Bissalam
To jama'a a nan za mu dakata a yau, sai kuma gobe idan Allah ya kaimu.
Imam Saleh ke cewa mu kwana lafiya, daga nan sashen Hausa na BBC.
Wannan shafi na kawo muku abubuwan da ke faruwa a sassan duniya kai-tsaye, musamman game da yaƙin Ukraine.
Umar Mikail and Imam Saleh
To jama'a a nan za mu dakata a yau, sai kuma gobe idan Allah ya kaimu.
Imam Saleh ke cewa mu kwana lafiya, daga nan sashen Hausa na BBC.

Asalin hoton, Reuters
An rantsar da wata sabuwar gwamnati ta daban, da ke zaman kishiya ga gwamnati mai ci a Libya, yayin da wutar fito-na-fito tsakanin bangarorin biyu ke kara ruruwa.
An rantsar da Fathi Bashaga a matsayin Firaminista can a birnin Tobruk, da ke gabashin kasar, inda majalisar dokokin Libyar ta zabe shi a watan da ya gabata.
Wakilin BBC ya ce yanzu dai kusan Libya tana da gwamnatoci biyu ne, bayan da shirin Majalisar Dinkin Duniya na kokarin dakatar da fada na shekara da shekaru na bangarori ya shiririce, inda aka kasa gudanar da zaben shugaban kasa a watan Disamba.
Shi dai, Firaminista mai-ci, Abdulhamid al-Dbeibah ya lashi takobin cewa ba zai sauka ba. Tun da farko Bashaga, da aka rantsar a yau, ya yi zargin cewa Firaministan mai-ci, ya tsare sararin samaniyar Libya domin hana ministocinsa zuwa taron rantsuwar.
Har ma ofishinsa, ya ce, an sace wasu ministoci biyu, wadanda suka kama hanya domin zuwa wurin a mota. Ana ganin halin da aka shiga yanzu ka iya sake tsunduma kasar ta Arewacin Afirka, cikin rikicin siyasa da yaki.
Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta gabatar da tuhuma takwas ga DCP Abba Kyari da karin mutum shida, a gaban wata babbar kotun tarayya ta Abuja bisa zargin hannunsu da fataucin kwayoyi.
Wannan na zuwa ne ‘yan sa’o’I da hukumomin kasar suka amince su mika ɗan sanda Abba Kyari hannun Amurka.
NDLEA ta gabatar da tuhume-tuhumen ne a gaban kootun tarayya da ke Abuja a kan ACP Sunday Ogbuya da ACP Sunday James da Sifeta Simon Ariba da kuma Sifeta John Nuhu, wadanda suka yi aiki da runduna ta musamman da ke yaki da iyagun laifuka ta Police Intelligence Response Team.
Da kuma wasu mutum biyum Chibunna Patrcike da Emeka Alfphosus, wadanda aka kama su a filin jirgin sama na Enugu bisa zarginsu da laifuka da suka shafi batun muggan kwayoyi ciki har da hodar ibilis.
Rahotanni sunce tawagar lauyoyin NDLEA karkashin jagorancin Mr Joseph Sunday ta shigar da kara inda ta zargi DCP Abba Kyari da sauran jami'an 'yan sanda hudu da hada baki wajen safarar hodar ibilis mai nauyin fiye da kilogiram 17.
Kazalika an yi zargin cewa Abba Kyari da mutanenssa da ke tsare a yanzu a hannun NDLEA sun jirkita kunshin hodar ibilis da ya kai nauyin kilogiram 21.
Hakan na zuwa ne a yayin da ofishin Ministan Shari'a Abubakar Malami ya bayyana amincewa da bukatar Amurka ta mika mata DCP Abba Kyari bisa zarginsa da hannu wajen aikata zambar fiye da dala miliyan daya ta intanet tare da Hushpuppi.
Ana sa ran a gobe ne za a saka ranar da za a fara sauraron karar da NDLEA ta shigar.

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar da ke sa ido kan harkokin nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce Iran ta ninka kusan biyu yawan sinadarin Uranium din da take ingantawa, har zuwa kashi 60 cikin dari a cikin wata uku da ya wuce.
Hukumar ta IAEA, ta fitar da rahoton ne, yayin da tattaunawa kan farfado da yarjejeniyar nukiliya ta 2015, wadda ke nufin shawo kan Iran ta rage burinta na nukiliya, ta shiga matakin siradi, wato, ko ta ware ko ta waraye.
A jibi Asabar ne, shugaban hukumar, Rafael Grossi, zai tashi takanas ta Kano, ya je Iran, da fatan shawo kan matsalolin da suka kasance kadangaren-bakin tulu, wajen cimma yarjejeniya ta karshe.

Asalin hoton, Vladmir Putin
Shugaban Rasha Vladmir Putin ya ce yaƙin da ya ƙaddamar a Ukraine na tafiya yadda aka tsara.
Yana magana ne yayin wani jawabi da ya gabatar a ranar Larabar nan.
Ya nanata cewa suna yaƙi ne da dakarun ƙasar ba wai fararen hulla ba, waɗanda tuni gwamnatinsa ta ba wa damar ficewa daga wuraren da ake yaƙi.
Ya ƙara da cewa babban abun da suka sanya a gaba shine na ganin sun gurgunta tsaron Ukraine, da kuma kawar da barazanar da take kasar ke yi wa Rasha.

Asalin hoton, Reuters
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Ukraine ta ce akalla mutane 22 ne suka mutu a hare-haren da jiragen saman Rasha suka kai a yankin Chernihiv da ke arewacin Ukraine.
Cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter, hukumar ta ce ana ci gaba da aikin ceto.
Ba a fayyace inda ake zargin an kai harin ba.
Tun da farko gwamnan yankin ya ce akalla mutane tara ne suka mutu sakamakon wani samame da aka kai a makarantu biyu da wasu gidaje masu zaman kansu.

Asalin hoton, Kremlin
Shugaban Rasha Vladmir Putin, ya ce da gangan hukumomin Ukraine ke garkuwa da ɗaliban Afrika da na sauran ƙasashen duniya da ke karatu a can, domin kare kansu.
Ɗaliban kasashen duniya sun yi ta zargin cewa jami'an Ukraine na hana su tsallaka iyaka don gujewa yaƙi.
Yayin wani jawabi da ya gabatar da yammacin nan, Mista Putin ya ce sun samu rahotannin da ke nuna cewa jami'an Ukraine na kashe ƴan ƙasashen waje, su kuma ɗaura alhakin hakan a kan Rasha.
Ya bada misali da wani abu da ya faru, inda ya ce sojojin Ukraine sun kashe wasu ɗaliban China.
Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya yi alkawarin cewa za a sa lalle ilalla Rasha ta biya kudin ɓarnar da take yi a kasarsa.
A wani sako da ya aike ta hoton bidiyo Shugaban ya lashi takobin cewa za a gyara duk wani gida da titi da aka lalata a Ukraine.
A halin da ake ciki dai Rashar ta ci gaba da kai hare-haren mamayar da take yi wa kasar, makwabciyarta.
Birnin Mariupol mai tasahar jirgin ruwa, wanda ke da matukar muhimmanci na ci gaba da shan ruwan makamai masu linzami, daga dakarun Rasha da suka yi masa kawanya.
Mataimakin magajin garin birnin (Sergei Orlov) ya gaya wa BBC cewa an katse wa mutanen birnin wutar lantarki, da naurarar dumama gida da kuma ruwa.
Ya ce halin da jama'a ke ciki ya munana, "an aci gaba da harba makamai da ruwan bamabamai, yanayin da ake ciki na farar hula, a iya cewa muna cikin mawuyacin hali."
Mista Orlov ya kuma ce abu ne mai wuyar gaske a iya kwaso dukkanin gawarwakin mutnen da aka kashe, kuma ya yi kiyasin cewa sama da farar hula 200 aka kashe ko jikkata.
Shugaban ƙasar Ukraine Zelensky ya yi wani taron manema labarai inda ya yi kira ga Ƙasashen Yamma su tura masa jiragen yaƙi.
"Idan ba ku da ƙarfin rufe sararin samaniyar (tabbatar da hana jirage wucewa ta sararin samaniyar Ukraine), to ku ba ni jirage", kamar yadda ya ce.
"Idan har aka kawar da mu, abin Allah Ya kiyaye, to Latvia da Lithuania da Estonia ne za su zama na gaba."
Waɗannan ƙasashe na daga cikin ƙawancen Nato na tsaro, wato kenan idan Rasha ta kutsa ɗaya daga ciki, to zai zama yaƙi ne da dukkan mambobin.
Nan ba da jimawa ba za mu sake kawo ƙarin bayani kan abin da Zelensky ya ce.

Asalin hoton, Getty Images
Farashin mai da iskar gas sun ci gaba da tashin gwauron zabi a kasuwar duniya, inda a yanzu farashin ganga daya ta danyan man samfurin Brent ya kai dala 119, mafi yawa cikin shekara 10.
A Turai ma farashin gas na ci gaba da tashi ba kakkautawa, kamar yadda farashin manyan kayayyaki irin su goran-ruwa wato aluminium, da kwal da alkama su ma ke ƙara tashi.
Duk da cewa Amurka ba ta sanya cinikin mai da gas na Rasha cikin takunkumin da ta jagoranci sanya wa kasar ba a kan mamayar ta a Ukraine, zuwa yanzu ana dari-dari sosai a fannnin ciniki da huldar kudade, wajen sayen kayayyakin Rasha.
Karin manyan kamfanonin duniya da kungiyoyi na takaitawa ko ma dakatar da harkokinsu a Rasha.
Kamfanoni na baya-bayan nan su ne IKEA, da Volswagen, da Spotify, da Citigroup, da H&M, da kuma uwa-uba Bankin Duniya.

Asalin hoton, AFP
An rantsar da kishiyar gwamnati mai-ci a Libya yayin da wutar fito-na-fito tsakanin bangarorin biyu ke kara ruruwa.
Fathi Bashaga ya sha rantsuwa a matsayin firaminista a Tobruk, amma kuma ya ce firaminista mai-ci, Abdulhamid al-Dbeibah ya tsare sararin samaniyar kasar ta Libya domin hana ministocinsa zuwa birnin wanda ke gabashin kasar.
Ofishin Mista Bashaga ya ce an sace wasu ministoci biyu da suka kama hanya domin zuwa birnin ta mota.
Ana nuna shakku kan wani shirin kawo karshen rikicin da ke faruwa tsakanin abokan hamayya a Libya, wanda Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ke mara wa baya.
Lamarin ya ƙara ƙamari ne tun da aka kasa gudanar da zaben da aka shirya yi a watan Disamba.

Asalin hoton, @AdudaG
Ƙaramin Ministan Harkokin Waje a Najeriya Zubairu Dada ya yi ƙarin bayani game da kuɗin da za a kashe na dala miliyan takwas da rabi - naira biliyan 3.5 - wajen kwashe 'yan ƙasar da yaƙi ya kora daga Ukraine.
Ya ce daga cikin ayyukan har da kula da waɗanda suka ƙi yarda su koma gida.
"Kar ku manta cewa aikin ya ƙunshi kula da 'yan Najeriyar da babu mamaki ba za su yarda su dawo ba, da kuma sauran ayyukan ciyarwa da ofisoshin za su yi. Za mu yi sawu da yawa da ake buƙata" a cewarsa.
"Kuma su ma kansu ofisoshin suna cikin tsananin buƙata...hatta ofishin jakadancimu na Ukraine sai an ɗauke shi daga ƙasar.
"Saboda haka idan akwai wani ɗan Najeriya da aka bari a ƙasar, za mu ci gaba da yi masa addu'a kar wani abin ƙi ya same shi."
Wani bidiyo da babban jami'in ma'aikatar harkokin waje ta Najeriya ya wallafa a shafinsa na Twitter ya nuna 'yan ƙasar na ƙoƙarin hawa jirgin da gwamnati ta tura musu a Warsaw na Poland ranar Alhamis.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Asalin hoton, NG Police
Gwamnatin Jihar Neja a arewacin Najeriya ta ce jami'an tsaro sun kashe 'yan bindiga 200 cikin kwana huɗu da suka gabata.
Kwamashinan Ƙananan Hukumomi Emmanuel Umar ya bayyana cewa dakarun tsaron sun fafata ne da yaran riƙaƙƙun 'yan fashin daji da suka haɗa da Ali Kawajo, da Bello Janbros, da Kachalla Halilu, da kuma Bello Turji.
A cewarsa, an ƙwato babur 60 da kuma shanun da ba a san adadinsu ba daga hannun 'yan fashin, inda aka mayar wa masu su kayansu.
Ya ƙara da cewa an yi fafatawar a yankunan Kundu da Babanlaba na ƙananan hukumomin Rafi da Mariga tsakanin Lahadi zuwa Laraba da suka wuce.
Jami'an tsaro biyu ne suka rasa rayukansu yayin gumurzun, in ji kwamashinan.

Asalin hoton, TASS
Dakarun Rasha sun kama iko da ginin gwamnatin yankin Kherson, a cewar shugaban gwamnatin Hennadiy Lahuta cikin wani saƙon Facebook.
"Amma har yanzu ba mu daina ayyukanmu ba," kamar yadda ya wallafa.
"Ma'aikatan gwamnatin yankin da nake jagoranta na ci gaba da aiki don magance matsaloli da zimmar taimaka wa 'yan gari. Yanzu muna jiran agaji."
Ya ƙara da cewa "na roƙe ku da kar ku yarda da labaran ƙarya da tsoratarwa".

Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergei Lavrov ya yi barazanar cewa idan har za a yi yaƙin duniya na uku zai zama "na nukiliya" ne.
Da yake magana yayin taron manema labarai a birnin Moscow ta bidiyo, Mista Lavrov ya ce Shugaban Amurka Joe Biden ya ce zaɓi ɗaya da ya rage bayan takunkuman da ake saka wa Rasha shi ne yaƙin duniya na uku.
Ya ce 'yan siyasar Yamma ne kaɗai suke da wannan tunanin ban da al'umar Rasha.
"Idan aka ƙaddamar da cikakken yaƙi a kanmu to waɗanda suka yi hakan ya kamata su yi tunani, kuma ina ganin sun fara tunanin hakan," a cewarsa.

Asalin hoton, NASS
Shugaban Masu Rinjye a Majalisar Wakilan Najeriya Alhassan Ado Doguwa ya isa ƙasar Romania tare da Shugaban Kwamatin Harkokin Waje Yusuf Buba a yunƙurin kwashe 'yan ƙasar da suka nemi mafaka daga yaƙin Ukraine.
Wakilan sun je a madadin majalisar bayan ta zartar da wani ƙudiri da ya buƙaci su yi aiki tare da ɓangaren gwamnati don tabbatar da an kwaso 'yan ƙasar kusan 5,000 da ke Poland da Romania da Hungary.
Ministan Harkokin Waje Geoffrey Onyeama ya ce ya yi magana da takwaransa na Hungary yana nema wa jirgin Najeriya izinin sauka don fara aikin.
A jiya Laraba Shugaba Muhammadu Buhari ya amince a kashe dala miliyan takwas da rabi - kusan naira biliyan uku da rabi - yayin aikin.
Lamarin na zuwa ne yayin da baƙaƙen fata ke kokawa kan wariyar launin fata da ake nuna musu a lokacin da suke neman ficewa daga Ukraine ɗin, inda wasu suka shafe kwanaki a kan layi saboda launin fatarsu.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Ƙasashen Afrika 17 sun kauce wa jefa ƙuri'a a Babban Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) don yin Allah wadai da hare-haren Rasha a kan Ukraine.
Daga cikin ƙasashen da ba su kaɗa ƙuri'ar ba akwai Afirka ta Kudu, da Aljeriya, da Uganda, da Burundi, da Senegal, da Sudan ta Kudu, da Mali, da kuma Mozambique.
Sauran su ne: Sudan, Namibia, Angola, Zimbabwe, Equatorial Guinea, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Madagascar, Tanzania da Congo.
Eritrea ce ƙasar Afirka kaɗai da ta kaɗa ƙuri'ar ƙin amincewa da ƙudirin na sukar matakin Rasha.
Uganda ta ce ta ƙi kaɗa ƙuri'ar ne saboda ta ci gaba da tabbatar da matsayinta na "yar ba-ruwana" yayin da take ƙoƙarin zama shugabar gamayyar ƙasashe 'yan ba-ruwana ta Non-Aligned Movement (Nam).

Asalin hoton, Azman
Yayin da 'yan Najeriya ke fama da ƙarancin man fetur, shi ma ɓangaren zirga-zirgar jiragen sama ya fara fama da tsadar man jirgi na Jet A1 a cikin ƙasar, a cewar rahoton jaridar Leadership.
Ƙarancin man ya sa farashinsa ya kai N426 daga N440 da aka sayar da shi a makon da ya gabata kan kowace lita ɗaya a filayen jiragen Najeriya.
Rahoton ya ce hakan ya jawo jinkiri ga wasu jirage na awanni huɗu zuwa takwas.
Mako biyu da suka gabata ana sayar da man kan N400 lita ɗaya kafin ya zama N440 a yanzu.
Kusan dukkan jiragen da ke zirga-zirga a cikin Najeriya sai da suka fuskanci jinkiri ranar Alhamis sakamakon matsalar man, a cewar rahoton na Leadership.
Gwmanatin Najeriya ta nemi izinin takwararta ta Hungary don saukar jirgin da zai ɗebo 'yan Najeriyar da suka shiga ƙasar daga Ukraine sakamakon yaƙi.
Yanzu babu jimawa Ministan Harkokin Waje na Najeriya Geoffrey Onyeama ya ce ya tattauna da takwaransa na Hungary.
Gwamnatin Najeriya ta ce kashin farko na 'yan ƙasar da za a kwaso za su sauka a yau Alhamis, inda za a ɗebo su daga Hungary da Poland da Romania.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Asalin hoton, Getty Images
Ma'aikatar ilimi ta Rasha ta sanar cewa za a fara wayar da kan ɗaliban firamare kan dalilin da ya sa "ya zama dole ƙasar ta ƙaddamar da yaƙi a Ukraine".
Sanarwar ta ce za a bai wa ɗaliban darasin ta intanet da misalin ƙarfe 12:00 agogon ƙasar (10:00 agogon Najeriya da Nijar) na yau Alhamis.
Za a bai wa masu kallo darasi "kan barazanar da ƙawancen tsaro na Nato ke yi wa ƙasarmu da kuma "dalilin da ya sa Rasha ta tsaya wajen kare fararen hula yankunan Donetsk da Luhansk".
Kazalika, sanarwar ta ce yaran za su koyi yadda za su tantance gaskiya da ƙarya saboda yawan labaran da suke samu da hotuna da bidiyo a intanet.