Wasu ɗaliban
Najeriya ƴan asalin jihar Sokoto da rikicin Rasha ya rutsa da su a Ukraine sun yi
kira ga gwamnatin jihar da ta gaggauta kwashe su domin suna ganin daman barin ƙasar
zai gagara nan ba da dadewa ba idan lamarin ya tsananta.
Ɗaliban da aka
bayyana guda 22 sun yi wannan kiran ne a zantawar da gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya haɗa ta kafar
zoom da su tare da kuma iyayensu daga gidan gwamnatin jihar.
Sanarwar da
gwamnatin jihar ta fitar ta ce ɗaya daga cikin ɗaliban mai suna Aisha Kabir ta
shaida wa gwamnan cewa halin da ake ciki a Kharkiv ya tsananta.
Rahotanni a
safiyar Lahadi sun ce sojojin Rasha sun kutsa Kharkiv kuma ana gwabza faɗa a
birnin na biyu mafi girma a Rasha.
“Muna jin ƙarar
harbe-harbe, ko da yake ana ƙoƙarin tafiya da mu cikin bus zuwa Romania, amma
direbobin suna jin tsoron za a iya kai masu hari, muna ganin jirgin ƙasa ne ba
ya da hatsari wanda za mu yi sauƙin ficewa.” In ji ɗalibar kamar yadda sanarwar da
mai magana da yawun gwamnan Muhammad Bello ya fitar ta bayyana.
Wani ɗalibin kuma
Shuaibu Muhammad, ya ce suna fuskantar ƙalubale a Krakow na Poland domin ba
isasshen abinci da wurin bacci mai kyau. “Daga Lviv zuwa Krakow tafiyar awa 12
ce, kuma yawancinmu ba mu san kowa ba da za mu yi magana da shi lokacin da muka
iso.
Wasu sun ce suna
fuskantar ƙalubale na yanayin sanyi da rashin tufafin da ya dace da bargon
bacci.
Wata ɗaliba Zarah
Ibrahimn ta bayyana fargabar cewa “ta ji ana faɗi daga gobe za a hana wa ƴan
ƙasashen waje fita Lviv, tana mai jaddada cewa Kharkiv na tattare da hatsari”
A nasa ɓangaren
gwamnan jihar ya yi wa ɗaliban alƙawalin cewa da su da sauran ɗalibai ƴan
Najeriya za su fice daga Ukraine nan ba da dadewa ba kuma su dawo gida lafiya.
Gwamnan ya ce ya
ba ma’aikatar kuɗi ta jihar umarnin ta tura wa ɗaliban da ke cikin mawuyacin
hali tallafin kudi kimanin dala 200 zuwa 300.
Iyayen ɗaliban
sun yaba kan yadda gwamnatin
Sokoto ta nuna damuwarta da kuma tausayin ƴaƴansu tare da jan hankalin ƴaƴansu da
su yi taka-tsan-tsan a yayin ficewa Ukraine.