Dakarun Rasha sun ƙwaci birnin Melitopol na Ukraine
Ma’aikatar tsaron Rasha ta tabbatar da kama birnin Melitopol a Ukraine, al’amarin da kamfanin dillacin labarai na Reuters ya bayyana a matsayin gari mafi muhimmanci da aka ƙwace tun lokacin da Rasha ta fara mamayar Ukraine a ranar Alhamis.
Melitopol na kusa da garin Mariupol, da ke yankin kudancin Zaporizhzhya.
Yan Ukraine 150,000 ke zama a Melitopol