Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Zelensky ya roƙi Nato ta tura masa jiragen yaƙi

Wannan shafi na kawo muku abubuwan da ke faruwa a sassan duniya kai-tsaye, musamman game da yaƙin Ukraine.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Imam Saleh

  1. Gwamnatin Najeriya ta amince ta miƙa DCP Abba Kyari ga Amurka

    Gwamnatin Najeriya ta amince da buƙatar Amurka ta miƙa mata ɗan sanda DCP Abba Kyari wanda ake zargi da hannu wajen aikata zambar fiye da dala miliyan ɗaya ta intanet tare da Ramon Abass.

    Ofishin Ministan Shari'a Abubakar Malami ne ya bayyana hakan ranar Alhamis bayan ministan ya gabatar wa Babbar Kotun Tarayya a Abuja buƙatar miƙa ɗan sandan wanda tuni aka dakatar da shi don neman amincewarta.

    Antoni janar ɗin ya ce ya nemi a kai Abba Kyari Amurka ne bayan buƙatar da ƙasar ta gabatar masa, inda ya yi amfani da dokar miƙa wanda ake zargi da laifi ƙasashen ƙetare ta Extradition Act a gaban kotun.

    Sai dai babu ƙarin bayani a yanzu game da abin da zai faru da sauran zarge-zargen da hukumar yaƙi da miyagun ƙwayoyi, NDLEA, take yi masa na safarar hodar ibilis idan aka kai shi Amurka.

    Tun a 2021 ne Amurka ta zargi DCP Kyari da mu'amala da Ramon Abass, wanda aka fi sani da Hushpuppi wanda kuma tuni yake tsare a ƙasar, da damfarar wasu kamfanoni fiye da dala miliyan ɗaya.

    • Hushpuppi: Da gaske Abba Kyari ya karɓi rashawar $1.1m daga hannun ɗan damfarar?
    • Ƴan sanda sun miƙa Abba Kyari ga hukumar yaki da miyagun ƙwayoyi
  2. Birnin Kyiv ya fuskanci rugugin bama-bamai a rana ta takwas

    Da yake yanzu muke fara rahotannin, ga ƙarin bayani game da abubuwan da ke faruwa kafin mu zo a rana ta takwas tun bayan ƙaddamar da hare-hare a Ukraine:

    A birnin Kyiv:

    • An jiyo wasu manyan fashewa cikin 'yan awannin da suka wuce, sai dai babu tabbas game da inda aka hara da kuma ko wasu sun ji rauni
    • Wakilan BBC sun ce ana iya jin ƙarar fashewar daga hawa na biyu na gidan ƙarƙashin ƙasa da suke ciki
    • Majiyar bayanan sirri ta sojojin Amurka ta ce jerin motocin yaki na Rasha da ke daf da ƙarasawa birnin Kyiv ba ya sauri saboda ƙarancin man fetur da kayan abinci

    A kudancin ƙasar:

    • Dakarun Rasha sun ƙwace iko da garin Kherson mai tashar jiragen ruwa, a cewar hukumomin yankin. Shi ne babban gari na farko da Rasha ta ƙwace
    • A gari Marupol mai tashar jirgin ruwa, ana fargabar mutane da dama sun mutu bayan awanni da aka shafe ana ɓarin wuta, kamar yadda mataimaikin magajin gari ya bayyana. Sai dai sojojin Ukraine sun ce har yanzu garin yana hannunsu
  3. Labarai da dumi-dumi, An dakatar da 'yan wasan Rasha da na Belarus shiga gasar Paralympics 2022

    'Yan wasa daga Rasha da Belarus ba za su shiga gasar tsalle-tsalle ba ta nakasassu wato Paralympics ta 2022 da za a gudanar a China.

    Hukumar kula da gasar ta International Paralympic Committee ce ta yanke hukuncin sakamakon yaƙin da ƙasashensu suka ƙaddamar kan Ukraine a makon da ya gabata.

    Da ma tuni aka shaida musu cewa ba za su shiga gasar da tutocin ƙasashen nasu ba, sai dai a matsayin masu zaman kansu, kafin daga baya a dakatar da su baki ɗaya.

  4. Assalamu Alaikum

    Kun shigo shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa tare da Umar Mikail.

    Ku biyo mu don sanin halin da duniya ke ciki a yau Alhamis, musamman a Ukraine inda Rasha ke kai hare-hare don mamaye ta.

    Barkanmu da hantsi.