rasha.
Daliban kasashen wajen na daga cikin wadanda aka kwashe.
Wasu rahotanni daga Rasha dangane da batun shigar da kayan agaji sun nuna cewa har yanzu ba a cimma matsaya ba.
An damu matuka da yadda fararen hula suka makale a wasu wurare, don haka suna bukatar dukkan bangarorin da su dauki matakin da ya dace domin bai wa fararen hula damar ficewa daga yankunan da yakin yafi kamari.
Shugaban Ukraine ya ce an tura wani jerin gwanon motoci zuwa kudancin birnin Mariupol da ke Ukraine domin ceto fararen hula wadanda ke rayuwa cikin rashin ruwa da wuta kusan mako guda.
Wata kotu a Kano ta aike da Abdulmajid Danbilki Kwamanda daya daga cikin jiga-jigan APC a jihar a gidan yari
Danbilki zai gaba da zama a gidan yari har zuwa 15 ga watan Maris.
Gwamnatin jihar Kano ta gurfanar da Danbilki Kwamanda ne daya daga cikin makusanta ga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari gaban kotun Majistere da ke Nomansland bisa zargin bacin suna da tunzura al’umma.
Ana tuhumarsa da batawa gwamnan Kano suna, kan zargin cewar gwamnan na Kano ya bayar da cin hanci kafin aka bai wa Shugaban Jam’iyyar APC Abdullahi Abbas takardar sheda ta zama shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano.
Shugaban Amurka Joe Biden ya tabbatar da cewa kasarsa ta daina shigar da fetur da iskar gas da makamashin kwal daga Rasha.
Ya ce hakan na nufin "Amurkawa za su kara matsa lamba" kan shugabancin Putin.
"Ba za mu kasance cikin wadanda za su mara wa yakin da Putin yake yi baya ba," a cewar Biden.
Duk da cewa matakin zai haifar da tsoron tashin farashin gas, ya samu goyon bayan dukkan jam'iyyun kasar.
Farashin man fetur ya tashi gabanin sanarwar da Mr Biden ya gabatar, inda farashin fetur samfurin brent crude, ya tashi da kusan kashi 5, zuwa $130 a kan gangar mai daya.
Ana sa ran Shugaban Amurka Joe Biden zai sanar da cewa kasarsa za ta daina sayen albarkatun man fetur daga kasar Rasha a yau Talata.
Masana na cewa sanarwar na karkashin matakan ladabtarwar da Amurka ke dauka saboda mamayar da rasha ke yi wa Ukraine.
Fadar White House ta ce Shugaba Biden zai yi jawabi inda a ciki zai sanar da "matakan da kasarsa za ta dauka domin ladabtar da Rasha saboda mamayar da ta ke yi wa Ukraine."
Gwamnatin Mista Biden na fuskantar matsin lamba matuka daga 'yan majalisar kasar da ke son ta dauki wannan matakin.
Akwai rahoton da ke cewa ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya tattauna da Fadar Vatican.
Rahotn na cewa Mista Lavrov ya sanar da fadar matsayar kasarsa dangane da yakin da ake gwabzawa tsakani Uraine da kasar tasa.
A ranar Lahadi Fafaroma ya ce yakin na janyo da "mace-mace da asara da kuma wahalhalu" yayin da yake jawabi ga jama'an da suka taru a dandalin St. Peter's Square.
A halin da ake ciki Mista Lavrov na shirin ganawa da takwaransa na Ukraine Dmytro Kuleba a Turkiyya ranar Alhamis mai zuwa.
Uwargidan mataimakin shugaban Najeriya Misis Dolapo Osinbajo ta ziyarci Maiduguri jiya Litinin karkashin wata ziyara da ta kai wata cibiyar yara mai suna Children’s Learning Centre wadda mai gidanta ya taimaka aka kafa ta ranar 8 ga watan maris 2017, yayin da yake bikin cikarsa shekara 60 da haihuwa.
An shirya makarantar yadda za ta samar wa dalibai kimanin 1,500 dakunan kwana da abinci da ilimi, musamman daliban da rikicin Boko Haram ya yi sanadin zamansu marayu a jihohi shida na yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Misis Osinbajo ta duba kayan da yaran suka hada a karkashin koya musu sana'a da ake yi a makarantar, ciki har da hada mutum-mutumi mai motsi da dinki da sauransu.
An kuma mika wa uwargidan mataimaki shugaban kasar wani kek na musamman a aka yi domin taya shi murnar cika shekara 65 da haihuwa.
Ƙungiyar Hadin Kan Ƙasashen Musulmai ta duniya OIC ta sha alwashin tallafa wa jamhuriyar Nijar da taimaka mata wajen warware matsalolin da ƙasar ke fuskanta.
Sakatare-Janar na ƙungiyar Mr Hissein Brahim Taha ne ya bayyana hakan yayin wata ziyara da ya kai wa Shugaba Mohamed Bazoum a Yamai a jiya Litinin.
Ziyarar ta Hissein Brahim Taha na daga cikin rangadin da yake yi a ƙasashen yankin Sahel da na Tafkin Chadi.
Taron ya yi duba ne kan alaƙar Nijar da OIC da kuma lalubo hanyoyin ƙarfafa matakan Musulunci da kuma goyon bayan aniyar warware matsalolin da Nijar ke fuskanta.
Mr Taha ya miƙa godiyarsa ga jamhuriyyar Nijar kan ƙoƙarin da take yi na goyon bayan ayyukan OIC da kuma musamman kafa reshen OIC na yankin Sahel da Tafkin Chadi a Nijar.
Shi ma shugaban ƙasar Nijar Bazoum ya bayyana cewa ƙasarsa a shirye take ta goyi bayan ayyukan OIC.
Ya kuma yi kira ga ƙasashe ƙungiyoyin OIC da hukumominsu da su shiga cikin lamarin kuma su ba da gudunmowarsu wajen kawo ƙarshen rashin tsaro da hauhawar kayan abinci da ake fama da su a yankunan Sahel da Tafkin Chadi.
Dukkannin ɓangarorin kuma sun tattauna kan batutuwan da suka shafi ƙasashen Musulmai da rawar da OIC ke takawa wajen magance rigibgimu da sasantawa da kuma ƙoƙarinta na ganin an hada kai wajen ɗaukar matakan Musulunci don magance matsalolin da duniyar Musulmai ke fuskanta.
Rahotanni na cewa wata babbar kotun tarayya da ke Abuja a Najeriya ta umurci gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi ya sauka daga daga mukaminsa.
Kazalika kotun ta umurci mataimakin gwamnan da kakakin majalisar dokokin jihar da sauran ƴan majalisar da suka sauya sheka tare da gwamnan daga jam'iyyar PDP zuwa APC su ma su Sauka daga mukamansu.
Kotun ta ce sauya shekar da suka yi daga jam`iyyar PDP zuwa APC ya saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya, saboda haka ba su cancanci zama a kan kujerun nasu ba.
Harwayau, kotun buƙaci su da su mayar da bako dayan albashin da suka karba bayan sauya shekar tasu.
Majalisar wakilan Najeriya ta sanar da cewa ta janye hukuncin da ta dauka kan wasu kudurin doka uku da suka shafi mata da aka sake gabatar ma ta.
Kudurorin dokar sun hada da na zama dan kasa, da na zama asalin dan wata jiha a Najeriya da na samar wa mata kashi 35 cikin 100 na mukaman siyasa.
Dukkan wadannan kudurorin dokan sun gaza tsallake bukatar doka da ta bukaci sai kason 'yan majalisa biyu cikin ukunsu sun amince da su kafin a amince da su a gyaran da ake wa tsarin mulkin kasar.
Sanarwar da majalisar ta fitar ta ce kakakin majalisar Femi Gbajabiamila da sauran 'yan majalisar na son ganin an ci gaba da aiki kan kudurorin uku, kuma sun mika su ga babban kwamitin gidan domin a sake gabatar da su.
Sanarwar ta kuma ce Majalisar za ta fara aiki kan kudurorin uku tare da sauran kudurorin da ke gabanta nan da mako hudu mai zuwa.
Sabbin hotuna da aka ɗauka daga tauraron ɗan adam sun nuna yadda ake ci gaba da aiki a wajen gwajin makamin nukiliya na Koriya Ta Arewa a karon farko cikin shekara hudu.
Wasu hotuna da wani kamfanin tauraron ɗan adam na Amurka ya ɗauka sun nuna alamun ana aiki gadan-gadan da kuma yadda ake yin kwaskwarima ga wurin gwajin makamin.
Wakiliyar BBC ta ce an kulle wurin tun a 2018 bayan shugaban Koriya Ta Arewa Kim Jong Un ya yi alƙawari ga tsohon shugaban Amurka Donald Trump kan cewa zai dakatar da gwajin makamai masu cin dogon zango.
Wannan binciken na wannan kamfanin na zuwa ne a daidai lokacin da ake hasashen cewa ƙasar za ta koma gwajin makaman nata na nukiliya.
Ƴan Najeriya suna ta mayar da martani da nuna kaɗuwarsu kan sace tare da kisan wata matashiya da aka yi a jihar Lagos da ke kudu maso yammacin ƙasar.
Ana tuhumar daya daga cikin direbobin motar wadda mallakar gwamnati ce - wadda aka fi sani da sunan BRT (Bus Rapid Transit) - kuma an kama shi, ana tuhumars ada aikata wannan mummunan laifin.
Matar mai shekara 22 ta bace ne tun karshen watan Fabrairu bayan da ta shiga motar ta BRT mai farin jini.
Labarin abin da ya faru ga matar ya tayar da hankulan jama'a har ta kai ga an fara wani gangami a shafukan sada zumunta, inda ake neman adalci ga matar: Justice for Bamise a Twitter.
Gwamnatin jihar Legas ta kuma yi alkawarin daukar matakin shari'a kan duk wanda aka samu yana da hannu kan sacewa da hallaka matar.
Wani rahoton BBC na cewa Sudan ta kwashe jiragen yakinta daga wani muhimmin sansanin sojojin sama na kasar dmin ba jiragen yakin Rasha damar kafa nasu sansanin.
Rahoton ya ruwaito ata jaridar intanet mai suna Al-Rakoba mai alaka da jam'iyyun siyasa masu adawa da gwanatin mulkin soja ta kasar na cewa Rasha za ta jibge jiragen yakin ne da jiragen da ke jigilar kayan yaki a sansanin a karkashin wani shiri na kai samame a wani wurin da ba a fayyace ba.
Jaridar ta Al-Rakoba ta kuma ce wani babban hafsan sojojin Sudan ya shaida ma ta cewa an kwashe jiragen yakin na Sudan ne daga sansanin Wadi Seidna da ke arewa da Omdurman zuwa wasu filayen jirgn sama da ke wajen Khartoum.
Hafsan ya kuma ce Rasha za ta ajiye sukwaduron day ko biyu na sojojin samanta a sansanin na Wadi Seidna.
Mataimaki shugaban Sudan Mohamed Hamdan Dagalo wanda ake wa lakabi da Himidti ya ziyarci Rasha cikin 'ya kwanankin da suka gabata inda ya tattauna da jami'an Rashar kan batutuwan inganta tsaro.
Hukumar da ke tsaron kan iyakar kasar Poland ta ce mutum miliyan 1.2 sun tsere daga Ukraine zuwa kasar ta Poland tun bayan da yaki ya barke tsakanin Ukraine da Rasha.
A ranar Litinin kawai, mutum 141,500 ne suka tsallaka kan iyakar kasashen biyu, kamar yadda hukumar ta wallafa a Twitter - wanda da kadan ne bai kai na ranar Lahadi ba wanda ya kai 142,300.
Kusan kashi 90 cikin 100 na masu tserewa 'yan kasar Ukraine mata da kananan yara ne. Wani malamain jami'a na cewa kashi 40 cikin 100 na 'yan gudun hijirara su bar Poland zuwa wasu kasashen.
Dama Poland na kula da 'yan Ukraine masu yawa, inda ake hasahsen akwai kimanin mutum miliyan daya zuwa miliyan biyu da suke fakewa a kasar.
Bankin Duniya ya amince da tsarin basussuka da tallafi ga ƴan ƙasar Ukraine na kusan sama da dala biliyan bakwai.
Bankin ya ce waɗannan kuɗaɗen za su taimaka wa gwamnatin Ukraine toshe kafofi da dama ciki har da biyan ma'aikatan asibiti da ƴan fansho da waɗanda suka manyanta da kuma tallafa wa masu ƙaramin ƙarfi.
Ƙasashen Sweden da Holland ne za su tsaya wa Ukraine domin ganin wasu kuɗin sun fito, haka kuma akwai wasu tallafin kuɗi na musamman daga ƙasashe kamar Birtaniya da Denmark da Latvia da Lithuania.
A cikin daren jiya shugaban kasar Ukraine ya wallafa wani bidiyo cikin wadanda yake wallafawa a kullum. Sai dai a wannan karon ya wallafa shi ne daga ofishin shugaban kasa da ke birnin Kyiv.
Ya ce ba boyewa yake yi ba. Kuma ya ce ba ya tsoron makomarksa.
Ana ganin bayyana wurin da yake ga duniya sako ne ga Vladimir Putin - domin har yanzu dakarun ukraine na kare birnin Kyiv daga harin da Rasha ke kai wa kan babban birnin kasar na Ukraine.